PAGE 18

1.6K 106 2
                                        


🌀🌀🌀🌀🌀
           *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



            *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺



           *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



'''AlHAMDULILLAH2 IDONA YAY SAUƘI NA GODEMA ALLAH SANNAN NA KUMA GODE MAKU MASOYANA BISA ADU'ARKU GARENI,BABU ABINDA ZANCE DAKU SAI ALLAH YASAKA MAKU DA ƊINBIN ALKHAIRINSA YA KUMA ƘARA MANA LAPIA BAKI ƊAYA'''.😊

'''WANDA SUKA KIRANI WAYA DA WANDA SUKAI TEXT BASUGA REPLY BA KUYI HAƘURI DAN ALLAH BANA SAMUN DAMAN KALLON WAYANE WLH DAN ƘARSHEMA SWTCHOFF ƊINTA NAI BAKI ƊAYA AMMA IYA YAWAN SAƘWANNI NA GANSU NA KUMA JI DAƊI NA GODE DA NUNA KULAWA'''.

*18*

*BAYAN WASU LOKUTA*

Cikin ƘanƘanen lokaci soyayya mai ƙarfi ta sake shiga tsakanin Hidaya da Ammar.

Son junansu suke na amatu inda suke gudanar da soyayyarsu cikin tsafta.

Adda kawai tasan da soyayyarsu banda Inna da kullum cikin zancen Ammar ya nemi matar aure take.


Alhmdl sana'ar ɗinkin Ammar masha'allahu yana samu da ita sosai,dan yanzuma Rabilu wani shagon ya buɗe na daban inda ya samasa kekuna ya koma can yake ɗinkinsa na mata daban.


Waec ɗin Hidaya ta fito ta kuma yi kyau inda ta fito da gud 9crdt da ake buƙata.har party Adda ta haɗa mata shima kuma sahibin nata yay mata kyauta mai kyau wanda bazata taɓa mancewa da ita ba indai ta kalleta wato sabuwar wayar hannu touchscreen ƴar ƙarama dai2 riƙon talaka.

Duk sallar Asuba Ammar ke tashinta da ranagaɗa mata calling saboda nauyin barcinta duk yanda Inna take da ita bata tashi sai dai taita faman juyi har saitaji ana gari ya waye zata miƙe.

    ******

sallamar da Ammar yayi ne yasa Hidaya ɗagowa daga wankewanken datake.

Binsa da ido tai saboda shigar dayay taimasa kyau sose.

murmushi suka sakarma juna idonta jikinsa dan bata bari su haɗa ido,ɗagowan datai domin kallon fuskarsa ya kashe mata ido tai saurin sauke idonta ƙasa.

Da ƴar dariyarsa yace da ita "ƴammata irin wannan kallo haka kaman baki taɓa ganina ba"

Murmushi Mai fitar da sauti tai kanta sunkuye tana ɗauraye kwano magana ƙasa tace"gani nayi ka ƙara yin kyau"

"Hmm ina wani kyau anan ,kedai zolaya ko?"

"Hmm Allah da gaske,idan kai aski sai naga kaman an ƙara halittarka da tsantsar kyawu na daban"

Da ƴar dariya ya sunkuya yana"Allah ? kaman yanda kema kullum ƙara kyau kike nayi2 ki faɗan sirrin kinƙi"

Hmm tace batare da tankasa ba.

Hannayenta ya kalla da suke ƙara masa kyau aduk sanda ta zanesu da lalle,"kawo na tayaki "

"umum barshi na gode karka bata kayanka"

"Hmm to ke kuma ƙunshinfa bakya gudun ya goge"

"saina kuma yin wani ai"

Sajensa ya shafa yana smilng inda dimple ɗinsa ya lotsa,"shi yasa kike burgeni duk hanyar adana mani kanki kinsani"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now