🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
Just typing batre da editing so in kunci karo da erros kuyi haƙuri.....
*66*
Bayan sati ɗaya da daddare suna zaune ɗaki Ammar na danna laptop Sadia na ninke singlet nasa data wanke ta dubesa da tsoron maganar da zata masa.Ta ɗau lokaci tana kallonsa da tinanin irin amsar da zai bata kamin nan ta kira sunansa da, "Mahbub"
Barin abinda yake ya ɗago da murmushin so da yake mata a kullum ya amsa mata da ,
"na'am Maman twins, yanzu dan Allah nace ki aje wannan ninkin idan na gama zanzo nayi ki kwanta ki huta kema bana son kina yawan wahala da aiki amma kinƙi"
"uhmm naƙi wayon na bari ka ƙwacen aikin lada na"
"to ai shikenan amma ki sani indai na rigaki gamawa tare zamu ƙarasa"
"naji" ta faɗi tare da ɗago kumburarriyar ƙafarta ɗaya ta ɗora kan gadon.
"Mahbub dama magana nake so muyi"
"uhmmm ina jinki ranki ya daɗe"
Ɗan shiru tayi kamin tace, "akan maganar makarantar Hidaya, nace amma ba har ita kai fushin ba ko"
Tsuke fuska yay daga fara'ar da yake da maida dubansa ga laptop ya cigaba da dannawa batare daya tankata ba.
"Mahbub kayi shiru"
Fuska ɗaure batare daya ɗago ba yace da ita,
"ban katse taimakon da kikai niyya ba, na haɗa Dr Shehu da Babanta komi ne suyi ajunansu basai anne meni ba"
Sai yanzu taji daɗi dan nata tinanin har makarntr yasa a dustbin bayan an rigada an gama sama yarinyar rai, dan ita batama taɓa tinanin zai amince ba tin lokacin data masa zancen ya kamata a samama Hidaya makaranta sai kuma abin yazo adaiadai Baffa yaje masa da maganar.
Ninkin taci gaba dayi kamin tace, "ni wlh Mahbub ko dakayi shawara dani ma daba kayi abinda ka aikata ba, sam banji daɗi ba kamata yay ace tinda dai ka yafe mata to ka manta da komai basai kayi wani ramuwa ba duk abinda ya rigada ya wuce ai ya wuce".....
Da mugun kallo ya dakatar da maganarta gami da cewan,
"kinga dakata, bafa wai na faɗa maki bane dan kisani gaba kina mani wa'azi ko nasiha ba, na faɗa maki ne dan fita hakkinki wanda nake ganin na shiga abaya lokacin da kike biɗar kulawa ta na gaza baki ita yanda yaka mata,so kija baki kimin shiru"
Ɗan rausayar dakai tayi tace,
"amma Mahbub tinanin ɗaya ya kamata kayi,zafin so ciwonsa bala'i ne koba a faɗi maka ba ka sani, idan kai ka iya jurewa matsayinka namiji ita macece wadda keda rauni bazata iya jurewa ba ka tausayawa halin da zata shiga da halin da mahaifanta zasu kasance ,banso ka biye zuciyanka ba akan ramuwa wlh, ni dama ka tintiɓeni b4 k aikata hakan"
Da mugun kallon da yake mata yace, "naji, nabi zuciyata na aikata abinda taso banyi shawara dake ba, to yanzu na nemi izinin taki zuciyar ba shawara ba sai ta faɗi duk abinda take so in yaso saina koma na aikata dan jin daɗinki"
Ya ƙarasa maganar gami da wurga mata harara.
"nifa ba haka nike nufi ba, amma dai danasan da hakan bazan bari ta faru ba ƙwamma ace aurota kayi muka zauna tare dan wlh ina tausayin Sis....."
VOUS LISEZ
HIDAYAH NOOR completed.
Fiction HistoriqueHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.