PAGE 19

1.5K 101 3
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



           *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺




           *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

'''SANAZ DEEYAH😍 ki riƙe Soyayyarmu da gaskiya💃🏽,alƙawarin soyayya ni XERKS na riƙe kema SANAZ saiki riƙeta da gaskiya'''.💃🏽

_Ɗungurungun wanga shafi naki ne my dear SANAZ one love ana mugun tare frnd again Sisto na😍😘,aci gaba da gashin DIREBAN GIDANMU Allah ƙara basira._



*19*

A hankali drip ɗin dake saƙale ga hannu Hidaya ke zuba.

Lokaci guda harta rame sose dama ba wata ƙiba gareta ba.

Yaune kawai ta sami daman barci dan kwanan biyunn data fara zazzaɓi sam bata iya yinsa.

Inna ce dake gefenta zaune ta numfasa tare da yima Ammar magana.

"Ammar yau dai ka tashi kaje shagonka tinda jikin nata da sauƙi ba'aje ana ta zama haka ba kace ka daina fita"

Shima numfashin ya sauke cikin ladabi yake ceda Inna,"tom Inna dama inada niyya yau saboda babu kuɗi ma ga hannuna gashi bamu gama biyan likitan kuɗinsa ba"

Adda ce tai magana itama wadda ta cire tagumin da tai ,"gsky dan ɗazu daya zo ma kaga da cewa yayi bazai sa mata ruwan ba sai an basa wancan kuɗin,yanzu kuma kaga ga allurai ma dayace anjima za'a samata kuma dole sai an bashi kuɗinsa ban san ya za'ai ba"

Inna ma cikin damuwa ta ƙara magana ,"to gamu ga Allah sai dai mu roƙi Allah ya kawo sauƙi ,zancen magani ko Allurai kawai ƙyaleshi zamuyi tinda ba kuɗin saya gasu duk masu tsada"

"A'a Inna bari ɗan anjima saina leƙa gidan Maman muhsin akwai wankin dana mata bata ban kuɗin ba saina amso a basa "

"tom shikenna Allah yayi albarka kunji ya ƙara buɗa maku da hanyar samu ya kuma fidda maku da abokan zama na gari"

Atare suka amsa da amin.

Katse tinanin Ammar sukai daya tashi ya tafi zaman babu abinda zaiyi masa ai jikin nata da sauƙi yanzu.

Hannunsa ya zare daga na Hidaya da tin zamansa idanunsa ke akanta,shi kansa har ya faɗa kaman shine mai ciwon.

miƙewa yay ciƙe da tarin damuwa a fuskarsa yace dasu sai ya dawo.

Tsaidashi Inna tai"au bakaci fa abinci ba ko"
"bar abincinn Inna na ƙoshi "

"ina lura dakai fa Ammar kwana ukunn ba wani cin arziƙi kake ba,ko ita datake ciwon ai ci take bare kuma kai.komu duk kaga mun fasa ci ne damuwa ai ba ita zata bata sauƙi ba Allah daya saukar mata shi zai warware mata"

"A'a Inna ai ɗazu dana leƙa wurin Yahya na sami fanke a wurinsa naci"

"tom shikenan sai ka dawo,Allah kiyaye ya bada sa'a"

Da amin ya amsa mata yasa kai ya fita.

Tashi Adda tai ta shiga wanka.
Motsin da Hidaya taine tana kuka ya katse tinanin Inna.

"Inna kaina ki cire mani bana so wayyo Allah na wayyo Adda"

riƙeta Inna tai tana mata adu'a ,shigowar Adda da sauri ta ƙarasa wurin Hidaya ta shiga cire mata allurar drip ɗin daya ƙare har yama fara zuƙan jininta.

HIDAYAH NOOR completed.حيث تعيش القصص. اكتشف الآن