Page 41

1K 88 7
                                    


🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀




          *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺




         *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*




بسم الله الرحمن الرحيم...


*🤣🤣🤣🤣 Kai Kai😂😂 woooo🤣🤣🤣 agaskiya XUMUNT@ NOVELL@ kuna nishaɗantar kuna ƙayatar dani irin sose ɗinn, irin wannan kaftawa haka da ruwan comment🤣🤣,O🤔 abu kaman gaskiya Allah sharhinku na sani dariya ba kaɗanba harda ƙullewar ciki😂😂 ,aci gaba da kaftawa dai kunayi ina jin daɗi💃🏼 kuna bari gwiwana na sagewa😔, Dan haka the whole page of today nakune kuyi yanda kuke so dashi ku bada ko ku hana ,am olwayz apprciating the way u show ur love,care and support to me wlh, sose nake ƙaunarku cikin raina kun zama tamkar ƴan'uwa agareni i love u lodi lodi over trillions😍😍*

_Haba Nucycool or hot ne ma🤭😂😜, calm down ki ƙyalesu ni ina bayanki ina gabanki soon muma zamuyi masu ƴar dariya kaɗan amma fa bada yawa ba_.

*_Abinda Allah Yace Game da Marayu a cikin Suratun Nisa'i Shine:_*
*﴿ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﺄْﻛُﻠُﻮﻥَ ﺃَﻣْﻮَﺍﻝَ ﺍﻟْﻴَﺘَﺎﻣَﻰ ﻇُﻠْﻤًﺎ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺄْﻛُﻠُﻮﻥَ ﻓِﻲ ﺑُﻄُﻮﻧِﻬِﻢْ ﻧَﺎﺭًﺍ ﻭَﺳَﻴَﺼْﻠَﻮْﻥَ ﺳَﻌِﻴﺮًﺍ﴾*
_*“Lallai Wadanda Sukecin Dukiyoyin Marayu da Zalunci, Kawai Suna Ciwa Cikinsu Wuta ne, Kuma da Sannu Za'a Sanyasu Cikin Wutar Sa'ira”*_

*_Wannan Itace Ayar data tsoratar Game da Cin Dukiyar Maraya da Zalunci._*


*41*

Sun jima suna romance ɗin juna yanda ya kamata kamin ya kalleta da ƴar dariya ya kashe mata ido guda.

"yadai"

Jiki a mace tai murmushi tare da juyar da fuska gefe tana sauke numfashi.

Kwantar da fuskarsa yay bisa ga tata yace, "yadai my Angel ko mu lula babban birini ne umm"

Bata basa amsa ba sai sauke numfashi datake.

Hannu yasa ya juyo da fuskarta ya sake bata kiss a wuya.

"baki bani amsa ba"

Lumshe ido kawai take tana buɗewa bata ce masa komi ba.

Ɗagowa yay daga kanta ya ɗaga riga zai cire ta miƙa hannu ta riƙeshi.

Kallonta yay ya ɗaga mata kai.

Narke fuska tayi ,"fita fa zamuyi"

"to basai a haƙura ba sai next time ,nidai kawai ki bari mu ƙarasa jin daɗinmu kinji.."
Ya ƙarasa faɗi shima da ƴar shagwaɓa.

Ganin da gaske yake zancen nasa ta saurin zamewa ta sauka daga kan gadon.

Zai haura ya kamota ta shige bathroom da gudu tana masa dariya.

Da dariyar shima ya bita tai sauri ta saka ma ƙofan key.

Nan kan gadon ya dawo ya kwanta inda yake fuskantar sama fuskarsa sai fidda murmushi take kai daka gansa kasan yana cikin walwala da jin daɗi.

Batafi 10mnt ba a wanka ta fito ɗaure da karamin towel nata,

Tsayawa tai tana kallonsa yanda ya tallabi fuskarsa ya kafeta da ido kaman yau ya fara ganinta.

Taɓe baki yay yana ɗaga gira ya kuma saita zaman kallon nasa,kallon jikinta tai ta dawo ga mirrow ma ta gama kallekallenta bata ga wani abuba ta dawo gabansa ta tsaya da ɗan dukan ƙasa tace,

HIDAYAH NOOR completed.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora