Page 29

1.2K 82 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
           *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


          *Story~Writen~Edited*
            *_By Mss Xerks_*🌺



     *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...


*29*

"Inna ki faɗi mana wacece?"

"Hidaya yayar Baffanki ce"

"Baffa na"? Ta tambaya da mamaki.

"ƙwarai kuwa itace babbar yayarsa ita muke cewa Yafindo"

Murna haɗe da kuka Hidaya tai wurin Yafindo.

Ƙam ta rungumeta tana ,
"Yafindo mai yasa kuka gujemu bakwa nemanmu munzama tamkar bamu da wasu ƴan'uwa"?

"to yi shiru ki daina kuka ni bana son tada zancen baya,yanzu tinda nazo gareku ba hikenan ba"

Da murmushi ɗauke fuskar Inna tace,
"ƙwarai kuwa sai godia ga Allah ,naji daɗi sosai na gode Allah da wani namu har ya iya tinawa damu yau ya dawo garemu"

Ƴar dariya Yafindo Mariya tayi,
"kuna raina kullum ina tinaninku ,wanne hali kuke ciki? aya kuke ?kuna ina kullum sainai wanga zance"?

"Allah sarki gamu ko muna lapia yakika baro can ƴan'uwa"?

"kowa lahia yake ,bayanda ban dasu suzo mu tahi tare ba sunkace a'a su basu zuwa gidan mara zumunci kuma talaka"

Murmushin gefen leɓe kawai Inna tai tace,"Allah kyauta" aranta.

"yanzu hala Zaliha wanga yarinya ce ta girma haka"

"ummm Yafindo gatann kam ta girma rabonki da ita tin tana zane"

"ikon Allah shekaru dayawa kenan kusan 17-18 ,to ina shi Yusufa ɗin"?

shiru Inna tai kanta ƙasa wani hawayen ya sakko mata.

"ummm ina magana ko sun fita shi da Baffan nasa nene tin zuwana ban gane su ba ga magriba har yanzu ko sai dare suke dawowa?"

Ɗagowa Inna tai ta sake duban Yafindo.
"ai yau shekararmu tara bama tare dasu"

Da zaro ido haɗe da mamaki da alamu na tambaya Yafindo Mariya ta dubi Inna.

"kina so kice mani sun rasu ne ko ƙaƙa ne"?

Girgiza mata kai Inna tai cikin takaici tace," Sulaiman ya gudu ya barni saboda talaucin da muke ciki daga baya shima Yusuf yabi sahunsa har iyau Allah bai nufa dasun dawo ba"

Riƙe haɓa Yafindo tai tana girgiza kai ranta a ɓace.

"Oo yanzu abinda ya aikata maku kenan ko,halinsa na rashin mutunci yanan kenn, To ku kwantar da hankalinku idan magana ya nemi yaja maku ya ɓata maku suna gani na dawo gareku kunji,kuma komin dare daɗewa idan yana raye ya dawo zai gane kuransa"

Murmusawa kawai Inna tayi bata ce komi ba illa aranta datace , _bana ko ƙaunar sake ido huɗu da Sulaiman a rayuwata ,Allah kasa ma ya mutu._

"kuma duk tsawon shekarunn baki sake wani auren ba?"

"ummm inan tare da yara na"

"Allah sarki..yanzu ai gani na dawo, da da mijina ma zamu taho to bai iya takawa hiyasa"

Dagann suka ci gaba da hirar yaushe gamo har akai kiran magriba suka tashi sukayi sallah.

Bayan sun idar sunci abincin dare aka kuma dasa wata hirar,su Inna sunsha labarin can ƴan Taraba kalakala tin bayan rabuwarsu tare da sallahun da babanta ya bada na cewan ko ya mutu karta kuskura ta doso inda yake.

HIDAYAH NOOR completed.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora