🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀
*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*50*
*****_MONDAY 21 JAN 2019 ,ADAMAWA STATE HIGH COURT 11:00am_*
mutanene maƙil zaune cikin Babbar kotun dake adamawa kowa na jiran isowar Alƙali.
Sadia kwance bisa kafaɗar Adda idonta runtse gabanta na tsananta faɗuwa.
Ammar wanda ke gefe da Hamma Abdullahi ya rafka uban tagumi zuciyarsa cike da fargaba.
Yahya da Kawu da duk wasu masoya goyon bayan Ammar suna hayaniya samasama Allah yasa gaskiya ta bayyana.
Ƴan sanda ne suka shigo riƙe da Hidaya,hangensu Baffa ya miƙo zuwa garesu tare dama ƴan sandan sallama.
Wanda ke riƙe da sanda hannunsa ne yace, "Baba nan ba wurin hira bane kana iya bari ka gana da ita daga baya idan shari'ah ta ƙare"
"dan Allah minti biyu kacal nake da buƙata ku bani"
D.P.O ɗin baya daya kama Ammar shi ya kalla Baffa yace, "oak amma kayi da hanzari dan Alƙali na gab da shigowa"
Hidaya ya kalla wadda kanta ke ƙasa hawaye na zuba daga idonta.
"ƴata ba komi nake so nace dake ba illa nai maki tini da abu guda ɗaya, gaki akotu wanda nan da lokaci kaɗan zaki tsaya gaban Alƙali don faɗar abinda duk zuciyarki ta raya maki gaskiya ko kuma ƙarya kamin akai ga kotun Allah, dan haka nake shawaratarki da ki tsaya tsakaninki da Allah karki tinanin duniyarki ki tina da lahirarki sannan kar kuma ki manta da cewar maraya kika zalunta ,ki tina akan zaluntarsa da kikai duniya ke ƙyamarsa karki so hakan ta faru ga zuri'arki nan gaba dan kamtudini tudan duk abinda kai sai anmaka sharran au khairan, ki faɗi gaskiya dan ganin kyawun makomarki, na barki lafiya Allah yasa a warware a sa'a"
Daga haka Baffa ya wuce da matsar ƙwalla a idonsa da tsanin tausayama ƴar tasa.
Shiru kowa ke zaune ba jimawa Alƙali ya ƙaraso inda kowa ya miƙe tare da gaisuwar girmamawa.
Bisa wurin zamansa ya zauna bayan daya buɗa littafin dake gabansa ya ɗago da maganarsa.
"Assalamu Alaikum, kotu tana son sanin ƙarar da ake son gudanarwa, sannan ina mai roƙon Allah yabamu ikon aiwatar da gaskiya, kuskuren kuma da zamuyi muna roƙonsa daya yafe mana...Bismillah"
Magatakarda dake zaune ne ya mik'e da takardu hannunsa sannan yace,
"ACC FARUQ MODIBBO shi ke ƙarar HIDAYA SULAIMAN a bisa mummunan ƙazafi data masa shekaru biyar da suka wuce wanda ayanzu yake roƙon wannan kotu mai gaskiya da albarka data wankeshi daga wannan mummunan zargi da mutane ke akansa na cewar ya aikata zina da ita koya nemi ya aikata".
Gyaran murya Alƙali yay kamin ya ɗan gyara zaman glass ɗin dake fuakar sa yace,
"ko wanda yake ƙara yanada Lawyer?".
Lauyern dake sanye da tufafinsa na aiki ya miƙe da faɗin, "eh Ranka ya dad'e me girma me shari'a, nine Barrister MUHAMMAD HARUN ZAKARIA Lawyarn wanda yake ƙara".
Ya ƙarashe maganar tasa da zama.
Alƙali ya sake cewa, " Ko wanda ake ƙara tanada Lawyer?"
Nan ɗayan layern ya miƙe da girmamawa yace , "Sunana Barrister AL-MUSTAPHA AHMAD ƊAN YARORO nine Lawyern wanda ake k'ara".
KAMU SEDANG MEMBACA
HIDAYAH NOOR completed.
Fiksi SejarahHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.