Page 75.

1.1K 79 13
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀

 
         *Story~Written~Edited*
           *_By Miss Xerks_*🌺




     *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...




*75*

Ya rage saura sati biyu biki Mansur ya shirya ya wuce Pataskum da ɗimbin saƙon ƙannensa na ya gaida masu da Antynsu.

Tana ɗaki kwance kan gado tana chart Inna taje ta sameta da isar mata cewan tai baƙo tace ita sam wlh bata zuwa.

Duk da ɓacin ran da Inna ta nuna mata amma ƙememe tai biris tace ai ba ita ta gayyatosa ba har saida Inna tace zata kira mata Baffa sannan ta miƙe ta yafa mayafinta ta fita tana kumbure2.

A farlon Baffa ta samesa zaune saman kujera yana danna waya,ganinta ya ɗago da murmushi yana kallonta harta ƙaraso ta zauna kan kujerar dake gefe dashi ta maida fuskarta saitin ƙofa.

Murmusawa ya ɗanyi yaci gaba da danna wayarsa,tsawon mintina kusan biyar jin baiyi magana ba ta miƙe da jan dogon tsoki zata fita taji yace,

"Irfan"

Ai ba shiri ta waigo jin yaron ya fito da gudu daga ɗakin Baffa yana, "na'am Abbaa babu dodo"

_Tare sukazo da Mukhtar suna shigowa ya sashi a ɗakin Baffa yace ya zauna yay shiru har sai ya kira sunansa tukunna in bahaka ba dodo zaizo ya canye shi._

Da murnarta ta dawo tare da faɗin,
"Muntari nah" ta tafi da niyyar rungume yaron.

Harga Allah sunan data ambata yay masa pepe cikin rai kuma itama sarai dan cin mutunci ta faɗi amma sai ya kawar da saurin miƙewa shima yay wurin Irfan dan karta ɗaukesa.

yaje kamo yaron dai2 da miƙa nata itama hannunsu ya jone nan ta take Mansur yaji wani shock na daban da sauri itama ta janye hannunta tana ɓalla masa harara.

"ka kauce min"

ta faɗi da ranƙwafowa zata miƙa hannu ta kamo Mukhtar.

Ranƙwafo da kansa shima yay dai2 da saitin fuskarta yana dubanta.

"kina so na baki shi"?

Ɗagowa tai tana masa banzan kallo yace da ita.

"babu abinda zai kasance a saman fuskarki ya bayar da rashin kyau,komi kyau yake maki idan kika yisa,ko kinsan wannan ɓata ran ma wani kyau na daban ya ƙarawa fuskarki, kici gaba dayi ina so"

Jin kalamar "ina so" aiko nan take ta ɗan saketa daga tsuketan datai dan bata son abinda zaisa sa jin daɗi.

"dan Allah ka kauce mani na ɗauki ɗana tsawon wata guda da mako biyu kuka nisanta ni dashi kaman wani cikinku yay mani naƙudarsa"

"kina son nabaki shi"
Ya ƙara mata tambayar akaro na biyu.

Banza tai masa gami da jan ɗan siririn tsoki,

"hmmm ki murmushi tukunna wlh saina miƙo maki shi in bahaka ba ko na ɗau yarona mu koma inda muka fito"

Kallon kama maidani ƙaramar yarinya tai masa wato ita zaima wayo, nan tai zata turesa aiko yana dariya yace da Mukhtar ,

"Boy sauri kaje kace da Inna ina gaidata kaji amma fa karka dawo yanzun"

"to" Irfan yace yay waje da gudu yana ƙwala kiran Inna Abbaa na gaidaki.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now