Page 26

1.1K 79 1
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                         🌀🌀🌀🌀🌀



        *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺





       *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*MRS OMAR NOVEL kuma ga naku page ɗin na sadaukar maku..naga comments ɗinku na kuma ji daɗi sose ina godia*.

'''Ban manta daku ba.'''

Nusaiba Y Giɗaɗo.
PRINCESS.
Jauharatu Shehu.
Ummu Khadeejah.

*26*

"kuyi gaggawar tashi ku nemo abinda ake buƙata domin ceto lapiyarsa"

Da sauri Adda da Hidaya sunkayo kansa jin furucinsa nasa.

"me me me ake buƙata? dama bai mutu ba?"

Suka jefa masa tambayar atare cikin yanayi na ruɗu.

Bai basu amsa ba kawai yay gaba saboda zai shiga theater ne yana sauri.

Kawu ne yazo ya kama Hannun Hidaya tare da maida kallonsa ga Adda.

"bai mutu ba sai dai yana cikin mawuyacin hali ayanzu...bayanan da yamani ne suka girgizani yasa na kasa faɗi maku dana fito"

"Kawu to a wanna irin hali yake"?

"kasencewar ya jirkita da yawa hakan yasa ya sami doguwar suma sai dai kuma ya zubar da jini da yawa ba kuwa kaɗan ba wanda takai ga yanzu sai ansa masa jini har leda huɗu sannan ma zai samu ya farfaɗo...."

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...

Da gudugudu Adda tai ward ɗin da taga Dr Ahmad yayi ɗazu.

tana zuwa ko yana gab da shiga theater room.
Ƙwala masa kiran datayi ne yasa ya tsaya ya ɗan juyo yana dubanta har ta ƙaraso.

Hannunta kawai take miƙa masa da kuka take cewa,
"likita a ɗibi nawa jinin a saka masa,zaiyi masa dai2"

"nima likita dan Allah a ɗibi nawa duka asa masa ban son rasa Hamma na"

Dubansu yay duk su biyun na ɗan lokaci sannan yace dasu"babu wannan damar kuma buƙatarsa kuke....na faɗawa mahaifin naku idan babu namijin dazai bada to aje a sayo yanzu akawo idan har kuna son rayuwarsa"

Yana gama faɗi ya shiga theater room ɗin.

Sunata kiransa bai juyo ya kallesu ba,ganin hakan yasa su kwasa da gudu har suka kaiga wurin dasu Kawu suke tsaye.

"Kawu aina zamu samo jinin to?"

"Yanzu Yahya ya dawo daga lab ɗin sunce duk leda guda dubu ashirin ne...".

"Innalilahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifi khairan minha...Kawu aina zamu sami dubu sittin yanzu,na shiga uku ni halima Allah ka ceto mani lafiyan Inna da Ammar"

"Patient ɗinku fa na can unconcious yana biɗar jini cikin gaggawa.idan har ba son rasa rayuwarsa kuke ba to kuyi maza ku kawo wanda za'a ƙara masa yanzu"

Nurse Rashida ta faɗa magana a sanyaye.

Zuciyar Hidaya ce ta buga dai2 lokacin da Nurse ɗin tagama masu bayani,Kaman ana jefar ƙafarta haka ta kwasa da gudu ta fita gate ɗin asibitin.

Su Malm Shuai'bu nata ƙwala mata kira amma ko waigensu batai ba.

Kawu ne yace da Yahya maza bita.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now