Page 39

1.2K 90 9
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



          *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks_*🌺





        *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحمن الرحيم...



*39*

Kwanan su Inna uku a asibiti aka sallamesu inda da taimakon wani dayake bada taimako aka bata sanda ƙafa ɗaya.

Sose suka ma mai taxi ɗin daya bugesu godia saboda yanda ya kula dasu.

Koda suka fito sunyi tafiya mai nisa sannan suka nemi wuri suka zauna suna hutawa.

Shiru Inna tayi ta jinginar da kanta ga bangon gidan da suke zaune.

Kallonta Hidaya tayi da tausayin mahaifiyarta tsantsa cikin ranta ta fashe da kuka.

"Inna ina lure dake kwanakinmu a asibitinn maganar ki batafi biyar ba"

Kallon ƴartata tai ta shafa kanta tare da kwanto ta jikinta.

"Hidaya mai yasa rayuwa take garamu haka shikenan mun zama bazamu taɓa dawwama cikin jin daɗi ba arayuwarmu, daga mun fita daga wannan matsala sai mu shiga wata wannan, wacce irin jarabawace haka maike faruwa damu"

"alhaki ,alhaki Inna"

Ta ɗago daga jikin Inna tana kallonta riƙe da hannunta.

"alhakinsu Hamma Inna shine ke binmu ,ki duba duk abinda yake faruwa damu shine abinda muka masu wannan sakayyarsu ce garemu"

Majinar dake hancinta ta zuƙe tare da goge hawayenta.

"sun kasance tare damu tsawon shekaru masu yawa basu taɓa ƙyamatrmu ba,sun bamu kulawar da Baffana ya gaza bamu, saboda wani ɗan ƙaramin abin duniya mai ƙarewa muka walaƙantasu muka ci mutuncinsu ƙarshe muka tozartasu a bainar jama'a wanda takai ga har Hamma ya gogi da baƙin fentin da bamai goge masa saini dana shafa masa"

Da matsanancin sabon kuka ta fashe tare da kallon cikinta.

"ƙarya nake Inna sharri na masa wlh bai aikata abinda na bar ɗinbin jama'a suna tinanin akai ba na ya nemi ya rabani da burcina"

Da zaro ido haɗe da mamaki Inna ta gyara zamanta tana kallon ƴarta.

Da ɗaga kai Hidaya ta maida idonta ƙasa,

"haɗina ne Inna amma ba yin kaina bane da tsaruwar hakan daga Umma Zakiya ,na tsaneshi alokacin daya daɗa maƙale mani yake neman rabani da jin daɗin dana shiga hakan yasa na dinga tinanin ta hanyar dazan muzanta masa ya rabu dani har abada shine Umma Zakiya ta bani wannan shawarar da kanta taje ta nemo mani maganin dana sa masa a lemu"

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shine abinda Inna ta faɗi.

"tabbas na yarda da maganar hausawa da suka ce alhaki ƙwiƙwiyo ne ,Hidaya bazamu taɓa ganin daidai da jin daɗi ba har sai mun nemi yafiyar marayun Allah"

Kallonta Inna tayi ,"kinga illar sharri ko shi dayake tare da Allah sai ya kiyayeshi daga aikata aikin ɓarna saboda kyawun da zuciyarsa keda ita,  ke kuma da kikasa kwaɗayi aranki kika shuka sharri kinga ai abinda kika girba bai tabbata akansa ba ya tabbata akanki yanzu ki faɗa mani wazai wanke maki wannan baƙin abin da Mansur ya goga maki ,Hidaya mai yasa baki shawara dani ba alokacin da Zakiya ta baki wannan gurɗaɗɗiyar shawarar ,duk cin mutuncin danake masu bazan iya sawa ki masa wannan sharrin ba duk anawa tinanin gaskiya ne"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now