🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*~By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*46*
Kamar yanda su Adda suka alƙarwanta ƙarfe 8 suka aika driver ɗauko su Inna.
Koda suma dama tin asuba suka gama shirinsu jiran ɗauka kawai suke.
Drivern na zuwa ba ɓata lokaci suka fito Gwaggo Amina goye da Mukhtar sai Hidaya riƙe da Inna,
Gama shigarsu ya tasa hancin motar direct to Modibbo Specialist Hospital,Kasancewar an san da zuwansu wanda tin a jiya Ammar ya gama cike duk wasu takardu.
Ko 30mints basuyi ba aka shiga da Inna I.C.U.
Suna nan zaune ita da Gwaggo Amina suna jira su Adda suka ƙaraso.
Da ganinsu ta miƙe ta tarbosu tana goge hawayenta.
Gaisuwarta kawai Adda ta amsa ba sakin fuska bata kuma tsaya sauraronta ba tai gaba zuwa ciki.
Sadia ce ta dafata tana lallashinta, "ki daina kuka mana Hidaya keda ya kamata ki mata adu'a Allah yasa an shiga asa'a"
"Sadia sunce fa idan aikin baiba sai dai a yanke"
"A'a nufi in ba'ai aikin ba shine sai dai ayanke amma indai akai aiki to insha'Allahu za'a sami lafiya ,dan haka shara hawayenki kinji my sis"
Gogen hawayenta tayi cike da son aminiyar tata ta kalleta tace, "na gode sose sis Allah ya barmu tare ya baku ladan aikin ladan da kuke"
Itama da na smile ɗin tace ,"Amin"
Kukan Mukhtar ne yasa ta juya ga Gwaggo Amina ta gallawa ƙaramin yaron da baima san mitayi ba harara wanda he is only 13months.
"ki bashi yasha ko Hidaya, yau yayi haƙuri ai" Gwaggo Amina tace da ita.
Juyar da kanta tai ta ɓata fuska.
Girgiza kai Gwaggo Amina tayi ta taso kwana biyu ta lura sam Hidaya bata son bashi nono sai dai yayi ihunsa ya gaji ruwa da koko kawai take ɗirka masa.
Hannunta ta buɗa tasa mata shi kan cinya,
"gashi nan ko ki bashi da kanki ko kuma wlh ni in zaro da kaina na bashi,wannan ai iya shege ne yaushe rabonki da bawa yaronn nono tsabar ɗaukan haki, ko dan kinga ana ƙyaleki shine iskancin naki zaici gaba to baki isa ba dalla amsa shi ki bashi yasha"
Kaman ta sa ihu haka taji ,kwatakwata yanzu bata ko ƙaunar ganin yaron gaba ɗaya haushinsa take ji.
Fuskarta turmuƙe ta amsa shi ta wani langaɓar da kansa kamar zai faɗi.
sai da Gwaggo Amina ta mata da gaske sannan ta basa yasha.
Yana ƙoshi Sadia ta amsheshi tana masa wasa.
"Ashe kin haihu shine baki taɓa zuwar mana dashi ba?"
Amsa ta mayar mata da ɓacin rai, "sau nawa na taɓa zuwa gidan naku da zaki wani ce ban taɓa zuwa dashi ba"
"Kai Sis yi haƙuri kar laifin nasa ya shafeni"
Tambayarta wace Gwaggo Amina tayi tace ita ta sauke mu da muka zo nan garin.
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.