*Xerks*✍🏼
🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*23*
A bakin Internatonal hospital Muhammad yay parking.
Da shigarsu ciki Ammar ya sami su Mommy a zaune dukansu sai kuka suke.Tsugunawa yay yana gaida Mommy,kasa amsa masa da baki tai sai ɗaga kai da taimasa idonta har ya kumbura saboda kuka.
Doctr ne ya fito daga room ɗin da Surayya take,Mommy ya kalla yace da ita an sami wanda take nema ɗin.?
Ehh Mommy tace dashi "gashi yazo" ta faɗa tana masa nuni da Ammar dake tsaye.
Miƙa masa hannu likitan yay suka gaisa tare da cemasa ya shiga daga ciki amma dan Allah kar ai abinda zai ƙara ɗaga hankalinta.
Shidai Ammar binsu da kallo kawai yake da mamakin jin abinda likitan ke bayani wai ciwon zuciya ke gareta.
Da hawaye nabin fuskar Mommy ta juyo da kallonta ga Ammar,nuni ta masa da ɗakin da Surry ke ciki tace,"bismilla ka shiga ciki sati guda kenan tana ambaton sunanka,yau kuma tace ataimaka mata akiraka tana son ganinka"
Ƙofar room ɗin ya buɗa ya shiga,kwance Ya hangeta kan gado da drip a hannunta banda oxygn da aka sa mata.
A hanzarce ya ƙarasa wurinta ,gabansa ba ƙaramin faɗuwa yay ba daya ɗora idonsa akanta,ta ƙanjame kaman ba Surry ba ƙashi kawai ke magana ajikinta fuskar tayi fayau duk ƙibarta babu ita kai da ganinta kasan ba ƙaramin jin jiki take ba.
A wahalce ta buɗe baki idonta a rufe ta kirayi sunansa."Ammar"
"na'am Surayya ya akai kinka gane nine..sannu kinji""ko a wanne hali nake ƙamshinka bazai taɓa ɓoyenba Ammar...tayani ɗaga murfin idona ina son maka kallon ƙarshe"
A sanyaye ya matsa kusa da ita yasa hannunsa dake rawa ya buɗe mata idanuwanta da ita bata iyawa.
A firgice ya ɗanja da baya lokacin daya zuba ƙwayar idonsa cikin nata,jini ne kwance acikinsa kaman an tsiyaya mata shi.
Kallota kawai yake hankalinsa atashe,"wai Surayya mai yaja maki wannan ciwon?,yaushe kika kwanta haka?"
Murmushi ta fitar mai sauti wanda ta jima batai ba murya a disashe tace dashi,"ciwon So...soyayyarka Ammar ita tasani a wannan halin..tinda kace na rabu dakai na kwanta haka"
"Sona kuma?"
Hannu ta miƙa a hankali ta kama nasa dake agefen gadon,hannun sanyi tamkar ƙanƙara.
"na rayu da sonka acikin zuciyata gashi yanzuma zan mutu dashi a zuciyata....wlh Ammar har cikin raina nake sonka ni kaina ban san irin wanda nake maba sai dana tsinci kaina a wannan halin na fahimci son gaskiya ne azababbe wanda zaka iya rasa ranka saboda shi"
"ki daina faɗin haka dan Allah,insha'allahu Allah zai tashi kafaɗunki"
"bazan tashi ba.. wlh mutuwa zanyi Ammar,rayuwata bata da amfani matsawar babu kai cikinta...banda burin daya wuce na kasance tare dakai amma banda wannan damar....zan miƙe ne kawai alokacin da kace kana sona zamu kasance inuwa guda..ka yarda zaka aureni ka tausayawa halin da Mommy da Daddy zasu shiga"
Duk da halin datake ciki na atausaya mata da lafuza masu daɗi hakan baisasa sauya fuska ba cikin ɓacin rai yace da ita.
"ki bari dan Allah Surayya mu daina maimaita wannan maganar,na faɗa maki ko kaɗan bazan iya alaƙanta wata da Hidaya ba ita ce kawai zuciyata ta kema so da ƙauna....ki bar ɗauka sona ne ya kwantar dake,ki ɗauka matsayin ciwo ne daga rabbi ya saukar maki dashi dan wata jarabawa"
STAI LEGGENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Narrativa StoricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.