🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*56*
Saurin tafiya ya dinƙayi harya isa ga ɗakin.Yana zuwa ya murɗa handle ya shiga,rass gabansa yace sakamakon hango Sadiya da yayi kwance kaman matacca da oxygen ga jerin drip har shida duk an ciresu na bakwai ɗin na shiga.
Ƙwalalo ido yay ya ƙarasa wurinta yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Jiki na rawa ya kama hannunta murya a raunane yace,
"Hayatee nah"
Kaman yasa kuka ya rungumeta tana daga kwancen.
"Hayatee wanna irin ciwo ke damun mani ke haka,bana sonsa ko kaɗan na tsani duk wani abu dazai taɓa mani lafiyanki "
Muryar Gwaggo Amina tasa shi ɗagowa daga jikinta idonsa jajir.
"Gwaggo"
"na'am Alhji ka ƙaraso"
"na ƙaraso Gwaggo""kaganta ko ai yanzu jikinma da sauƙi tinda harta samu tayi bacci amma ɗazu abin ba kyau,kuka sai an kiraka ka cire mata kai amai kuwa kaman zata amayar da kayan cikinta,yarinyar nan ai ta wahaltu"
"Gwaggo to mai suka ce yana damunta ,nifa bani son abinda yake taɓan lafiyanta"
Ya faɗi da sake damƙar hannunta yana murzawa.
"karka damu sunyi mata gwaje-gwaje dan harma fitsarinta suka ɗauka sun kuma tambaya tana da ciki nace masu babu tinda kaga kwanan akai gwajin cikin babu"
"ina reslt ɗin yake"
"ai basu kawo ba tukunna"
"to mi suke da har yanzu da basu kawo ba"
Ya faɗi da ɗan faɗa yayinda ya zira hannunsa ga aljihu ya zaro wayarsa ya kira Dr Mujahid.
Koda Dr Mujahid ya ɗaga Ammar na amsa sallamarsa cikin faɗa yace dashi,
"Dr mi kuke da har yanzu baku kawo result ɗin madam ba,kasan kuwa a irin halin da take ciki kodan ba matarka bace"
"Ranka ya daɗe ai kai kace abar nata ayi na waccen yarinyar daka kawo shiyasa amma yanzu insha'Allahu za'a gama sai ayi nata"
Sam shi yama manta da yayi wannan zancen,"to lab ɗin ɗaya ne ,ai saboda faruwar ugent abu akayi da yawa ko ko kuma kai ɗaya ne likita"
"kayi haƙuri ranka ya daɗe naga baka son kowa a wurin iyalinka ne idan bani ba"
tsoki yay ya katse wayan ya ajiye.
Hannunsa yasa ga kumatunta yana shafawa,"Allah ya baki lafiya Baby nah yasa kaffara ne"
Gwaggo Amina dataji shi ta amsa da amin inda ta nemi wuri ta zauna dan ta huta itama.
Shiru yayi yana kallon ta kallon so da kuma tausayawa.
Kissing nata yay a wuya ya kwantar da kansa ga gefenta.
Wayarsa datai ƙara ya ɗaga ya kara a kunne ganin sunan Adda jiki.
"Salamu alaikum" Adda tai sallamar.
"wa'alaiki salam"
"Ammar ina Sadia n ya jikin nata Ammar"?
KAMU SEDANG MEMBACA
HIDAYAH NOOR completed.
Fiksi SejarahHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.