🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Writen~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''2U My Sanaz Deeyah ,luv u sis irin wujuga wujuga akoda yaushe yinki nake walla over ma...'''
*30*
To cikin kaɗan ɗin lokaci Inna ta sauya daga Innarta zuwa Inna mara M.
So,jinƙai,tausayi duk data kema su Adda yanzu ta zubar aƙasa yanzu tsantsar ƙiyayyarsu ke yawo a zuciyarta wanda ƙaunar ganinsu ma bata sonyi.
Gori da hantara sune kawai ke haɗa ta dasu,dan maganama cikakka bata dasu haka zalika ma Yafindo.
Gaisuwar ko Ammar ba sose take amsa masa ba dan watarn dan kanshi zai gaji ya miƙe ya fita shago yana kukan zuci akan fushin da Inna ke dashi wanda ya rasa dalili.
Kasancewar yanzu abinci mai rai da lapia suke ci in ba nama d kifi in ba kifi da nama toko duk sanda ta zuba masu sai ta kora masu baƙar magana akan Ammar ya kasa nemowa ita kuma baƙin jini ya hanata aure.
Babu ranar Allah da zata waye ta faɗi Adda bata zubda hawaye ba dan abin sosai yake damunta akan sauyin da Inna ta masu,waya shiga tsakaninsu laifin mai suka mata sun kasa ganowa dan haƙurin duniya sun bata amma ƙarshe macuta azzalumai ƴan baƙinciki take kiransu.
Ammaa ,Kawu, Yahya da Matarsa babu wanda baije ya sameta akan tayi haƙuri tayi afuwa akan laifin da Ammar yay mata amma duk ciki babu wanda taima kallon arziƙi bare ta saurare shi.
Randa Ammar ko ya zauna mata ɗaki yana kuka haiƙan kan ta yafeshi in ba haka ba rayuwarsa zata tozarta zai shiga wani hali idan har bata bar yafe masa ba.
Buɗar bakin cetai dashi ai dama ita bata da wata alaƙa dashi da har in tayi fushi dashi zai iya ganin ba dai2 ba ,kuma ita maganar gaskiya yanzu tama fara gajiya dasu su daure suje su nemi ƴan'uwansu su koma can tinda ance su masu fararan ƙafa ne duk inda suka shiga to babu arziƙi sai ƙahon talauci kuma har asiri ma sukanwa mutum idan yana da wadata.
Abdullahi mijin da Adda zata aura yanzu ya kawo kaya dan har an tsaida biki sati uku saboda Inna tace baza'a haɗa dana ɗiyarta ba haka kawai aja mata ɗangwaran gwan farar ƙafarsu da asirinsu yaja ace dole da Ammar za'ai.
****
Ammar na zaune daga shagonsa yana sauraron wani tafisir ya hangi Hidaya wurin mai nama tana saya.
Da sauri ya rakiɓi sandarsa ya shiga dungurata har ya ƙarasa gareta,
Bata san da zuwansa ba sai dataji yace "gimbiyata" sannan ta juyo ta dubesa.Murmsuhi ta fitar mai sauti tana kallonsa ,"gimbiyar mai rabo dai ko"
"bafa nason irin wannan wasan da kike mani ki daina zuciyata zata iya bugawa"
"sai muci gumba ai dama mun jina bamu ci ba"
"au yanzu kin gaji dani kenan har so kike na mutu"
"to ya za'ayi kullu nafsin ai za'iƙatul maut in lokacinka yayi dole ai ka tafi da sonka da rashin sonka"
Ɗan murmusawa Ammar yay ya maida idonsa ƙasa da tinani na sauyawar al'amari acikin ransa.
Dubansa kawai take tana taɓe baki , _gaskiya Allah ya taimakeni wai dana auri Hamma nace na auri me,na godema Innata data gano mana hanyar dai2 ,ƙwamma kaje kaci arziƙi ka barsa inda yake dan talauci baiba_.
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.