🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*33*
Tinda Adda ta farka a motar kuka kawai take tana ambaton Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha har suka isa ga police station ɗin.
Yahya dake driving bai ƙarasa parking ba Adda ta buɗe da gudu ta fita tana ihun kuka.
Tin daga waje take ƙarya ne bai aikata ba sharri suka masa ku sakar mani ɗan'uwa dan Allah dan Annabi innocent ne bazai aikata hakan ba har takai ga cikin station ɗin.
ɗan sanda data hanga dake bakin ƙofa ta kama gam ta riƙe tana sai kun sakar mani ɗan uwa wlh sai kun sake shi.
Da sauri Rashida data shigo ta riƙe ta tana bata haƙuri.
Cikin kuka kaman ta shiɗe tace, "shi ɗaya ya ragen a duniya bani da kowa bani da wani gata sai na Allah ,shima ni kaɗai gareshi idan na barsa anan ban san irin hukunci dazasu yanke garesa ba"
"Adda ki daina kukan insha'allahu bazamu bar nan ba sai da Hamma kuma makircin data haɗa sai ya koma kanta da izinin Allah"
Zubewa kan ɗan ƙaramin bench ɗin dake wurin Adda tayi tana aikin kuka wadda raɗaɗin da zuciyarta keyi ta kasa faɗin komi.
Da ƙyar da haɗawa da Allah su Abdullahi suka haɗa wani police daya taimaka ya haɗasu da D.P.O.
Shigarsu office ɗin yay masu izini dasu zauna bisa kujera.
Yahya ne ya zauna shi kuma Abdullahi ya tsaya tsaye.Bayan da Yahya ya miƙa masa hannu suka gaisa yake shaida masa cewan sunzo neman beil ne akan matashin saurayin da aka kama yanzu bisa sharrin da aka masa na cewan ya nemi ya haikewa wata budurwa har cikin gida.
"babu ƙarya ko sharri acikin wannan lamari domin kuwa mu da kanmu mukaje har gidan kuma muka sameshi a hali na maye wanda hakan ya tabbatar mana da lamarin gaskiya ne wanda mu kuma a yanzu zamu miƙa case ɗin ga kotu dan case ɗin babba ne kuma shi mijin yarinyar yace bazai yarda ba"
Da haƙuri dai haka suka dinga haɗa D.P.O da karya shigar da ƙara kotu domin abin zai zama babba.
Da ƙyar D.P.O ya yarda da cewan zai basu beil amma sai sun biya dubu talatin.
"Haba yallaɓai dubu talatin sunyi yawa ka taimka ka rage mana ko dubu biyar ne sai a baku mu masu ƙaramin ƙarfi ne"
Dariya D.P.O ɗin yayi ya murza kujerarsa ta juya dashi wul ta maido da dubansa ga Abdullahi da yayi maganar.
"hmmm wai dama baku shirya beil ɗin nasa ba kuma kuka biyo sahunsa,
To bari kaji ahaka ma ganganci zanyi na baku shi saboda ban shigar da case ɗin nasa cikin file namu ba saboda nasan tabbas za'a biyo sahunsa tinda abin harka ce ta kuɗi"Yahya ne daya ɗan numfasa yace, "kayi haƙuri ranka ya daɗe karka shigar munji zamu bada dubu goma iyaka abinda muke dashi kenan"
Dukan table ɗin nasa yayi ya ɓata fuska inda yay masu nuni da ƙofa dasu fita.roƙonsa suka shiga yi ganin sunƙi fita ya ɗau record book ɗin inda ya shigar da sunan Ammar bisa aikata laipi na faɗe.
shima Abdullahi ransa ɓace ya dubi Yahya yace su tashi su fita. "Allah ba ai ba azzalumin bawansa bane gaskiya kuma bata taɓa ɓoyuwa,sharri kuma ɗan aikene"
KAMU SEDANG MEMBACA
HIDAYAH NOOR completed.
Fiksi SejarahHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.