Page 78.

1.1K 82 1
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


           *Story~Written~Edited*
            *_By Miss Xerks_*🌺



      *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*NOT EDITED*

*78*
 
Tsawon kwanaki huɗu Mansur yayi yana jinyar Hidaya cikin tsantsar kulawarsa dan ko aiki bai fita karo na biyu daya kuma ɗaukan hutu.Nata ɓangaren duk abinda yake so tana yinsa ba musu ba gardama,abinci daya kawo ko baice taci ba zata buɗa taci hakana magani idan yana wani abin da kanta zata ɗauka tasha.ba nurƙufanci idan yayi magana zata basa amsar duk abinda yake so,Abu ɗaya ke fito da Mansur daga ɗakinta zuwa masallaci daga nan kuma idan ya dawo yana katararta mai take so,ina ke ciwo,ya take jin jikinta duk sune tambayansa tare da adu'an samun ingantacciyan lapia mai ɗorewa.Ko bacci Mansur zaiyi topa sai tana liƙe jikinsa data motsa zai farka itama kuma harta saba da hakan.ai dataji ras yanzu bako inda ke ciwo saita koma gidan jiya.tin asuba da sunkai sallah yay mata magana bata amsa ba sai harara da take binsa da ita.da wuri ya tashi ya wuce zuwa ɗakinsa yay wankansa ya shirya zuwa fita aiki dan student sun kusa fara exms,koda ya fito kitchen yaje ya ɗora mata break fast ya wuto dashi ɗakinta.Daya gaisheta bata amsa ba hakana dazai fita yana ta zan fita saina dawo amma ko ci kanka batace masa ba,sai daya girgiza kai sannan ya rataya jakansa yay waje tare da cewan ta kula masa da kanta .Duk wannan yinin ranar tin shigowar safe bai kuma shigo mata ba hakan kuma yay mata daɗi dan ita ganinsa ma takurawa ce atare da ita.Washe gari ma haka,ganin har kwana biyu bataji ɗuriyarsa ba gashi ana neman a kuma yunwa zata kuma cin ubanta sai ta fara jin haushin kanta bai kamaci ta dinƙa masa duk abinda take masa ba tinda. Fitowarta a wanka bayan ta shirya ta fita zuwa parlo karo na biyu kenan data taɓa fita dan kanta,zama kan kujera tayi tai shiru tsawon awanni bata koji motsinsa ba.Tashi tai tana ƙarema parlon kallo to ina ne hanyar ɗakinsa,hangen wata ƙofa datai ta buɗa sai taga corridor ne.Tsintar kanta tayi da shiga damuwa,dawowa tai ta buɗa ƙofan parlo ta fita.Daga can ta hangi mai gadin da sai ayau ta taɓa ganinsa shima ya taɓa ganinta dan duk shi azatonsa Mansur shi ɗaya ne a gidan sai randa zasu asibiti yake cemasa zai kai madam ne.Da sauri mai gadin ya taso ya ƙaraso gareta da rissina mata, "Ina kwana Hajjajju" , "ina kwana,ya aiki"?
"alhmdl Hajiya,mai ake da buƙata?",Ɗan shiru tayi tana ƙarema compound ɗin kallo,ganin bataga motarsa ba tace dashi, "ammm dama nace ya fita ne"?"ehhh Hajiya ya fita ɗazu da safe ,yaje asibiti amso magani"Gabanta ne ya faɗi ras, "Baya da lafia ne"?,"ehhh Hajiya baya da lafiya kusan kwana biyu ma kenan,ashe baki sani ba" , "to amma miyasa bai faɗan ba" tai maganar muryarta na rawa.Washe baki mai gadin yay yace, "Hajiya kenan,bai son ɗaga maki hankali ne amma ai naga jikin da damadama tinda da kansa ya tuƙa mota yau saɓanin jiya da sai napep ya hau". Bata ce masa komi ba ta juya ta koma parlo,zama tai kan kujera da rafka uban tagumi kawai sai jin hawaye tayi tap a cikin idonta,anya kuwa bazata bisa ba,Tana nan zaune jugum dan har akai la'asar kasa tashi tai,jin murɗawan ƙofa ta ɗago tana duban wurin Mansur ne ya shigo dafe da kansa sai ledan magani dake a ɗayan hannunsa yana haɗa hanya da alamu jiri ke ɗibansa.hankali tashe da sauri ta tashi ta riƙosa ganin zai faɗi,kamosa tayi zuwa kan kujera ya girgiza mata kai da a'a. "to ina zan kaika"
"bari na wuce ɗaki na idan na zauna anan bazan iya tashi ba", Ledar hannunsa ta amsa ta riƙa da kamasa sose yay mata nuni da ƙofan dake baya da ɗakinta suka shiga zuwa ɗakinsa.Tin kamin ta kwantar dashi ya faɗa kan gadon dafe da kansa yana runtse ido sai juyi yake,ƙafafunsa yake mimmiƙarwa tare da damƙe pillow yana ambaton innalillahi.Tini hawayen dasuka cika idonta suka shiga zuba.hannayensa ta kama ta riƙe tana kuka ta kasa ce masa sannu.Buɗa idanunsa yay ya kalleta yaga itama shi ɗin take kallo,girgiza mata kai yayi yace, "um-um" ya faɗi da son ta daina kukan da take.Goge hawayen tayi cikin muryan kuka tace dashi, "sannu" ,Ɗaga mata kai kawai yayi,dafa kansa tai ta shiga karanto masa adu'oi ahaka har ya samu yayi bacci.Ganin ya sami bacci ta miƙe ta shiga kitchen ta dafa jallof na taliya ta dawo bayan data zuba ta cikin wata warm cooler,Akan madai2cn center table dake a ɗakin ta aje.Kusa dashi ta dawo ta zauna tana kallonsa har ya rame,ashe shirun dataji da dalili.ganin irin gumin dake keto masa ta cire ɗankwalinta ta shiga goge masa.Miƙewa tayi ta kunna AC sannan ta dawo ta kwantar da kanta daga jikinsa kaɗankaɗan sai tai murmushi inda take tsinkayar sanyin acikin ranta.Sai daya sami bacci sosai sannan ya farka,sannu ta masa ta kamasa ya miƙe zaune ta jingina dashi jikin gadon."Sannu" tace ,sai da yay murmushi sannan yace yauwa,adu'an samun sauƙi ta masa tukunna ta kamashi ta rakasa toilet,kasancewar juwar dake ɗibansa bai jima aciki ba shap2 yay wankan ya fito.Tana zaune ganin ya fito ɗaure da towel iyaka ƙugunsa yana goge jiki tai saurin rufe idonta tare da miƙewa ta fita.Sai data tabbar daya gama kimtsawa sannan ta shigo kanta ƙasa ta nufa abincin ta zuba ta shiga bashi.a wannan tsawon kwanaki da yay ba lafiya itake ta jinyarsa tana bashi kulawa yanda ya kamata.dake ta iya driving ita ke ɗaukansa kullum ta kaisa ai masa alura,alhmdl jiki yay sauƙi sose su Hajiya duk sunzo sun dubashi hakama su Inna duk ita ta kirasu ta faɗi masu.ba ƙaramin daɗi Mansur yaji ba da yanda Hidaya ta kulashi dan koda yaji sauƙin sai yaƙi tashi yace shi bai warke ba ƙwamma ya zauna hakan,cikin shagwaɓa ta kai masa dukan wasa ita gaskiya ya miƙe bata son wannan abin ba'a wasa da ciwo.da daren yau suna zaune bayan sallan isha'i yana cike wasu takardu ita kuma kanta na kwance saman kafaɗarsa bacci na son ɗaukanta wayarsa tayi ruri.bai jinkirta ba ya ɗaga ganin sunan hydar ajiki,bayan gaisawarsu hydar ke cemasa tafiyar nan tasu gobe,"oak goben ne kenan?", "ƙwarai kuwa saika zama cikin shiri dan da wuri zamu wuce", Mansur yace dashi, "zamu kai wata nawa kenan?", "ehhh to zamu kai uku zuwa huɗu", "biyar fa kace hydar", sai da hydar yayi dariya sannan yace, "kana nufin ya maka yawa kenan bazaka iya tafiya ka bar madam ba", "a'a bawai hakana bane,banda matsala da ita ai,Allah dai ya kaimu goben" daga nan sunkai sallama.aje wayarsa ya ɗago da duban hidaya wadda tin cewar wata huɗu ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa.gira ya ɗaga mata da cewan, "yadai?" fuskarta a tsuke kaman wadda ta shirya ma kuka tace, "ina zakaje?", "ohh na manta ban faɗi maki ba,wani course zamu je can enugu zamuyi wata shida zuwa bakwai acan....". Ba kai ga ƙarasa ba tace, "amma banda kai ko", dariyar datazo masa ya gimtse, "bakiji bayanin da nake maki tin farko bane".na tsawon mintina uku ta bisa da kallo sannan tace, "banji ba", buɗa baki yay zai maimaita mata tace, "ni bance ba barshi", "amma ai yana da kyau na sanar dake" ," ka barshi kawai nace banso tinda baka da matsala dani" nan taja ta kwanta da juya masa baya batare data ƙara ce masa komi ba duk da maganar da yake mata ƙarshe tasa hannayenta ta toshe kunnuwan nata,murmushi yay ya zago ta gabanta ya tsuguna, "to kuma kin kwanta bazaki tashi ki tayani haɗa kayana ba". Idonta rufe tayi masa shiru haka yay ta maganarsa taƙi ce masa komi.duba da dare nayi ya miƙe da kansa ya haɗa kayansa cikin trolly.washe gari da sassafe ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗora masu breakfast,Allah Allah take ta kammala kar Mansur ya tashi aiko har ta gama bai farka ba nan ta jera masa a center table ɗinsa taja ƙofan tasa key ta datsesa a ɗakin ta fita tana dariya.sai tara ya tashi ,subhanallah ya faɗi ganin lokaci da yayi,da sauri ya sakko ya faɗa toilet yayo wanka ya shirya,abincin daya gani ya buɗa,doya ce soye da ƙwai da miyan ƙwai akai sai ketchup data ijje.zubawa yay yaci bayan daya kammala yay hamdala ya miƙe da rataya jakarsa yaja trolly,murɗa handle ɗin dazai yaji ƙofan rufe,sake murɗawa ya tabbatar da a rufen take.mamaki ya kama can kuma ya saki murmushi ya tabbata aikin Hidaya ne,beside drower ya buɗa ya ɗauko spare key yasa ya buɗa,fitowarsa parlo wani daddaɗan ƙamshi ya daki hancinsa nan take ya lumshe ido da jan dogon numfashi kamin daga bisani ya buɗa idanunsa ya sauke su akan Hidaya wadda ke kwance kan doguwan kujera tana bacci.gareta ya ƙarasa ya tsuguna yana mai kallon fuskarta tare dasa hannu ya shafota,buɗa idonta a hanƙali da sauri ta miƙe zaune tana daɗa waresu,da mamaki take kallonsa kamin tace, "kayii ta ina ka fito"? "ta inda kike kulleni",ɓata fuska tai ta dubesa kaɗan, "to yanzu ina zaka", "tafiya mana", "to tafiyanne harda su trolly kaman wanda zai shekara can", "ummm kinsan ko kwana ɗaya mutum zaiyi yana da kyau ya tanadi kayan sawa sa baka zauna aƙazance ba bare kuma nida zanyi watanni da yawa". Sarkin kuka idonta tap da ƙwalla tace, "to wai tafiyan dole ne"? "umm dole ne a wurina mana tinda nema zan fita", "ni kuma fa,sai na zauna ni ɗaya agidan kaman wata mayya", "to aike daɗinki ne,nida zamana ke takura maki agidan ai kinga hakan bazai dameki ba", shi wannan ya daina sona yanzu shine abinda tace cikin ranta nan ta miƙe zata wuce ɗaki ya dakatar da ita da kama hannunta,wani iri taji take abinda takeji game dashi a ƴan kwanakin nan ya motsa mata. kicikicin ƙwace ta shiga yi ta kasa.kanta ƙasa yasa hannu a haɓarta ya ɗago da fuskarta yana kallonta yace ,"to miye na kukan kuma?", "baka ce ban damu dakai ba", "to naji yi haƙuri kin damu dani,amma kisan duk da hakan bazan fasa tafiyana ba,na lura zamana agidannan na takuraki da yawa,kuma sannan ke ba sona kike ba ƙwamma kawai naje can idan Allah yasa na sami wata saina...", hawayen daya shiga zuba saman kuncinta da yanda take cije haƙora tana hura hanci yasasa shiru bai ƙarasa zancen ba.zai share mata ta ture hannunsa yayinda ta haɗe fuska kaman mai shirin dambe. "Hidaya gaskiya na faɗa,ba kya sona kinga zamana a gidannan baida wani amfani tinda takura maki nike,bana son ganinki cikin damuwa Hidaya,wlh ina sonki,ina sonki ina sonki fiye da yanda kike tinani,"
Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyarta tai ƙasa da kanta tana murza zoben dake hannunta.cikin sanyi murya yace da ita, "toni zan wuce,sai Allah ya dawo dani ko,ki kula da kanki sose kinji,na zuba maki kuɗi a account ɗinki ga motata nan zan barta anan in yaso saiki na amfani da ita wajen zuwa school".hannun trolly nasa yaja zai wuce tace, "saboda bana sonka shine zaka bar gidan?", ɗaga mata kai da faɗin ƙwarai kuwa,kaman wata mai koyan magana tace dashi, "to to to". Kallo yabita dashi yanda take tura baki gaba. "to to me?",shiru tayi ta kasa kuma cewa komi sai juya zoben dake yatsanta take."umm ina jinki to to me?" , "to to ai nima ina sonka" tai maganar a hanƙali yanda bazaiji ba.banji ba mi kika ce,sai data ɗan ɗago ta kallesa tai wani narai2 da fuska sannan ta kuma cewa nima ina sonka,cike da annashuwa ya fitar da murmushi mai sauti ya kuma matso da kunnensa yace banji ba,da cune fuska datai ta shiga dukan ƙafa tana Allah kaji yace nifa da gasken banji ba nadai ji kince nima amma banji ƙarshen ba kinsan ina da matsalan kunne,a'a wayo zaka mani,kinsan da gaske banji to shikeannan tinda bazaki maimaita ba na haƙura bari na tafi karna makara,da sauri tace haka fa nace i luv you ta faɗi da wata sarƙaƙƙiyar murya mai kashe jik,ba shiri ya juyo da fitar da wata iska mai ɗumi daga bakinsa,suna haɗa ido ta saurin juyawa tare da rufe idanuwanta,takowa yay ya rungumeta ta baya gami da ziro fuskarsa ta kafaɗarta,cikin wata iriyar murya yace, "plsss said if again",kasa cewa komi tai sai sauke numfashi da tayi.jin hannunsa saman mararta tsam ya matse ta ƙwace tayi ɗakinsa da gudu ya bita,tsayawarta taji ya ficikota kan gado ta faɗo samansa,ƙunshe kanta tayi cikin ƙirjinsa tana juya kanta wanda hakan ya fara sasa shiga wani yanayi daman duk zaman da yake dakewa kawai yake,cikin kunnenta yace, "kin kashen jiki da wannan kalmar taki,ita na jima ina biɗa daga bakinki,ki ƙara faɗi naji kinji" ya faɗi yana mai ƙara matsota jikinsa.jin shirunta kaman wadda ruwa ya canye ya hura mata iska cikin kunne,maƙe kafaɗa tayi tace ai ba abnci bane,hmmm wlh idan har daga bakinki zan jita ta fi mani abinci sau dubu,buttol na rigansa ta cire ta kama gefe da sawa cikin bakinta da ƙarfi tace, "i lub u i luv you so much, "I luv you too noor," da sauri ta ɗago tana dubansa,ido ya buɗa ya dubeta da ɗaga mata gira,sauka tayi daga jikinsa ta koma gefe,tashi shima yayi ya kamo hannnunta duba da yanda ta ɓata rai"whats wrong my noor"?, bana son wannan sunan,ba kya so?" ɗaga masa kai tayi umm bana so.hannyensa biyu yasa ya kama fuskarta,"kina sona",ɗaga masa kai tayi idonta a ƙasa,to kiso abinda nike so,girgiza masa kai tayi nidai ka sauya mani wani,sai daya sauke numfashi sannan yace noor miyasa bazaki sakawa zuciyata farincikin da ta ke son sawa a saman fuskarki  ba,kaɗa masa kai tayi da cewan a'a ba haka bane dan ita harga Allah bata son wannan sunan.to ki amsa sunan domin ita ta baki saboda tsantsr so da ƙaunar da take maki,tinda kika shigo cikinta kika gama hasketa da hasken ƙaunarki,ki daure ki amsa mata sunan data baki kinji one nd only,ɗauke da wani sanyayyen murmushi tace na amsa idan har hakan zai saukar da ffarinciki,jin daɗi,walwala da nishaɗi atare da mijina abin ƙaunata abin alfaharina.jin daɗin kalaminta Mansur ya janyota jikinsa yana mai lumshe ido har na tsawon lokaci sannan ya saketa ya tallabi fuskarta da kallon laɓɓanta kamin daga bisani ya ɗora bakinsa akai.

GOES TO YOU ASEYYA NOVELLA'S LODGE,TANX FOR UR SUPPORT.

_SHARE AND COMMNTS._

*Xerks*✍🏼

HIDAYAH NOOR completed.Onde histórias criam vida. Descubra agora