Page 67.

1.1K 78 6
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀




        *Story~Written~Edited*
            *_By Mss Xerks_*🌺





         *Devoted to Ummi Aisha*





*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



  *67*

Cikin sati uku da suka ƙara kaman ko wace rana Allah dake rayar da bayinsa haka danƙon so gami da ƙauna ke ƙara wanzu cikin zuƙatan Ammar da Sadia.

Duk wata kulawa da mata ke biɗa wajen mijinta Ammar na bawa Sadia hakan Inna da Adda riritata suke saboda cikin jikinta.

Hakana ɓangarenta yanda ake son sauke hakkin miji wajen faranta masa tana bin duk wata hanya dan ganin ta samar dashi ga Ammar.

Duk sanda ko ta ɗaga hannu cikin jin daɗi take godema Allah daya mallaka mata Ammar matsayin mijinta da kuma dangin miji masu ƙaunarta.

            ****

Hidaya ce zaune kan gado ta rafka tagumi gefenta Mukhatar kwance yana baccinsa.

Wayarta ta ɗauko inda ta danna numban Sabira nan taji ba kuɗi aciki.

Miƙewa tai ta nufa ɗakin Inna inda ta sameta zaune tana karanta suratul kahf kasancewar yau juma'a.

Gadon ta haye tana jiran idarwarta shiru shiru ta gaji dan idan Inna ta zauna lazimin friday kai kace sassaƙata wurin akai.

"Inna wai har yanzu baki idda ba kinfa gama karatun naga"

"ehemmm" Inna tace da ita nan Hidaya ta ƙyalƙyale da dariya.

"wlh Inna babu wani lazimin daza'ace ba'a magana,kimin magana kawai"

Hannu Inna ta juya mata da kuma faɗin, "ehemmm"

Nanfa Hidaya ta kuma sakin dariya harda kwanciya kan gado.

"kinsan Allah Inna da wannan ehem ɗinma guda biyu da tini kin bani amsata"

Girgiza kai Inna tai tana dubanta gami da ɗaga mata kai alama na mi take so.

Itako abin dariya yake bata nan taci dariyata sannan ta kuma cewa,

"kiwa manzon Allah Inna ki buɗa baki ki mani magana,ki daina biye ta wannan ƴan ɗarikar sallah ce kawai wadda aka haramta magana acikinta wanda da zarar kayi sallaharka ta warware"

Banza Inna tayi da ita ta maida hankalinta ga lazimin da take.

"wayyo Allah yanzu Inna kinan har bayan la'asar to nidai dan Allah kuɗi zaki bani in kina dashi"

kallonta Inna tayi ta juya mata hannu alama na mi zatai dasu.

"Inna abu zan sayo dan Allah"

Da hannu ta kuma juya mata nan fa Hidaya ta kuma sheƙewa da dariya.

"Allah Inna kamar bebiya in kina wannan abin,dama idon Mukhtar biyu yaci dariya"

Itama kanta Innar sai data dara amma sam taƙi magana.

"Inna kati zan sayo ko hamsin ce ki taimakeni ki bani"

ɗaga kai tai ta mata nuni da wadrob tace ta zira hannunta ƙasan kaya ta ɗauko.

itako tana dariya ta nufi wadrob ta buɗa ta zira hannunta taji babu,

"wai Inna nan ɓangaren"?

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now