🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*68*
Cikin cijewa tana juyi da kai taja bedsheet ɗin gadon nan akai sa'a Ammar ya farka.
Jin bata ajikinsa ya miƙa hannu ya janyota yaji wayam,
Nishin daya jiyo yasa sa saurin buɗe ido a tsorace.Light ya kunna inda ya hangeta can ta wurtsula tana gwaragware tana faɗin wayyo.
Aruɗe yay kanta ya kamota da talbo fuskarta,
Cikin tashin hanƙali ya shiga tambayarta."Hayatee,Hayatee lafiya?Baby nah buɗa idonki, mi ya faru? mike maki ciwo? Tin yaushe kika tashi ban sani ba,wanna irin bacci nai"
Bazata iya buɗa baki ta masa magana ba sai hannu datasa ta tallabi fuskarsa tana kallonsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,ko haihuwan ne"?
Yay maganar kaman zai kuka dan yana da rauni akanta.
hannunsa ta ɗora ƙasan mariyarta tana kuka.
Shima da hawaye tap idonsa yake faɗin, "sannu mai sunan Mamana,Sannu,sannu kinji"
Duk ya ruɗe ya rasa ya zaiyi mai ya kamata yayi.
duk da cikin ciwon da take hakan bai hana ta fuskanci yanayin daya shiga ba na ruɗu.
dafe yake da cikin nata sai sannu yake jera mata.
hannusa ta kama wanda tai nuni da ƙofa da faɗin, "Inna"
"Inna zan kira"?
Ɗaga masa kai tai ta maida murfin idonta ta rufe tana hawayen azaba dan ita ɗaya tasan mi takeji.
Pillow ya ɗauko ya jinginata a jiki yay ƙofa zai fita ya kuma dawo,haka yay tayi sai ya doshi ƙofa sai ya dawo du ya hargitse gaba ɗaya ma ya manta da wata aba waya bare yay tinanin kiran wani.
Da hannu take masa nunin kawai yaje yace, "a'a bazan iya barinki haka in fita ba"
Tinanin ta yanda zaije kiran Inna Hassana yake dan bazai iya fita ya barta ita ɗaya ba a wannan halin ba, cicciɓarta yay ko zai iya ɗaukanta yaji bazai iya ba dan ta ƙara nauyi.sai da ƙarar alarm ya buga tukunna yay tinanin kiran Inna Hassana.
Yana riƙe da ita ya danna kiran Inna sai daya kira sau uku tukunna ta ɗaga dan sallah take time ɗin.
Da ɗagawarta tai sallama ya amsata a ruɗe nan ta shiga tambayarsa ko lafiya yace babu lafiya Sadia, kamin ya ƙarasa ta katse wayan da cewan gani nan.
Ko minti biyar bata ƙara ba yaji turowar ƙofarta,itama ba ƙaramin girgiza tai ba da yanda taga Sadia.
Kamota tai zuwa jikinta tana ta mata sannu,tambayarsa take tin yaushe ta fara "ce yake tin ɗazunne Inna" muryarsa a rauni.
"Inna mu tafi asibiti"
"a'a naga alamun haihuwar ce baya yiwu mu shiga mota ba mu ɗan jinkirta tukunna Ammar",
"yanzu buɗa mani waccen drower ɗin ka ɗaukan wata baƙar leda dama kaman nasan da hakan na ajesu nan"
Ɗaukowa yay ya miƙo mata,reza da zare ne aciki nan ta ɗauko ta aje gefen drowern kusa da ita.
VOUS LISEZ
HIDAYAH NOOR completed.
Fiction HistoriqueHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.