Page 59.

1K 83 16
                                        

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


      *Story~Written~Edited*
            *_By Mss Xerks_*🌺



      *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...


*59*

Ganinta tana kuka Inna ta dafata da tausaya tace.

"minene Hidaya?ko jikin ne?"

Sautin kukanta ne ya fito ta ɗago tare da girgizama Inna kai.

"to mine kuma na kuka,ni gaskiya inagama Hidaya zaifi maki ki haƙura da Ammar dan bana son wani tashin hankalin nan gaba...."

Bata ƙarasa maganar ba tai saurin sa hannunta ta rufe bakin Inna tana girgiza kai.

"a'a Inna kiyi min dai adu'a,nasan alkhairi nane"

Batasan tashin hanƙalin ƴar tata hakan yasa tace, "to idan da alkhairi Allah ya tabbatar sai dai kuma ya kamata kija aji ko"

"amin ,sai dai Inna ina tsoron na rasashi" tace tare da goge hawayenta inda ta jinginar da kanta jikin gadon.

"bazaki rasashi ba tinda dai shima har yanzu yana sonki, sai dai dolen dai ki dinga nuna masa bashike gabanki ba ayanzu"

"to shikenan Inna"

Hira suke sama2 da Inna dan ta ɗebe mata kewar damuwarta saboda likita yanzu yace kar adinga barinta tana yawan tinani.

Sunata hirar harda labarin daya sata dariya a wanda Inna ta bata likita ya shigo yasa mata drip da allurai dazai mata sannan ya fita.

Alokacin Baffa ya dawo suka zo shida su Umman Sabira nan suka zauna ita kuma Inna ya ɗauketa suka koma gida ta shiryo ta dawo.

Wajen ɗaya drip ya ƙare Dr yay ma Nurse Rashida waya yace idan tana ciki dan Allah taje room 4 akwai patient nanan yasa mata drip so idan ya ƙare saita cire mata.

Oak tace dashi dama babu abinda take hakan yasa ta miƙe da azama ta nufi ɗakin.

Tana zuwa da shigarta tai sallama inda ta tarar da Inna zaune Hidaya ko na bacci saisu Sabira dake zaune suma.

Sam Inna ma bata shaidata ba dan shekarun da yawa anjima ba'a haɗu ba ganin alaman hakan Rashida tace ,

"Inna baki ganeni ba ko"

Kallonta Inna tayi tace, "umm likita ban shaidaki ba kinsan jiyan duk ana cikin ruɗu banace na ganeki ba"

Murmushi Rashida tayi tace, "Inna Rashida ce fa idan baki manta sunan ba ƙawar Hidaya"

Tafa hannu Inna tayi da riƙe haɓa tace,

"laaaa Rashida,yo aini wlh ban shaidaki ba kwatakwata Allah sarki kinga ashe da rabon zamu kuma ganawa ,sannu ya kike ya wurin iyayen naki"?

"wlh kuwa dai Inna kowa na lafiya,ashe Hidaya ce ba lafiya"

"ehhh wlh itace kinganta nan anma jikinma da sauƙi,dama anan kike aiki"

"ehh to ina dai ɗan taɓawa anan ɗin idan na shigo garin amma har yanzu ina can adamawa yanzu nazo gidan ƙanwan Mama nane"

"Allah sarki sannunki, amma kinyi aure ko"

"ummm Inna nayi harma da yaro na yanan Mus'ab"

"eye masha'Allahu to Allah ya raya, idan ta tashi ko zan faɗa mata kin shigo"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now