🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Miss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*74*
Tinda ta shiga ɗakin tasa ma ƙofan key bugun duniya taƙi buɗewa haka Alhj suka gama zaman daza suyi suka wuce kan cewan duk yanda sukai da ita a sanar masa.
Koda Baffa yasa ta gaba ya tambayeta cetai ita wlh data auri fasiƙi ƙwamma yay sadaƙa da ita.dariya Baffa yayi yace to idan bata sonsa ta yarda ta fito masa da wanda zata aura nan da wata guda.
Da wuya suka sha kan Hidaya ta amince da auran Mansur badan tana sonsa ba sai dan biyayyar iyayenta.
Ba tare da ɓata lokaci ba Alhj yace to idan har ba matsala zasu tsaida rana nan da wata biyu kacal,gyaran murya Baffa yayi yace mai zai hana aɗan ƙara masa duba da hidindimu da za'ai.
Ba matsala Alhj yace karya damu zai ɗauki nauyin komi nata,duk da yanda Baffa yayi na cewan bai aminta ba sai da Alhj ya roƙesa kan cewar shima uba ne wurinta karya damu da hakan.
Hakan ko akai nan da nan Alhj yasa a masa oder ɗin kayan ɗaki da kitchen daga italy, haka shima Baffa ya bai fasa saya mata wasu abubuwan ba duk kuwa da Alhj ya gama mata komi.
ɓangaren Mansur ma tini ya miƙe tsaye ya fara haɗa kayan lefe dan Alhj ce yay kuɗinsa ne zai aiki bazai masa ba,duk sanda zaije sayan abu Shama'u ƙanwarsa yake sawa gaba suje su sayo komi dan duk cikin ƙannensa tafisu wa yewa.
Yayi akwatunansa sha biyu maƙil da kaya na kece raini ya kashe kuɗi aciki ba kaɗan ba kuwa, haka Hajia ma ta ƙara masa guda uku suka zama shabiyar aka ɗauka aka kaima Hidaya.
Hajia da Inna ma nata hidima kan ɗiyar tasu wajen gyarata dan dama tin farko ita Hajia nason Hidaya to tsautsayin daya faru shi ya dagule komi to ayanzu kuma sai wannan soyayyar ta dawo abu kaɗan tayi waya tace da ita mai take so ya take so ai biki Hidaya ko batace wa komi sai dai tai shiru..daga ƙauye ma haka suma ba'a barsu ba kowa da gudun mawarsa ta gyaran ɗiya ƴan uwan Inna duk sun miƙe tsaye suma anata shirye2.
Itako tamkar ba wadda za aima aure ba idan ba sani kai ba bazaka gane ba tinda dai ba murna take da hakan ba.
Akaro na uku da Baffa ya ƙara jaddada mata amincewarta shine farincikinsa domin hakanne rufin asirinsu daga su har ita bata ƙi amayar masa da abinda ke cikinta ba na zata auresa ne dan umarni bawai dan tana sonsa ba ko zata sosa anan gaba.
Baffa yace ahakan ma yaji ya gode.
****
Ɓangaren Sadia mai jego tini tayi arba'in suka koma nan pataskum.
Sabuwar soyayya da ƙauna ta sake shiga tsakaninsu da Ammar wanda keji da ita da Affan,iskar da batai masa ba baya bari ta raɓesu.
Kamin Sadia ta goya Affan sau biyu Ammar ya goyasa sau biyar dan kusan shi yake jegon.
Inna da kanta ta shirya taje ta sanar masu da bikin Hidaya sunyi murna matuƙa suma tare da adu'an fatan Allah ya nuna masu lokacin Adda nata murna.
Sadia ita ta dinƙa lallashin Hidaya da bata haƙuri ta fawallawa Allah to roƙesa yasa hakan shine mafi alkhairi, da wannan bakin da suke bata ita da Maryam ta samu ta sakko ta fara sakin jiki ta daina takurewa a ɗaki amma fa badan tana farinciki da faruwar al'amarin bikin ba.
DU LIEST GERADE
HIDAYAH NOOR completed.
Historische RomaneHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.