Page 58.

980 86 4
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀


*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺


*Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*_NAYI MISTAKE ƊIN NUMBA LAST PAGE MAIMAKON 57 NASA 56AGAIN_*

*58*

Baice dasu komi ba ya fice daga ɗakin.

Sai da yay ɗan taku mai nisa tukunna ya tsaya yana shaƙar iskar dake kaɗawa mai sanyi.

Ji yay gaba ɗaya yanayinsa ya sauya,farinciki ya mamaye shi saɓanin ɗazu da yake jinsa wani gingiringin kaman wanda aka ɗorama dala da goron dutse akai.

Juyawa yay ya kalla sashin room ɗin Hidaya sannan ya juya ya cigaba da takawa a hanƙali wani sanyi na ratsashi.

Kansa ƙasa yake tafiyar bai ankare ba yay karo da mutum.

Bismilla suka faɗi tare inda ya ɗago yaga Sadia wadda ke a ruɗe.

"Babyy" ya faɗi yayinda yake kamata daga neman faɗuwar da take saboda jirin dake ɗibanta.

Fuskarta da tarin damuwa tabisa da kallo tana tattaɓa jikinsa.

Murya na rawa tace, "Baby what's wrong with u, mai ya faru ka faɗa mani"

Ganin yanda duk tabi ta ruɗe ya riƙe kafaɗarta yana lallashinta.

"calm down Baby,babu abinda ke damuna sai rashin lafiyanki"

"to bana ji sauƙi ba"
"hakan yasa kuma naji daɗi ba"

Ya faɗi yayin daya rungumeta.

Kasancewar goma tayi ba mutane dake giftawa ya sunkuci kayarsa suna dariyar masoya bayan dayay juyi da ita suka wuce zuwa room ɗin.

Bako kunyar Gwaggo dake tsaye wurin ya buɗa ƙofa ya shige da ita.

Akan gadon ya ajeta wanda zamansa kusa da ita kenan likita ya shigo da sallamarsa.

Amsa masa sallanar sukayi Ammar ya miƙe da tambayarsa ,"lafiya"

"lafiya lau ranka ya daɗe" ya faɗi yayin daya maida kallonsa ga Sadia yace, "madam ya jikin naki"

"naji sauƙi docter"
"to Allah ya ƙara lafiya, babu dai wata matsala ko"

Ɗaga masa kai tayi tace, "umm babu komi"
"masha'Allahu hakan muke so,Allah ya ƙara lafiya"

"har yanzu baku fitar da result ɗin bane"
Ammar ya tambaye shi.

"ehhh ranka ya daɗe shine ma na kawo maka yanzu"

Kujera ya zauna yace da Ammar ranka ya daɗe bismilla ya masa nuni kusa dashi.

Kusa dshi ɗin Ammar ya zauna yana sauraronsa.

Ɗauke da fara'a a fuskar Dr Mujahid ya kalla Ammar tare da miƙa masa hannu yace,

"ina son na fara tayaka murna kamin takardun sunzo gareka"

"murnata fa tame"

"albishir ne babba nike son yi maka wanda kuka jima kuna tsammayinsa amma sai an fara bani goron albishir tukunna"

"kaga Dr bani son wasa faɗi dan Allah ka daina ja mani rai"

Murmusawa Dr Mujahid yayi yace, "madam na ɗauke da juna biyu na tsawon wata huɗu"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now