Page 72.

976 85 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


         *Story~Written~Edited*
             *_By Miss Xerks_*🌺



        *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...


*72*
Washe gari ƙarfe bakwai suka fito inda suka nufa library direct dan daren jiya basu samu sunyi karatu ba musamman ma Hidaya da baccinta ta sha.

Basu fito ba sai 11 saboda lecture ɗin da suke dashi na nursing practice,koda suka fito sai da suka tsaya suka saya gurasa suka ci a masallaci sannan suka wuce hall.

Malama Samiha dake masu nursing practice bata samu zuwa ba sai Mlm Abba ne yazo ya amshi period ɗin nata.
Yana shiga suna shiga Allah ya kiyaye su bai rufe ƙofa ba.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya miƙa masu attendance sheet suka fara rubuta sunansu shi kuma ya fara lecture nasa na sociology.

Yana koƙari ba kaɗan ba dan indai yay lecture sai an fahimta duk jakantar mutum sai dai kuwa in baiso ba.

Ya rage 30mint prriod nasa ta ƙare yace "tear a sheet of paper" nan ya rubuta masu quize sukai tare da sanar masu next lecture nasa test zaiyi saɓanin sauran malaman da kai tsaye suke shigowa ba tare da sun sanar ba.

Quize ɗin ba wuya nan da nan sukayi sukai submitting bayan sun gama ya tattara takardun nasu ya bama classrep yace ya kai masa office.

Fitarsa Hidaya ta sauke ajiyar zuciya da ƴar daria, "Maryam Allah ya rufan basket ɗin asiri"

"hhhh dame fa"?

"wlh da bazan shigo ba dan na raina lecture ɗin mutuminn da tini nayi lossing ɗin 20mrks,oh Allah ya soni"

Dariya Maryam tai tace, "Allah kam ya soki tashi mu tafi muyi sallah mu ɗan huta kamin foodtaboo ya shigo kuma ya gasa mu"

"oak muje"

Sakkowa sukai daga steps dai2 da daza su fita sukai kiciɓis da maimuna.

"ku ina zaku haka"?

"masallaci mu huta"

Dariya Munirat tai wadda ke tare da Maimuna tace,

"yaran nan kuna wasa da foodtaboo,to na rantse maku da Allah rashin mutuncinsa ya wuce inda kuke zato ba kuga kowa ya kasa fita ba, kaɗan daga cikin aikinsa a rashin attending ɗin nan da kuke ya baku CO"

"mtswww in ya fasa,wai ina ce ma dai sai 2:30 zai shigo to akan mi kuma zamuyi ta zama kalla fa kiga 1:30 yanzu,ke dalla mu tafi bazai yiwu akan tsoron wani banzan malami muƙiyin sallah ba"

Hidaya ta tura Maryam dan su wuce.

"hmmm shawara mudai muke baku ba wani abuba,mutumin nan na sako ƙafansa bakin hall baka isa ka shiga ba bare kuma ya zira ƙafarsa ciki,amma kuje idan uzuri gareku in kuma har yazo baku dawo ba ma kiraku"

Maimuna tace dasu dan ita tana tsoron rashin mutuncin foodtaboo.

Maryam tace da ita, "yauwa Maimuna dan Allah da kun hangi motarsa ki kiramu ,sallah ma kawai zamuyi mu dawo kuma zan rakata asibiti amso magani in Allah ya yarda bazamu jima ba,ki tsaran mana seat kinji"

To Maimuna tace suka shige hall su kuma suka tafi.

Suna tafe Hidaya ke tambayan Maryam, "wai ya sunan food-taboo na gaskiya ne?"

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now