Page 15

1.3K 133 1
                                    


🌀🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



        *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks🌺_*



          *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



15

Ɓarawon bacci ne kawai ya iya sace Ammar badan yay niyyar yinsa ba.

Ko Sallar asuba kasa tashi yinta yay dan daya farka hazo hazo yake gani sai Hidaya dake masa gizo tana masa karatun bata sonsa.

Saurin rufe ido yay ya juya ya kwanta tare da toshe kunnensa da yamutstsan pillowns dan ya tsani kalmar ban sonka Hamma.

Har akai salla yana daga kwance sai kansa dake masa wani bala'in ciwo yana jin kaman acire masa shi.

Har gari ya waye yay shaaa bai fito ba.
Itako Adda hartai wanka ma ta shirya tana niyya tafiya masallaci.

Jin shiru ba motsin Ammar tin asuba data fito sai tai tinanin ko ya wuce masallaci ne dan duk sallar idi bata wuce shi kamin a fara huɗuba ya fita.

Tuwon data ɗaura ta sauke zata tuƙa taji sallamar Yahya daga waje yana ƙwalama Ammar kira.

Leƙowa yay suka gaisa da Adda yake tambayrta ko aboki na ciki.

"A'a wai bai fito ba dama"

"Ehh wlh ina ta kiran wayarsa ma akashe"

"To bari na duba maka amma ina tinanin da ƙyar in bai tafi ba"

Kwance ta sameshi dafe da kansa.
Kaɗa kai tai ta ƙarasa wurinsa.

"Ammar lapia"?

Shiru bai bata amsa ba.

"Ammar" ta ƙara kiran sunansa.

"Uhhmmm" kawai ya iya cemata.

"mai ya faru ?menene naji jikinka zafi"

"Kaina ne zai faɗo Adda ki mani adua"

riƙe kan tayi ta masa adu'a.
A kafaɗarta ya kwantar da kansa.

Murya can ƙasa yace da ita,"Adda Hidaya bata sona"

"tana sonka mana kafi kowa sani ai"

"nafa gani fa a idonta Adda,har kuka take saboda nace ba ita ba wani"

"Hmm yanzu dai ka tashi dan Allah haba sai kace ba namiji ba,ita datake mace ta iya jurewa bare kai dan Allah ka tashi ni bansan ciwo ya kamaka"

"bazan iya tashi ba faɗuwa zanyi,dan Allah kisa hannunki kicire mani kalamann nata bana son jinsu"

Kallonsa Adda tai,har zata faɗa masa wanna Faruq Hidaya ke nufi sai kuma kawai ta ƙyalesa shima ya ɗana.

Yahya ta kira tace yaje ya lallamesa suzo su tafi.
Da ƙyar Yahya ya lallaɓasa ya tashi yayo alwala suka tafi masallacin idi.

Da suka dawo gida ya wuto dan bai biya gidan Inna ba saboda in yaje komai zai iya faruwa.

Yana ma Adda sannu da gida tare da barka da salla ya shiga ɗakinsa ya kwanta.

Sauke tuwon Adda kenan Hidaya ta shigo cike da murna,ta wuyan Adda ta saƙalo hannayenta tace bark d salla Adda na.

"barknki ƙanwata munyi salla lapia"

HIDAYAH NOOR completed.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang