🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*54*
Koda su Mami suka isa ga station ɗin babu yanda basuyi ba amma sam ƴan sanda sukaƙi sauraronsu alokacin sukace sai dai su dawo gobe.
Washe gari kam 6na safe can yay masu duk hankalinsu atashe dan basu san taƙamai man laifin da yay ma hukuma ba.
Nan ma sai da suka jima sannan D.P.O ɗin wurin yazo nan suke jin bayanin cewan an kamasa ne bisa tuhumarsa da suke na aikin mafiya.
Kuka Mami tayi ba kaɗan ba dan bata taɓa tinanin wani nata da aikata wannan muguwar sana'a ba sai gashi ɗan data haifa shike harkar.
Tsine masa da zatayi aka rufe mata baki ana bata haƙuri ,nan suka tabbatar mata da ai yanzu bai ciki ya jima da fita suna son dai ya bayyano masu duk wasu masu hannu da shuni aciki domin hukuma tai gaggawar ɗaukan mataki kansu.
Agaba suka sa Ubaid da manyan kulki sunsha zasusha fama kamin ya amsa masu tsmbayoyinsu sai suka ga akasin hakan domin tsab sai daya lissafo masu masu aikata harkar mafiya da inda duk za'a samesu.
Sunyi mamaki sose ƴan sanda kuma abin yay matuƙar girgiza su jin irin yanda suke tafiyar da al'amuransu.
"amma yallaɓai karku shiga wannan dajin kai tsaye domin akwai haɗari acikinsa kuna iya zuwa da niyyan kamasu kuma asamu mishkila dan hatsabibai ne ,hanya guda ɗaya zan kira Isha'q in yaso zan san dabarar da zan haɗa"
Hakan ko akayi inda Ubaid ya kirayi Isha'q a waya yace yazo nan gida shida oga yanzunn akwai wata babbar harƙalla data samu sai dai shi bai jin zaiyi su ɗin dai zaiyi masu hanya sannan kuma suyi saurin sakin mutanen dake cikin gidan dan ya sami labarin ƴan sanda sun san da wajen suna kuma nan tafe wajen kawo masu sumame.
Shima nasa ɓangaren Ishaq da jin hakan yako danna numban ogansu inda suka tsara wurin daza su haɗu.
Ba ɗau lokaci ba suka haɗu a wata anguwa daba mutane cikinta daganan kuma suka yanko zuwa gidan Ubaid.Koda zuwansu ko ƴan sanda suka rufar masu dama suna ciki zuwansu suke jira inda aka kamesu gaba ɗayansu, can gidan tsafin nasu kuma aka sa mashi wuta.
kwanakinsu 7 cikin cell ana garasu sannan aka miƙasu ga kotu inda ta yanke masu hukuncin ɗaurin rai2 da rai banda kuɗin diyyar rai da kowannensu zai bada miliyan 20 ahakan ma an sauƙaƙa masu sai Ubaid wanda ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara goma shabiyar tare da diyar rayuwaka na miliyan 5.
da yanke wannan hukunci aka ingiza ƙeyarsu zuwa gidan kaso, dukansu suna masu kuka, danasani cike da nadamar abinda sunka aikata.
Ubaid da aka bashi damar yin magana da iyalinsa ya tsaya yana kallonsu da hawaye fuskarsa ya kasa magana.
Da kuka Mami tace, "ka cucemu ka kuma cuci kanka Ubaid, baka yi amfani da ilimin da kake dashi ba kai watsi dashi ka jefa kanka ga halaka ,ka kashe rayuka bila adadin Ubaid ka ɗaukarma kanka zunubi babba, bana ko son ƙara ganinka a idanuwana zanso ka ƙare rayuwarka cikin gidann batare da munkuma ganawa ba,kaico nayi rashin ɗa na gari Allah ya jiƙanka Najib"
Ta ƙarashe naganar da matsanancin kuka.
Yanda take kukan ba kaɗan ɗin daɗa tashi hankalin Ubaid yayi ba.

VOCÊ ESTÁ LENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficção HistóricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.