🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*_ƳAN GRUP INA XUMUNT@ NOVELL@ 1&2 KUNA KASHENI BANA DYING DA COMMENTS ƊINKU😍,WANI JINA NAKE A SAMA YASIN DUK SABODA KU😎,KAI DOLE MA NA KWASOTA💃🏽💃🏽._*
*_INA FATAN ALLAH ƘARA HAƊE KAWUNANMU ZUMUNCINMU YA ZAMA MAI ƊOREWA,ALLAH YA HAƊAMU A ALJANNA_*👏🏼
*8*
Dawowa cikin shago Ammar yayi bayan ganin tafiyar Hidaya harta ƙule.
Kwanon abincin ya buɗe yana kai amma Adda ta kyauta da tayi faten wake.
Zama yay tare da yiwa ƴan shagon Bismilla.
Su uku ne dama waɗanda suke tare,Usman,Bello sai Yellow dan haka dukansu suka sauko suna shima Adda albarka data taimake su ta kawo masu abinci dama yunwa sukeji.Dariya Ammar yay yace aiko ba maici sai kun biya.
Suma Dariya sukayi suna ahaba aboki ai kamata ma yay ace kai zaka dinga sai mana abinci dan ka fimu samu a shagonn kullum fa cikin kawo maka ɗinki ake.
Dariya shima ya kuma yace ai banda ma ahali na yasin ni wannan ɗinki bayi zanba duk asa maka basir,kalla fa tunda akace azimi ya gabato wannan ya kawo wannan ya kawo ni harma nagaji da ansa.
Yellow ne yay dariya "lalle to ai ka gode Allah wlh,dan billahilllazi nasan bayan salla sai ka tashi da kusan dubu hamsin na iya kuɗin ɗinki kawai,kai Ammar fa abinka shar da kai"
"haka ne wlh kudai Allah ƙara rufa mana asiri"
Da amin suka amsa dukansu.
Suna cikin ci customer ɗin Ammar tai sallama.
Amsa mata sukai inda Ammar ya yunƙura zai miƙe tace dashi Aa ka kammala kawai inan.Wuri ta nema ta zauna a ƙofar shagon tana danna wayarta.
Sauri2 Ammar yayi ya gama ya tashi ya fita.
Wanke hannunsa yayi da kuskure baki sannan ya juyo gareta tare da ƙara mata sannu da zuwa.
Yauwa tace masa ɗauke da murmushi a fuskarta.
"kana jin daɗinka fa Ammar"Murmushi yayi wanda ya fitar da dimple ɗinsa da yawancin mutane keso.
"wanna irin jin daɗi hajjaju wannan ai saiku ,mu da kuke haɗamu da kaya ina batun hutu tare damu"
"Hmm gashi kuwa da yamma ma abinci kake ci banda wanda kaci da rana "
"O wai abinci,aini sai yanzu nake cin ma na rana na "
"bawani haka kawai saika ƙi cin abinci ka bari sai yamma irin wannan lokacin "
"to ai kinga daga gida aka kawon kinga saina jira "Zamanta ta gyara ta shiga karkaɗa ƙafa.
"to gaskiya ya kamata a gyara ana kawo maka abincinka da wuri,in ba haka ba ta ina zakaji daɗin yin aikin "
Murmusawa ya ƙarayi,
"Allah ko"
"Allah,ko ni ina dafawa sai ina kawo maka?"
"hhh waneni.yanzu dai ya akai wasu kayan aka kuma kawowa "Girgiza masa kai tayi alamu na Aa."to sai zan kawo ɗinki zanzo shagonan"
"O to kice kin biyo sawun kayanki kenan,aiko dai ko guda ban yanka ba inaga wannan karan ai bake a kayan salla"
ESTÁS LEYENDO
HIDAYAH NOOR completed.
Ficción históricaHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.