Page 44

1.1K 80 5
                                        

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                      🌀🌀🌀🌀🌀






            *Story~Written~Edited*
                       *_By Mss Xerks_*🌺




           *Devoted to Ummi Aisha*





*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...





*44*

Daren ranar haka kowa ya kwanta cike da damuwa a ransa daga kan Adda har Sadia da Oga.

Ɓangarensu Inna ma cike da danasani da nadama suka koma gida tin kuka na masu daɗi har suka daina.

Hidaya kuwa daren ranar rayashi tayi da kuka gaba ɗaya ta kasa rufe murfin idonta,Hammanta da Adda su kawai take gani a idonta, lamarin Allah kenan mai yanda yaso dama ance kwaɗayi mabuɗin wahala da ace ta tsaya a iya inda Allah ya ajeta da yanzu rayuwarta mai daɗi nan amma son abin duniya daya rufe mata ido harta walaƙanta wasu gashi ita ayanzu bata cikinsa su da suka barwa Allah komi nasu gashi ya wadata su danasu na kansu ba cin gajiyar wani ba.

          ****

Washe gari da safe 7 Sadia ta fito ta haɗa breakfast ta jere a mazauninsa kaman yanda ta saba.

Koda ta gama taje ɗakin Ammar ta murɗa handle ta jisa a rufe ,anata tinanin bacci yake dan haka ta ƙyalesa ta koma ɗaki.

Wanka tayi ta shirya cikin ƙananun kayanta data saba sawa koda yaushe dan ita bata son kaya masu nauyi ko kaɗan indai ba dole ne ya kamata sawar ba.

Jugum tayi zaune kan gado tana tinani bayan data gama shirinta wadda ko powder yau bata shafa ba.

Ganin 9 ta kusa ta dawo parlo ta zauna ta jima nan zaune shiru Ammar bai fito ba nan ta kuma miƙewa zuwa ɗakinsa tai ta knocking shiru hakan yasa ta sakko ƙasa ko yana ɗakin ƙasa nan ma taje ta ta faman knocking babu alama da mutum ciki.

Da tarin damuwa fal aranta dana sani abinda tayi kawai take har 10:30 tayi,kallon TV take amma hankalinta gaba ɗaya bai kai.

Tashi tai ƙwalla tap idonta ta koma sama tana zuwa ta tadda ɗakin nasa a buɗe, ajiyar zuciya ta sauke da murmushi ta faɗa ɗakin.

Zaune yake kan darduma ya idda sallar walaha yana jan carbi,kusa dashi ta zauna har ya shafa adu'a.

Baiko kalla inda take ba ya miƙe ya haye kan gado,da shagwaɓa ta taso ta hau itama daga jikinsa ta manne tare da kama maɓallin rigar dake jinsa.

"shine jiya ka gudu ka barni ko, bamu kwana tare ba duk naita kewar jikinka"

Ta wutsiyar idonsa kawai ya kalleta baice da ita ƙala ba yaja pillow tare da gyara kwanciyar da yayi.

"Mahbub dan Allah kayi haƙuri kaji bazan sake ba"

"yanzu Sadia abinda kikayi kin kyauta kenan, ban taɓa tinaninki da aikata haka ba"

"wlh Faruq bawai dan walaƙanci ko cin mutunci nayi hakan ba,na rantse maka da Allah har cikin raina da niyyar taimakonsu na gayyatosu gidannan da kuma tinanin tinda Hidaya tayi nadama zata fito fili ta bayyanawa duniya cewar sharri ta maka na cewan zakai zina da ita ko sauran farincikinka daya rage ya dawo...."

"daga nan kuma sai kika saka Adda ta walaƙantasu ko"

Girgiza masa kai tayi duk da bai kallonta, "a'a wlh dana san hakan ma zai faru bazan soma kiranta ba...."

"kun bani mamaki daga ke har Adda, bai kamaci ace kun walaƙantasu ba dan kuna masu arziƙi ayanzu saboda ramuwar abinda suka maku duba da yanayin da suke ciki, baku tinanin Allahn daya baku aron dukiyar ya amsa kayarsa tinda baku tabbacin zaku dawwama cikinta su kuma ya azurtasu,ko ba komi darajar sunan data amsa na sunan mahaifiya duk da laifin data maku bata cancanci kuyi mata haka ba, ku ko tausayinta ba kuji ba ƙafarta fa har ruwa take amma ahaka kuke kiran wani yajata yay waje da ita haba kun bani kunya wlh"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now