🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀
*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*47*
"ambaton Mafiya da yayi najini a tsora ce to ban nuna masa hakan ba sai ya tambayeni na amince nace masa ehh zan iya idan har zan samu abinda zan dinga ci da iyali na suyi fahari dani in kuma kai ɗiyata makaranta.",
"Dariya yayi yace baka da matsala indai fagen wannan ne har wanda zaka taimaki wasu marasa shi ma zaka samu amma idan harka yadda zakayi duk abinda mukace kuma ayanzu haka kamin ka fara mana aiki zan baka million guda,
Jin haka ba musu nace zanyi koma mine." ,"wani tsumma ya ɗauko ya bani yace gashi abokinsa ke neman takara babu kuma kuɗi aƙasa dan haka suna neman mutanen dazasu tsubbace suyi kuɗi, ya miƙo mani na amsa yace cikin kwanaki uku muna so ka kawo mana ƙananun yara guda 50 zaka ga yanda zamu maida su kuɗi ba tare da munje mun buga ba,abin ya girgiza ni sose kai tsaye nace masa a'a bazan iya ba ko ɓera bazan iya kamowa na kawo a maidashi wani abuba bare ɗan adam",
"dariya yayi wadda harta sa na tsorata da hakan,nan mukai ta fafatawa nace ni gaskiya bazan aikata hakan ba bazan jefa kaina ga hatsari ba,bazan iya ɗaukan ɗan wani ba domin nima ina da ƴaƴa wanda idan aka ɗaukensu ban san yanda zanji ba, har dare muna haka dashi ƙarshe sai yace to zamuje can wurin ogansu sai a sauya mani wani abun tinda idan har mutum ya rigada ya amsa ya amince da shigar mafiya toko bai fara ba yanan sunan a ƙungiya." ,
"Haka mukaje wurin ogansu suka tambaya dodonsu na tsafi nan suka ce wai nakai jinin wani nawa,na matata ko ɗana ko kuma wani ɗan uwana anan naga abinma hauka ne na ɓata rai nace bazan ba bazan iya kisa ba su sakeni kawai tinda dai ba'a dole yanzu idan sune aka ɗebewa iyali ya zasuji, suka ce ai na riga na shigo nace masu sam bazai yiwu ba kuma su sani tabbas sai asirinsu ya tonu jin abinda na faɗa kamar ƙiftawar ido naji na daina magana kwatakwata sai dai na buɗa bakina amma ba magana nan suka ƙullemu nida wani mutum da igiya aka mana aski akace gobe za'a yanka mu,na shiga firgici da razani babba bandamu da halin dazan shiga ba iyalina kawai nakeji suna a awanna hali yanzu na rashina duk da dama ba wani jin daɗi suke dani ɗin ba",
"washe gari munaji muna gani haka aka samu a inji iko na rabbi wlh juyin duniya wuyanmu da duk wani sassa na jikinmu yaƙi yankuwa, kullum haka cikin kuka nake da adu'oi babu abinci sai ƙazamin ruwa da suke bamu kuma kullum ahaka ake samu ga inji idan yaƙi asa wuƙa in yaƙi muci duka da manyan gora, haka ina kallo aka maida wanda muke tare akuyar aman kuɗi amma ni Allah bai basu ikon aiwatar da abinda sukai niyya ba ,ahaka wasa wasa yau suce gobe suce sai da muka ɓata shekara goma acikin wannan gida." ,
"watarana da ikon Allah muka sulale mu da yawa muka gudu, isarmu tsakiyar daji duka idanunmu suka rufe bama gani, haka muka kwana wurin sai a washegari wani yazo ya ganmu aka ɗaukemu aka kaimu gidan mai garin yola,mun shekara biyu anan anata adu'oi da magunguna har Allah ya kawo waraka daga nan aka sallamemu da kuɗin motarmu."
"da tambaya na ƙarasa anguwarmu ban manta layin ba har kuma gidan sai dai ina zuwa na tadda an maida gidan babban shago nayi tambaya akace kun jima da tashi yanzu haka ba'asan inda kuke ba, na shiga tsantsar tashin hankali dan ban san inda zqku dosa ba har ƙauyenmu naje akace baku zo ba sunyisunyi na zauna nace a'a sai na nemeku duk inda kuke tukunna zan sami nutsuwa, haka nakomo nayi yawon nayi yawon har nagaji na dawo nan ƙofar shagon da zama ko Allah zaisa ku dawo,to watarana na fito nan kan titi ina tafiya duk a wahale sai ga haɗaɗɗiyar mota tazo wucewa nan tai parking gabana." ,
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.