Page 27

1.1K 78 0
                                    

🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



        *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺



      *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



*_Ummu Nasreen saƙon soyayyarki fisabilillah gareni ya iso,wlh sosai naji daɗi na gode na gode da saoyayyar da kike mani dan Allah...nima ina sonki matuƙa ana tare_*🤝🏼


*27*               

Washe gari ƙarfe goma na safe Maman Hauwa da Mijinta sunka ƙaraso asibitin da kuɗin gida da aka saida.

Adda na amsa da godia ta wuce wurin Kawu dake zaune daga bakin ɗakin da Ammar yake.

Tsugunawa tayi ta gaidasa ya amsa mata,miƙa masa kuɗin tayi yasa hannu ya amsa yana duban kuɗin.

"Waɗann fa?"

"Kawu miliyan guda ne, aciri dubu ɗari biyu a bada kuɗin aikin daza'ama Inna da kuma kuɗin karayarta.
Sai kuma a ɗauki dubu ɗari da arba'in kuɗin Ammar.a fitar mana da dubu hamsin saboda zirgar yau da gobe ta magani,ragowan kuma Kawu dan Allah gidanmu daya rushe nake so a fara mana aikinsa kamin a sallamemu" ta ƙarasa faɗi da kuka.

Tinda ta fara magar kan Kawu na ƙasa sauraronta kawai yake har ta kai aya.

"to aina kuka samo wannan kuɗin Halima?"
"can gidan da Ammar zai zauna muka saida"

Har zai mata zancen aikin da ankace shima Ammar ɗin za'a masa sai kuma ya fasa.
Sauke numfashi yayi kawai batare daya ce da ita komi ba ya miƙe ya fita.

Cikin awa guda suka gama biyan kuɗin komi,
Nan danan ko aka zo aka ƙarasa sama Ammar jini dama roba biyu ya rage jiya yasha biyu amma duk da haka har yanzu bai motsa ba...,ita kuma Inna aka shiga da ita ɗorin karaya.

Duk da Allurar da akama Inna na kashe zafin ciwo hakan bai hanata jin zafi ba dan tasha kuka ba kaɗan ba.

Haka su Hidaya ma suka zauna sukai ta kuka ana lallashinsu kaman ana tinzirasu.

Bayan an gama da Inna shima Ammar aka miƙashi ɗakin ɗori.
duk da karaya biyu ce ga jikinsa hannu da ƙafa har aka kammala baima san anyi ba.

Bayan dawo dashi nan room ɗin dayake aka maida masa da ragowan leda guda na jini.

Adda da Yusrah nadaga ƙasa kan tabarma sunyi jugum da tagumi suna jiran yanda ta Allah zata kasance da Ammar tinda ga jini dai ya kusa ƙarewa zai farka ɗin ko kuma akasin haka ne zai kasance.

Hidaya ko ita na daga gefen gadon hannunta kan hannunsa mai lafiyar da aka maƙala masa jinin.

A hankali taji ya ɗaga yatsansa guda,ƙifta ido ta kama tana duban yanda yake ɗagasu har ya ware duka tafin hannun nasa.

Murna fal cikinta wangale da haƙora tace,"Ad,Adda taso kiga Hamma ya motsa"

Du su biyun suka miƙe suka tsaya kansa suna kallonsa da ɗan murmushin da bai gama cika fuskarsu ba.

A hankali kuma sukaga ya juyar da kansa ya kuma juyarwa da alamu dai wuyan nasa a sage yake.

Ganin da gaske dai motsawar yake da gudu Adda ta fita ta kira Nurse Nusaiba.

Tare suka dawo itama da ƴar murna ta nufi wurinsa dan duk hankalinsu na kansa tin jiya mutum da alamu na rai ajikinsa kuma ace har yanzu bai motsi.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now