🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*53*
Ta jima kwance tana kukan ciwon dafin son da ya mamaye zuciyarta ayanzu yake neman yi mata illa kamin daga bisani ta miƙe zuwa toilet.
Wanka tayo ta shirya cikin riga da skirt na farar atamfa.ɗinkinta mai ɗan kyau,
gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta datai fayau da ita idanunta duk sunyi loko.
Da tausayin kanta ta ɗau farar powder ta shafa ko lip bam bata shafa ba ta zari mayafinta ta fito parlo inda ta sami Inna zaune tana kallo.
"Inna" ta kirayi sunanta bayan data zauna kusa da ita.
Juyowa Inna tai ta kalleta, "na'am Hidaya lafiya dai ko"
"dan Allah Inna ina son na ɗan leƙa gidansu Sabira mu gaisa kinga mun jima bamu haɗu ba"
"bakiga yamma ta kawo kai ba ki bari kyaje gobe idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya"
Shiru ta ɗanyi na wani lokaci dan bata jin zata iya zama batare data leƙa waje ta ɗan ɗebe kewa ba.
"dan Allah Inna bazan jima ba wlh yanzu zanje na dawo"
"to ai shikenan saiki sauri kamin Baffanki ya dawo da kuma wancan ɗan rigimar taki shima"
Jiki ba ƙwari ta miƙe kaman mai cuta tare da cema Inna saita dawo.
Adawo lafiya tai mata da sake jadadda mata data karta zauna.Flat takalamin ta zira, buɗa gate ɗinta tai karo da Jamil yana niyan knocking.
Da mamaki ta kalleshi shima ya bita da kallo na mamakin kamin daga bisani ta ɗan murmusa tare da gaida shi.
Shima da fara'a saman fuskarsa yace da ita, "gaskiya bazan amsa ba dan ina fishi da ke"
"ahhh haba dai fishi, laifin minayi ai Yaya bai fishi da ƙanwarsa"
"lalle laifi ko kika mani babba tinda har kuka iya tashi daga wancan gidan naku baki sanar dani ba"
"laaa kayi haƙuri kasan ba waya a hannuna kuma ma dai lokacin abubuwa sun ɗan sha kaina shi yasa amma kayi haƙuri"
"hmm ya zanyi haƙuri ai dole na"
"uhmm ya kake ya ayyuka"
"wlh komi lapia ya kk kema da Inna"
"Inna na lafiya"
"Ɗana fa?" ya tambayeta bayan daya kafeta da ido yana murmushi.
"uhmmm Yana ƙalau shima" ta amsa cike da ƙosawa.
"to madalla haka ake so"
Shiru na ɗan lokaci ya biyo baya sannan Jamil ya katse su da cewan, "ammm idan ba damuwa Hidaya ina so muyi wata magana dake mai muhimmanci"
"topa ,ba komi idan bazai ɗau lokaci ba ina jinka idan kuma da tsayi gaskiya sai dai kayi haƙuri dan yanzu ina sauri"
"ehhh to bazan ce ba amma ina zaki haka"
"zanje gidansu Sabira ne kuma Inna tace kar na jima kaga kuma ga 5 har ta kawo kai"
"ahhh to muje mana sai na kaiki ,kinga ma daɗa hira sose ko"
ESTÁS LEYENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficción históricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.