Page 71.

1.1K 79 2
                                        

*HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


        *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks_*🌺



           *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



*71*

Suna ƙarasawa balcony Mua'azzam ya shimfiɗa masu carpet ɗin dake hannunsa nan suka cire takalmansu suka zauna.

Kaman yanda suka saba koda yaushe kamin su fara karatu wani daga cikinsu zai buɗa masu da adu'a.

Maryam ita ta masu adu'an sannan Mua'azzam ya shiga watso masu tambayoyi akan abubuwan daya koya masu jiya.

Mu'azzam ɗan level 4,kamuwar kai da yanda su Hidaya ke son karatu yasa jininsu ya haɗu tin a library da sukaje karatu hakan yasa suma suka riƙesa da muhimmanci duba da shima ba irin sha3 maza bane abinda ya kaisa kawai shi yake dan haka kullum idan yana free suke fitowa yay masu tutorial kuma suna ƙaruwa sose haka kuma suna bashi girmansa dan ya girmeme masu a shekaru kusan ya basu 7yrs.

Duƙufe suke da kawuna suna ta karatu har alerm ɗin daya saita ya buga.
Dubawa yay ya katse kamin ya ɗago da idonsa ya kallesu yace.

"tom time ya cika fa ku tashi maza kar malamin nan ya rufe maku ƙofa"

To Maryam tace nan ta shiga tattara takardunta.

Ɗan lokacin daya ɗauka yana ta kallon Hidaya wadda kanta ke ƙasa bata sani ba ya saki murmushi da cewan.

"Beauty lafiya dai naga kin ɓata rai kina faman ƙunƙuni ke ɗaya,ko an maki wani abinne?"

Bakin nan agaba data turo tace, "wlh tinanin tafiyar nan nike ,haba an tashi anma mutane hall mai shegen nisa"

Ƴar dariya yayi yace, "to kitashi Maryam saita goyaki"

Baki Maryam ta buɗa da faɗin, "ahhhh tab na goya wannan ai baya na ya gama aiki,dalla ki tashi mu tafi mutum sai shegen son jiki"

"dalla can ni dake aga wanda yafi wani son jiki,ni wlh ma bana son lecture ɗin guy nan ɗan ƙarami dashi sai uban iyayi da rainin hanƙali"

"Hmmmm lalle ne Beauty wlh kin raina bawan Allah nan da yawa kullum sai kinci masa face,kinga ki tashi ku tafi time na daɗa ƙurewa"

Yatsina fuska tai tace, "nifa bazani ba yau,Maryam kawai ki wuce kin mani attendance...."

Bata ƙarasa ba Maryam tace, "wannan ne kuma baki isa ba saikin miƙe mun tafi,ana shirin exms ɗin kina kiran daina shiga lecture bayan kin san malaman nan sunfi rashin mutunci a zuwan time ɗin nan"

Mu'azzam dake talbe da baɓa yace, "ko ba kice ba zuwanta dole,kinga Beauty babu dalilin da zakice baki shigan lecture dan haka tashi ku tafi kamin muyi faɗa"

Maryam ta sake ɗora mata da ,

"ki tashi dan Allah ko yauma sai kinja an rufe mana ƙofa ne,ke ƙwamma ki ƙarfafa jikinki ma kinsan 3dayz zamu jera nutrition na mana lecture mu da bamu taɓa shiga lecture ɗinsa ba ni har tsoron ma goben nike wlh"

Da dariya Mu'azzam yace, "wato ke har kin fara tsorata kenan ai na faɗa maku mutuminn baida imani tin lokacinmu haka yake tsula tsiya,kune ai idan nace ku shiga sai kuce ku ba yanzu ba ai nutrition ɗin ba wuya, hmmm zaku gauraya ne 2mrrw ana zaku gane ba ƙaramin abu bane shima"

Maryam tace, "kasan Allah Mu'azzam tinda yay postng nike a tsorace ,bafa mu taɓa attending lecture nasa ba ko sau ɗaya gashi ance yana sane da list ɗin masu shiga ,aini yau inaga tsayuwar dare ma zan masa"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now