Page 17

1.3K 96 1
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
             *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



          *Story~Written~Edited*
            *_By Mss Xerks_*🌺

        


           *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...




*17*

Da hannunsa ya gogi kafaɗarta ita ko fuskar nan a kumbure.

Da ƴar daria ya kalleta"to wai shan tokan na mine sahibar"

Shiru ta share shi,ganin ma zai takura mata ta miƙe ta shiga ɗaki.

Inna daƙe ɗauraye wani kwano tace "kai kake biye ƴar nan,tin daren shekaranjiya take famanwa mutane miskilanci tsabar shegantaka ko me aka mata oho "

"autarmu kenan Inna,sai da lallaɓawa"

"Hmmm walaƙanci ne kawai wlh,jiya da baka nan babu yanda halima batai da ita kan ta faɗa mike damunta ba amma dan iskanci tai banza da ita.ace mutum babu abinda aka masa yay ta nurƙufanci ina jin haushin abinn wlh"

Dariya Ammar yay inda azuciyarsa yake raya to mai aka mata.

Katsesa Inna tai da,
"Ammar ya kamata dai yau ka daure ka leƙa shagonn kaji ko,tinfa cikin azimi ga yau har sati ga Sallah ko ma'aikata ai sun koma bakin aiki bare kuma ku ƙananu2,jiya ma wurin mutum biyu suka zo nemanka"

"insha'allahu Inna zan koma cikin satinn ma kuwa"

Suna haka kuwa kira ya shigo wayarsa,Nadiya aka rubuta nan danan yay picking.

Da gaisawarsu tace dashi dan Allah ya taimaka mata ɗinki ta kawo masa amma ayau take so ko nawa ne zata biya.

Bai musata ba yace to shikenan ta bar sallahu anan shagon zuwa sallar isha'i tazo ta amsa.

"ka gani ko,na tabbata akwai ma wanda suka kai maka da yawa bakanan "

"wlh ko Inna ita wannan ina samu da yawa a wurinta gaskiya bata ƙyashin biyan konawa akace mata"

"to Allah bada sa'a yanzu maza tashi kai kari kazo ka tafi"

Ɗaki ya shiga ya sami Noor ɗinsa zaune tai jugum da alamu wani abun take tinani.

Kusa da ita ya zauna har saida ya zare mata hannun tagumin tukunna ta sanda zuwansa.

Kallonta yy wanda fuskarta ta nuna da alamu na damuwa atare da ita.

"mai kike tinani"?
"Ba komai"
"Ban yarda ba,karki koyi ƙarya"

Da ƴar ƙwallarta ta kalleshi yay saurin matse idon yana karta bari hawayen su zuba.

"Hamma bana son rabuwa da kai,da kai nake son rayuwa,dan Allah ka kasance tare dani kaji,ina sonka sona har abada"

Numfashi ya sauke inda ya talbi fuskarta,
"to yanzu miye ya faru da har kike tinanin zan iya rabuwa dake umm Baby nah"

A shagwaɓance tace dashi,
"ba kaine rannan saboda nace karka ɗaga wayar budurwarka shine kake jin haushina ko jiya ma kaƙi zuwa gidann kai tafiyarka ma inda bazan ganka ba"

"la'ila ha'ilallah! Haba Noor Allah ba hakana bane"

"to yane"
"jiyafa gaisuwa mukaje gidan yayan su Yahya kuma bamu dawo ba sai dare na dawo agajiye kawai na wuce gida na kwanta Adda bata faɗa maki ba"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now