PAGE 6

1.7K 123 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
             *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


            *Story~Written~Edited*
                *_By Mss Xerks🌺_*


            *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*topa wata tace typing ɗina na mata kaɗan dan Allah na daure na ƙara yawon readmore yazama ko 15-20 ne lolx.*
*to karki damu indai kin yarda na dinga karanto maki kina typing ɗin ba 20 bama sai na kaiki har 50 in kina so,kuma namaki alƙawarin editing,amma duk da bansan yawan readmore ɗin danake ba aƙalla nasan ina readmore sama da 2..dan haka kiyi haƙuri ki daure ki riƙe shi ahaka kaman yanda kika ƙagu soon zakiji asalin alaƙar dake tsakanin su Adda da Inna da kuma irin halaccin da Hidaya zataima waɗannan bayan Allah*

*Fans ku biyoni*

*6*

A toilet da Hidaya ke wanka yau dai ta tsaya ta ƙare ma kanta kallo tsaf.

Ɗan turo baki tayi alamun na nuna rashin jin daɗi.

_shikenan wanann shegiyar Bra ɗin nima yanzu zata aureni haka kawai ina zaman zamana_.

Da fushi dai tayi wanka ta gama bayan ta gama shaving.

fitowarta ta tadda Adda tazo suna tare da Inna.
Kusa dasu ta zauna kamin ta tsane tasa kayanta.

Suna cikin hira wata yarinya ta shigo.
Gaida Inna da Adda tayi tare da miƙa masu cingom ɗin da aikota ta kawo na biki.

"ikon Allah yanzu har bikin yazo ƴar nan"
Cewar Innah dake tambayar yarinyar.

"ehhh Inna ga wannan akace ma abawa Hidaya nata na party"

"to angode kice muna masu Allah sanya alkhairi kamin muzo"

Bayan fitar yarinyar Adda ke tambayar Inna wacce ƴace bata gane ta ba.

"ehh ba lalle ai kisanta ba gaskiya dan tare sukaci ƙasa da wannan ƴar" ta nuna Hidaya.

Dariya Hidaya tayi,
"Adda wlh kika ga yarinyar saikin tausaya mata,wata ƴar ɓigil da ita wai ita za'ama aure"

"ke dalla can idan ita yarinya ce ai kema yarinyar ce,dan sai nace ma ta girmeki in ban manta ba da cikinki naje sunanta"

"ahh haba Inna ki daina faɗin haka mana wani yaji ai sai yamani dariya"

Dariya Adda tayi "gskiyrki ƙanwata dama ace dai sun barta tayi karatunta,ko dayake kema fa kin girma da kin fara kula samari zaki ce mani kema aure"

Hmm kawai tace masu ta tashi ta shige ɗaki.

Ɗebo kayan dazata saka tayi ta tsaya tana tinani.

Tagaji dasa kaya ba bra kuma gashi ta tsani bra,rannan Sadia sai data mata tsiya akan hakan.

Tana wannan tinani Adda ta shigo ta sameta.
Kira sunanta tayi ita kuma ta juya tare da amsawa.

"ungo" ta miƙa mata baƙar ledar dake hannunta.

Buɗewa tayi dan ganin maike aciki,Brezia ce sabbi guda biyu fara da baƙa.

Amsa tayi tana ma Adda godia cike da kunya.
"sai kidinga sawa kinka dai yanda kika koma ba kamar da da kike ƴar ɓingil ba"

Kunyace ta kamata tinda take da Adda bata taɓa jin kunyarta ba sai yau.

HIDAYAH NOOR completed.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon