🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Miss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*79*
adaren wannan ranar suka angwace abinsu.safiyar yau Zaune suke kan dinning suna break fast Mansur yace da ita, "My Noor anjima saiki shirya muje mu gaida su Hajia ko",wata kunya ce ta mamayeta, duk tsawon zaman da sunkai na wata biyar bata taɓa zuwa ta gaidasu ba, "kinyi shiru","to Allah ya kaimu" tace dashi suka cigaba da cin abincin.bayan sun kammala ta kwashe kayan abincin ta shiga dasu kitchen,kwance ta dawo ta samesa kan kujera yana danna waya,kusa dashi ta zauna inda ya ɗago da ido ya kalleta da cewan sannu,hira suka shiga yi yake ceda ita ,my noor idan mukaje saimu taho da irfan ko,ƴar dariya tayi tace tab ce zakai sarkin rigima kaga honey randa baka da lapia da sukazo rashin mutuncin daya dinƙa mani daya bani haushi ai har dukansa nai hajia tai tamani faɗa.hmmm aike ce mai rigiman ma bashi ba,toni kuma minai da nazama ƴar rigima honey,kin manta kukan da kika sha jiya kan nace zan tafi na barki,wai dama haka kike sona da yawa har baki son nayi nesa dake,hmmm tace tana murmushi sannan tace to waima ya zancen tafiyar ka fasa zuwa,dariya yay ya miƙe dga kwancen da yake ya lakuto kumatunta yace kinsan Allah dama ba wani tafiya da zanyi,nayi hakan ne dan na tabbatar da abinda na ganin cikin idanunki,ɗan cuno baki tayi da cewan to mika gani,hmm sona mana,yanzu da'ace banyi haka ba haka zaki barsa acikinki ya cutar dani dan bake zai cutar ba.lumshe ido tayi da jin yanda ya zago da hannyensa weast ɗinta yana murzawa.kishingiɗa yay daga kujeran ita kuma ta kwanto jikinsa da cewan wai dear da gaske da irfan zamu taho,ehh mana,kozai hanamu shanawa ne kawai a ƙyalesa yace da ita.hmm ni rigimarsa ce bana so ai duk su hindatu suka ƙara shagwaɓa shi Allah.to ai kinga ƙwamma muje mu ɗaukosa shima yazo yaji ɗumin iyayensa ko,ehh hakane,bayan sallar azhar daya tafi masallaci yace ta ahirya kamin ya dawo,koda ya dawo zaune ya sameta kan stool gaban mirrow tana taje kanta duk ta turɓune fuska tana shirin kuka saboda yanda tazan ke mata zafi.ta wuyanta ya sarƙalo hannyensa ya dubeta ta mirrow da kwatanta yanda tayi sai ta saki dariya,ynzu my noor tajan dole ne gafa idonki har yay ja sarkin kuka komi ki masa kuka.a'a Honey taza fa da zafi,to shikenan ki ƙyale kawai ki barsa ahaka.kayi inje gidan hajiya ahaka aima sai tace ni ƙazama ce,hhh to ai dama itace ace mutum tinda yazo gidansa watanni bakwai bai taɓa taza ba sai yau saboda miskilanci yay masa over,kallonsa tayi ta ɗan hararesa da cewan nito ka daina tina mani baya,yace da ita to shikenan na daina,yanzu kinsan mi za'ai,girgiza masa kai tayi shi kuma ya saki murmushi gami da kama gefen towel ɗinta datai ɗaurin ƙirji dashi zai kunce tai saurin riƙe hannunsa,Honey gidan fa hajia zamuje karmu ɓata lokaci,to gidan hajia zuwan dole ne maje wataran ko kuma da daddare,a'a nidai gaskiya a'a muje yau,duk da yanda yaso ta hanasa ya haƙura dole.nan ya tayata tajan gashin a hanaƙali wanda har akai la'asar bai gama ba saboda yanda yake jan gashin kaman wanda ke tararayan ƙwai,cikin dokakkiyar shaddarsu suka shirya wadda sunkai iri guda sunyi kyau sose,sarƙe da hannun juna suka fito ya buɗa mata mota ta shiga,kamin magriba har sun isa gidan da tarin tsaraban da suka kai masu,sose hajia taji daɗin ganinsu alhaji ma sai murna yake banda su umaima da suka rungume hidaya suna tsallen maraba da zuwanta basu barta ta zauna da hajia ba dan suna gama gaisawa suka ja hannunta zuwa ɗakinsu nan sukai ta hira,irfan ko da akace masa ga mama da gudunsa ya baro wurin hauwa mai aiki dake shirya shi yasha ball ya ɓata kayansa,yana zuwa ya ɗafe jikinta yana mama oyoyo,tana dariya ta rungumesa da cewan munyi faɗa ai baka daina wasa da ruwa ba ko.safra'u ce datazo wanka gida tai dariya tace tab wannan ɗan ai wataran saina ɗauresa da igiya ko anfa ƙulle famfo na compound sai ya tafi na toilet sai kace kwaɗo,dariya hidaya tayi tace to kaji anty safra tace zata ƙulleka da igiya irfan ɗina ka daina wasan ruwan kaga mura idan ya kamaka baya maka da daɗi kuma abbaa ma zai daina sayo maka chovulate,da sauri yace to mama na daina ina abbaa na,yana wurin hajia,daga jikinta ya sakko ya tafi yana tsallensa yay wurin abbansa daya buɗa masa hannu ya rungumesa dan mansur na bala'in son irfan a rayuwarsa.sai goma sannan suka baro gida irfan tin a mota yay bacci abinsa itama hidaya na shiga ɗaki ta kwance saishi ya cire mata kayan jikinta.bayan wata guda tana daga kwance shi kuma yana gyaran fuska ta kirayi suannsa honey nah,umm dear ya ankai,honey dan Allah yaushe zamuje pataskum in gano su inna,duk randa kika shirya,ai da sauri ta mike zaune niko yanzu ma na shirya,to tashi muje,uhmuhm nifa ka bar wasa Allah ina son ganinsu 9month fa rabona dasu,Allah da gaske nike maki nima duk randa kika shirya am ready too.da murna ta diro daga gadon ta shiga pacjng kayansu ko rabin awa batai ba ta haɗa komi,kallonta kawai yake yana ƴar dariya sai kace wadda zasu tafi yanzu,itama kallonsa tayi tace maza dai ka yanke.hhh shikenan sai a fasa zuwa,ahaba dai yi hanƙali ko ka bari idan ka gama dariyan sai kaci gaba dan so nike gobe iyanzu idan Allah ya kaimu ina kan cinyan Inna ta in kwana gadonta.ƙarashe zancenta ya kashe cliper ɗin ya dubeta da cewan au wai kwana zamuyi idan munje.batare data kallesa ba ta miƙe da jan trolly ɗin kayan nasu tace in kaji ana kwanaki to su zamuyi.ni kuma in dinga kwana aina,to baga gidan hydar nan ba saika wuce can.dama ba sona kike be idan allurar shauƙinki ta tsikare ni cikin dare in yaya kenan,ka miƙe ka jero salloli.ba wannan zancen kinga zancen gaskiya kwana ɗaya zamuyi.sakin kayan irfan tai ƙasa tazo ta ƙanƙamesa tana masa kukan shagwaɓa,nidai gaskya ban yarda ba dan Allah ko sati guda ne muyi,Swthrt ki tausaya mani mana kinfa san halina,to ba sai inna ta bamu wurinta ta koma wurin vaffa,koma baga ɗakina nan ba.ahh lalle yayi to tinda an sami solution miƙe kici gaba da aikinki.tashi tayi tana ƴar rawarta gobe sai pataskum shi kuma yaci gaba da nasa gyaran fuskan bayan daya gama yay ma irfan aski dama shike masa.tin uku dare hidaya ke farkawa ta tashi mansur tace honey ƙarfe nawa,can daya gaji yace da ita 12 na dare nan ta ya sami lapia ta ƙyalesa ya cigaba da baccinsa basu suka farka ba sai bakwai na safe dan sallar asuba basuyi ba kaman tayi kuka dan ita ayanda ta tamawa tafiyar 6 sun fita.aiko koda sukai sallah cetai su bari idan sunje can sayi wanka,mamaki ta bashi ba kaɗan ba sai daya lallaɓata sannan ta shiga tai wankan saɓi ɗaya ta fito tana shima idan yasan zai jima kawai ya wanke fuskarsa.girgiza kai kawai yayi ya faɗa toilet,yako sha bugu zaman da yay ganin yaƙi fitowa ta faɗa kawai tajawosa suka fito.sai tara suka ɗaga motarsu zuwa pataskum saboda irin gudun daya shatata ƙarfe huɗu suka isa aiko cike da murna inna ta tarbesu dan baffa bai nan lokacin da sukaje.lalle mutan adamawa irn wannan bazata haka,rungume da innarta tace ai inna ce nai sai dai kiganmu kwatsam.gaskiya ne naji daɗi sose sannunku da zuwa mu shiga daga ciki.tom inna bari na kirasa ko,nan ta juya zuwa waje inna ta bita da kallo tana mai farinciki dan ganin ƴar tata datayi ya tabbatar mata da cewan tana cikin kwanciyar hankali duba da yanda tayi ɓulɓul abinta alamu na babu wata damuwa atare da ita,hannun mukhtar ta kama sukai ciki kamin su kuma suka shigo daga baya.shinkafa da lafiyayyen miyan kaji inna tayi masu sukaci sukai ƙat,Kwanansu goma mansur yace to ta shirya suje gidan amininsa hydar,sun jima sose gidan hydar suna hira dan tin biki rabon su da haɗuwa,itama hidaya sai ayau taga kibɗiyya matarsa dan koda sukaje biki bata ɗaga kai ta kalleta ba.sai gabanin asri sannan sukai sallama suka wuto.akan hanyar komawarsu Mansur yace kai bari na kira modibbo ya kamata naje mu gaisa,kallon hidaya yayi ya ɗanyi ya kamo kumatunta da wasa yace madam kin gaji ko kiyi haƙuri akwai wani aboki na nan shima ina son muje mu gaisa in masa ya gajiyar biki.shiru tayi masa tana son tace masa aa dan shi mansur kwatakwata bai san wata alaƙa data faru tsakaninsu ba.kinyi shiru yace da ita yana kallonta,muje mana dear nagaji da yawa wlh,to bari nayima hydar waya ya bani address ɗinsa dan baan taɓa zuwa ba.wayan hydar ya kira nan yake faɗa masa yace ya gode sukai sallama.basu ɗau lokaci ba ahanya suka isa gidan,sai da mai gadi ya fara sanar da ammar ta wayar landline ɗinsu tukunna yabasa izinin ya buɗa masu gate su shiga.kai wato modibbo da soja ne ba ƙaramin tsaro zaisa cikin gidansa ba,uhmm kawai hidaya tace dashi nan suka nausa hancin motarsu zuwa ciki bayan da mai gadi ya wangale masu haɗaɗɗen gate ɗin da aka sauya yanzu.da kansa ya zago ya buɗa mata ta fito irfan saƙale kafaɗarta saboda yay bacci,asabe ce tayi masu iso zuwa part ɗinsu sadia.Ammar na zaune parlo yana kallo suka shiga,ganin mansur ya miƙe fuskarsa sake ya miƙa masa hannu sunkai musabaha yana angoango shigowar yaushe,wallahi yau kwannanmu goma,lallai sannu da zuwa bismilla ga wuri nan ku zauna.zama sukai kujera guda shi kuma ammar ya zauna gefe da tasu.ina yini hidaya tace dashi yace lapia lau amarya ya gida,lafiya lau,yace to madalla.mutumina kana jin daɗi wata ƙiba fa naga ka ƙara mansur yace da ammar,da ƴar dariya ammar yace ba dole ba amma dai ka leƙa ma hydar ko,daga can ma muke nace to bari mu biyo tanan karmu koma ya zama shiririta abin.gaskya kam ka kyauta,bari na kira maku madam ko.wayarsa ya danna numban sadia ya kirata yace tazo tayi baƙi,batafi minti biyar ba ta sakko goye da affan bayanta.ganin hidaya ta saki ihu da faɗin sis,oyoyo ta tafi da sauri ta rungumota,irin wannan bazata haka,uhmm wlh tafiyarma ba shiri munje anguwa ne yace bari mu biyo tanan dan banma san nan zamuzo ba,lallai ne amarsu iyee ansha ƙamshi amma fa duk da haka ina fushi dake ace kinzazzo koki leƙon.hmm wlh banfa zo ba sai yau,ahh na yarda irfan bacci ake,umm wlh.mansur daya saki baki tin ɗazu yana kallonsu yace wai dama kunsan juna ne?murmuahi hidaya tayi tace to Ehh mana ƙawata kuma ƴar'uwa ai zakaji ina sadia to itace,ehhh gaskiya haka kam.nan sadia ta juya ta gaisheshi tare da miƙewa ta shiga kitchen ta ɗan haɗo masu wani abu haka na motsa baki ba daɗewa ta kawo masu.wai anya kuwa Madam wannan girki naki zai shiga,mansur yace da ita.ahhh karkayi mana haka kazo gidan abokin naka kace bazaka ci komi ba tafiya fa kukai.ba haka bane tambayeta ba daga gida muke ba,ehh toko ma dai minene kuci ko yane koda yake ni baruwana gaka gashi nan ni bari naja ƴar uwata.hannun hidaya ta kama bayan data ɗaukar mata irfan dake bacci har yanzu sunkai ɗakinta.zama sukai ta aje mata snacks da juice ɗin datai masu,kallonta hidaya tayi tace anya seesee wannan haɗi naki kuwa zai sami shiga cikina,hararta sadia tayi tace to walaƙanta ni kinji saiki daɗi,har kin isama kizo mani kice bazaki ci komi ba.kai seesee nifa ba hakana nike nufi ba Allah daga gidan abokinsa muke mun cika cikinmu da yawa.uhmm kedai ko kice mani babynmu baya so,murmushi hidaya tayi tace wa ba wani baby Allah na ƙoshi.ke wlh saikin ci aje mayafin naki kaman wata baƙuwa.kaɗan hidaya taci snacks ɗin ta bari,sadia bataji daɗin hakan ba nan tace kinga idan waNi abin kike so ki faɗan na girka maki.Allah seesee da ina son wani abin zan faɗi maki.to shikenan in kawo maki awara.aiko da sauri hidaya tace mutuniyata zakice maza kawon.sadia na daria ta miƙe ta fita ta kawo mata tana tsokanarta lalle babynmu ɗan kwaɗayi ne.kedai seesee wai ina kika ganni da wani ciki kike ta wani faman babynki,ke dalla can kin isa kice mani yanzu baki kamu bane wanna irin hutu ma zakiyi haka kusan fa watanki tara.hmm taranne ma koma nace goma.awarar hidaya ta ɗauka wadda taji ƙwai a suyarta ga taruhu dataji aciki tayi daɗi,tab seesee amma dai wannan awaran bana saidawa bane.umm kinga ɗazun adda tayi mana ita da safe kedai maza kici in kuma na juye maki a cooler.da murmushi hidaya tace da kinsami ladana kuwa kinsan ina son in yita agida amma bazan iya ba saboda wahala.aike kinfiya son jiki awaran da yanzu ba wuya.Allah seesee koyan to.nan sadia ta koya mata duk yanda zatayi cikin ƙanƙanen lokaci kuma a sauƙaƙe.sun jima sunata hira hidaya sai ƙoɗa kyan affan take wai duk yafisu kyau.da murmushi sadia tace hmm haka ake cewa ai bama kiga kyau ba saina haifi ƴata tukunna.dariya hidaya tayi tace au har kinsan mai kyau ma zaki haifa kice in fara shirin dawowa suna idan na koma.sadia tce ke rufan asiri banda komi gaba ɗaya nawa affan ɗin yake shekara biyu ba fa,wai dai ina cewa ne idan na haifi mace kyanta saiya fi nasa insha'Allah..Allah yasa to amma nifa sai nake maki ganin kaman dai.ɗan buguɓta sadia tayi tace ke bar wannan wasan dan Allah tazaran ƴaƴan gidanmu five years ne kuma nima hakan zanyi da yardan Allah...hidaya tace a'a wlh bamu yarda ba..haka sukai ta hirarsu dan sai dasu mansur sukaje masallaci sunkai sallah tukunna mansjr yace ta fito su tafi.kwanansu goma sha biyu sannan suka koma gida hidaya harda kukan ta.
Kwana uku da dawowarsu yau da rana hidaya tayi lafiyayyan damu mai rai da lafiya da awara haɗe da kunun aya mai tsinke kunne ta jerasu kan dining.da kanta tajw ta taso Mansur a ɗaki,yana murza hannayensa ya ɗale kan kujerar dining yana iyee yau wanna irin girki aka mani haka ƙamshi tin daga ɗaki.umum dear tin kan yakai cikinka,plate ta ɗauka ta zuba masa ai da fara ci sai santi kaman me nan hidaya ta fara dariya."wato my noor kinsan me",kaɗa masa kai tai tace umum sainaji daga gareka tukunna.wato rabona da cin irin wannan dambun tin 1918,da zaro ido hidaya tace 1918 fa kace ba 1980 ba.ƙwarai kuwa ai alokacin nake ce maki tsabar ƙwarewar mai damun nan da da gero take yinsa haka idan ta zuba maka zata shara masa ruwa akai bayan angama abin ba'a cewa komi kunnenka har wani kaɗawa yake.dariya harda kifawa hidaya,tsai da cin nasa yay yace mi kikema dariya haka."ahh to honey ba dole nayi dariya ba,cefa kai wai bayan an gama damubun a shala masa ruwa bama mai ba,tab gaskiya na bala'in iya girki",ta ƙarashe maganar tata tana kuma kifawa da dariya."wai kina nufin ruwa nace ba mai ba". "au baka san ma mikace ba kenan lalle",miƙewa tai yana mai bin jikinta da kallo ta zago ta kamasa."yadai mizaki mani kuma",a'a honey sakkowa zakai.mu koma ƙasa ka ƙarasa cin abincin nan kar asami akasi wurin santi ka kifo". Kamasa tai ta zaunar dashi ƙasan carpet ta cigaba da ciyar dashi.bayan ya kammala ya ɗauki irfan suka fita bai dawo ba sai yamma inda ya dawo ya sami hidaya kwance tana bacci.tashinta yay ta buɗa idonta da ƙyar tana yamutsa fuska."lafiya dai noor kika kwanta da yamma haka bayan kinsan ba kyau baccin yamma irin haka".da kyar ta miƙe zaune tace dashi honey wlh kaina ke mani wani irin ciwo mai azaba" ,"subhanallah ciwon kai kuma to sannu bari na ɗauko maki paracetamol kisha ko kinsha wani maganin"? Umun ta gyaɗa masa kai nan ya mike zuwa ɗakinsa ya ɗauko maganin ya dawo.ya ɓallo zai bata yace anya mako kinci abinci dan ɗazun bakici ba naita fama dake kikace ke kin ƙoshi."to ai bakin nawa ne ba daɗi naso naci naji bazan iya ba kuma kaga ma har kunu na dama sai ijjesa nayi na kasa sha wlh kaman ma zazzaɓi keson rufeni", jikin nata ya taɓa yaji zafi rau,innalillahi noor wannan ai ba ƙaramin ciwo bane Allah yasa ba malaria fever bane kece in ance ki shiga net ƙememe kiƙi."net zafi garesa duk ka kasa samun bacci mai daɗi". Allah ya sauƙe yace ya miƙe ya ɗauko mata awar ɗazu,da ƙyar ta samu ta iya cin uku ya bata paracetamol ɗin tasha.bayan tasha ta kwanta saman cinyarsa tana son tayi bacci ta kasa saboda tashin zuciyar da take ji.kan kace mene amai ya kubce mata da gudu ta miƙe tai toilet sai shaaa,hankalin mansur tashe yazo ya riƙeta yana mata sannu,ta ɗau lokaci tana sharara aman dan saidata amayar da komi dake cikinta ya rage sai ruwa dake zubowa wanda ke neman shiɗar da ita.jikinta ya ɗauraye mata yace kotaci wani abin tace a'a.kan gado ya kwantar da ita saboda sanyin datake ji ya rufeta da blanket.wadrob ya buɗa ya ɗauko mata hijab ɗinta yace bari su wuce asibiti kawai dan duk yanda ankai ulcer nan ce.Abbaa ina zamunje irfan dake game a wayarsa ya tambayesa."asibiti" ya bashi amsa yayin da yake ɗaukan key saman center table. "Abba waza'ama allura" ,ba allura bane Son Mama zamu kai bata da lafiya" , Allah sarki Mama Allah ya bata lafiya" amin mansur yace ya bashi key ɗin motan yace ungo riƙe to bari naje na ɗaukota mu tafi ko" amsa yayi ya koma kan kujra ya zauna yaci gaba game ɗinsa.ɗakin mansur ya koma ya kamota tace aa nidai ka barni basai munje asibitin ba kamin safiya zanji sauƙi.taya zan barki ahaka,kiga maganan ma da ƙyar kikeyi abinci yaƙi zama cikinki ki daure ki tashi muje.Allah honey bana son wannan ɗan banzan maganin dazasu bani mai shegen ɗaci.zance karya baki amaki allura kawai yi haƙuri ki taso.yana lallashinta ya kamta suka fita.suna zuwa ba ɓata lokaci duba ɗaya da likitan tayi mata tace sai anmata gwajegwaje har mansur yace no need dan yana tabbacin ulcer tace kawai tai murmushi tace aa ya bari dai ayi test ɗin.cikin mintina kaɗan aka gama mata abinda za' amata suna zaune likitan ta kirasu nan ta tabbarwa da mansur cewan madam na ɗauke da cikin wata biyu,kallon bai fahinci maganar dakike ba yay mata.da fara'a ta kuma ce masa ƙwarai kuwa tinda gadai abinda result ya bamu ka duba ka gani.dubansa yay ƙwarai 2month oregnancy."to amma likita abin ya bani maamaki", "hmmm alhji kenan ai ba'a mamaki da ikon rabbi ko,jarabawa ce Allah yayi maka abaya domin ya gwadaka zaka iya jure rashin na tsayin wani lokaci kuma muma sautari akan sami kuskure wajen gwajegwajenmu." ,tana kai aya ya girgiza kai yace ehh hakane likita ba'a mamaki da ikon ubangiji amma kamar yanda kikace kuna kuskure inaga anan ɗinma kunyi kuskure a sake gwajin nan agani.to tace dashi suka ƙara gwada hidaya sakamako ya kuma tabbatar masu da ciki ne na watanni biyu harda ɗorin sati guda akai.wayyo zokaga daɗi wurin mansur da hidaya tamkar an masu bushara da aljanna,godia kawai suke ga Allah,mukhatar dayaga yanda suke yace Abbaa wai murnan me kake yace Son ƙanwa ko ƙani za'a maka.a rashin fahimta yaron yace ƙanwa kuma.ehh mana munje mun sayo baby ne asibiti yanzu irin ta anty safra'u."mama ce ta sayo irin na anty safra mai kuka inyainya" da dariya dukansu sukace ehh irinsa .murna shima ya fara za'a sayo masa teddy mai kuka idan ta girma tayi magana.tin a mota mansur ya kira hajiya ya sanar mata itama murna ai tana faɗiwa su umaima sai gida ya kaure ta ihun murna.dako suka koma gida yanda yaga hidaya take na rashin jin daɗin jikin nata saice yay ko goyaki zanyi saiki fi jin daɗin kwanciyar.hmm kai honey idan ka goyani taya kuma zaka iya baccin.sai nayi rufda ciki mana taso kiga.ganin da gasken yake tace umum ka barni zan iya ahakan yunwa dai nikeji.abinci ya ɗauko ya bata taci shima bai zauna ba ta amayar dashi.sose yaji tausayinta hakan yasa ya ɗora saman cikinsa ta kwanta duk da uban gumin dayake ketawa saida yasa masu blanketa saboda sanyi da ita tace tana ji.baccin ma shi gaba ɗaya kasashi yayi saboda farinciki daya gama mamaye shi.*KUYI HAƘURI DAN ALLAH DA CANJIN RUBUTUN DA KUKA SAMU NA KWANA BIYU WLH BANI DA ENOUGH TIME NE MUNA BIKI KUMA IDAN NACE SAI MUN GAMA ZAN MAKU TO GASKIYA ZAKU JIMA BAKU JINI BA SABODA BAYAN BIKIN NAN MA AKWAI HIDIMAR DAZAN SHIGA,.*
_SHARE AND COMMENTS._
*Xerks*✍🏼
![](https://img.wattpad.com/cover/188462047-288-k516781.jpg)
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.