: 🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*Jinjina da ban girma gareku*
Maman Hajiya
Maman Sayyed &Noor
Maman khady&khaleepa
Khadija Habib
Sadiya Muhammad
Maman Mayeesha*12*
Da safe da wuri Hidaya ta tashi tayi gyaran gida ta kuma yi wanka abinta ta shirya.
Inna na kwance lokacin bata tashi ba Hidaya ta tasheta.
"Inna zanje wurin Adda"
"Da wannan safiyar ki bari dai zuwa anjima.ita yanzu in kinje bata tashi ba""To ai Inna wayar Hamma zan kai masa jiya cikin dare akai ta kira"
"O na manta ɗauki maza jeki kaimasa ki gaishesu,ki kuma cemata idan da ragowan tsakin masarar nan yau ko dambu za'a mana"
"tom sai na dawo"
"uhmm ki kula,Allah ya kiyaye"Da sallamarta ta shiga gidan,Adda ce kawai ta tashi Ammar har lokacin bai tashi ba.
Gaida ita tai ta isar mata da saƙon Inna tace to insha'allahu zako ayi.
"kinga shiga ɗaki ki kwason wasu ƙullin kaya ki kawon nan"
To tace ta shiga ta ɗebosu gari guda har tana nishi.
"yanzu Adda duk wannan wankin zakiyi,kawai kema kina haƙura da wankin azumi wahala ne"Murmushi Adda tai tace kedai zube duk abinda kika ga anyi kamawa tai,bakida takalmin salla babu kuma mayafi.
Ehh ko Hidaya tace da ita,itama hijabin nata ta cire tace bari ta tayata.
"A'a ina ke ina wannan wankin,jeki zamanki yanzu zan gama abuna"
"dan Allah Adda waini ina son ina yin wanki sai kice bazanyi ba""zakiyi bari ba yanzu ba tukunna"
Da ƙunƙuni tai ɗaki Adda tace "to zo kiyi amma wlh ko kince kin gaji sai kin ƙarasa"
Dariya tayi"ehh naji"
Sunayi suna ta hira Ammar ya fito daga baccin daya tashi.
Miƙa yay ya ja bokiti ya zauna akai."Adda kin manta nima zanyi wanki baki tasheni ba"
"ina sane ƙyaleka nayi ka huta in ka tashi kayi"
"ai in rana ta fito bazan iya ba kinsan azuminn fa akwai wuya""to Hamma kawo muyi maka mana"
"kajita sai kace iyawa zatai,wannan ma da kike nasan na marmari ne ajima kaɗan zaki fara kin gaji"Dariya Hidaya tai "Allah Hamma da gaske ka ɗauko,ai mun kusa gama wann ɗin kuma wanki ma fa ba wuya"
Adda ce tace "ke bazamuyi ba dan ma ya samu ana cewa ya kawo to yay kayansa bai gajin bane"
Da dariya ya tashi ya shiga ɗaki ya kwaso yuyan kayansa ya fito dasu.
"umm nima dama nafiso na wanke abina sanfi fita,amma na rasa wa zan bawa sai wann ƴar duk ta mani jagwalgwalo"Adda ta kalla"wai kinji nice nake jagwalgwalo"
"Hmm ai ba ita zaki tambaya ba masu kayan zaki tambya in ankai masu.kinsan idanba Adda rabon adawo maki da wankin kine ace basu fita ba ki sake"
Ya faɗa yana dariya.

YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.