Page 61.

886 71 7
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
        *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



        *Story~Written~Edited*
           *_By Mss Xerks_*🌺




      *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...

*_DOMIN FARINCIKINKU DA JINDAƊIKU MAMAN NASREEN, MARYAM NURA AND ANEESA MARAFA👌🏼_.*

*61*
Dama wayarta na ƙirjinta tin ɗazu take kiransa not recherble duk hankalint ya tashi.

Ganin kiransa ko da sauri  ta miƙe cike da farin ciki tai picking tare da karawa a kunnenta.

Sallama yay yajita shiru har saida ya kuma wata sannan ta amsa a hankali.

"Mahbub tin ɗazun nake ta kiranka not rechrble duk kasa hankalina ya tashi,fatan dai lafiya"?

"Ayyah sorry Baby nah laifin netwrk ne nima naita ƙoƙarin na kira yaƙi zuwa,karki damu mijinki na cikin ƙoshin lafiya,ya na barki umm?"

"ka barni da kewanka"

Bai jita ba saboda yanayin yanda take maganar kaman bata so ko mai ciwon baki dan haka ya sake ce da ita.

"Baby bana jinki fa"

Sake maimata masa tayi hakan yasa shi miƙewa zaune daga kwancen da yake yace,

"Hayatee ko baki da lafiya ne naji muryan naki yayi ƙasa"

Rungume da pillow nata ta juya kwanciyarta da faɗin.

"ehhh mana"

"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".....

Da shagwaɓar dake haɗe da murmushi ta tare maganarsa da, "to baka kusa dani ba dole komi nawa yay ƙasa ba musamman ma muryata"

Ajiyar zuciya ya sauke dan ya tsorata ainin datace bata da lafiya shirinsa daa yanzu ya miƙe ya tafi.

"kin tsorata ni da yawa kinsan bana sonki da ciwo"

"to aima dan baka ga yanda na koma bane abar tausayi kuma duk a rashinaka, kawai ka mani wayo ka tafi ka barni ni ɗaya ni dai kawai ka dawo yanzu"

Lumshe idonsa yayi gami da sauke numfashi yace,

"yanzu Kurratul ayni nah kyaso na taho yanzu, ƙarfe 11fa ki dai yi haƙuri jibi ya iyanzu kina tare dani kwance a duk inda kika fiso na jikina"

Kukan shagwaɓa ta fara masa wanda yake nishaɗantar dashi idan tanayi.

" kofa abinci na kasa ci gidan duk ba daɗi, nidai zan biyoka"

Hannunsa saman idonsa daya rufe yana jan hancinsa sose ta bashi tausayi sam baiji daɗi ba yasan dole tayi kewarsa dan bai taɓa tafiya ya barta ba batare dashi ba.

Ɗan ƙaramin tsoki yayi yaji dama bai taho ba kawai sawa yayi akawo Hidayan.

Maganarta ce ta katse tinanin da yake ,

"Mahbu ɗinah"

"ummm Hayatee nah,kiyi haƙuri kinji ni kaina kin ganni duk wani iri rashinki tare dani babu daɗi jina nake kaman a garwashin wuta, amma dan Allah ki daure kici abinci karki kwana da yunwa yanzu maza ɗauko muna hira kinaci kinji"

"ni bazan iya ci ba,gidan fa duk ba daɗi ko ina duhu babu iska duk a tsorace nike bazan iya fita ba" ta ƙarasa maganan da kukanta wanda take yinsa bilhaƙƙi da gaskiya.

Can Ƙuryar fadar zuciyarsa yaji kukan nata tamkar ana masa azaba da dalma.

Da muryansa datayi sanyi cike da tausayinta yace,

"kiyi haƙuri nasan yau dole ki kasance a duhu cikin zafi saboda nine hasken dake haska maki ko'ina da kike kasancewa nake kuma kawar da duk wani zafi dake raɓarki , sam bazanso ɓacin ranki ba bare zubar hawayenki, Rayuwata kuma hasken idaniyata,farincikina kuma muradin raina ki shirya gani nan dawowa yanzu izuwa gareki"...

Yay maganar inda ya miƙe yana neman rigarsa daya cire zai saka.

Jin abinda yace da fahimatr da gasken yake tai saurin katse shi,

"um-um Zumanaaaahh dare yayi da yawa kuma bazan hanaka abinda kajeyi ba domin anfanuwarmu ne, ka zauna ka nutsu kayi aikinka na kwana biyu, karka manta kamar yanda gangar jikinka ne ke anan ruhinka ke atare dani haka nima ruhina na atare dakai gangar jikina ne kawai ke anan dan haka babu batun kasancewata acikin damuwa sai dai nasan dole zanyi kewan tattausan jikinka daya fiye mani katifa daɗin gudanar da hutuna"

Dage mata yay shi kam dolen yanzu zai taho ya fasa kwana zai biyo jirgi, da lallami ta lallamesa ya haƙura.

Kan gadon ya koma ya zauna da faɗin.

"ummm naji to amma idan kina so na haƙura ki tashi dan Allah ki ɗauko abinci kici kina buƙatar abinci Baby nah na buƙata"

Bata musa ba ta miƙe yana mata daɗɗan kalami ta fita zuwa parlo ta ɗauko abincin da Adda ta kawo mata egg muffins ne sai lemun kankana wanda aka haɗa da madara.

Riƙe dasu a tray ta dawo ɗaki ta zauna yana mata hira tanaci har saida cikinta ya cika wanda rabin cikar tasa tausasan kalamansa ne.

Bayan data kammala yace tai tsalle sau ashirin yana jinta yana ƙirgawa kaman yanda suka saba kullum idan sukaci abincin dare,

Haka ta miƙe da dariya a hankali tana tsallen saboda Babyn dake cikinta har tai 20 cikinta ya zazzage sannan yace ta kwanta.

"gadon ma babu daɗi" ta faɗi langaɓe da kai tana turo baki kaman wadda ke gabansa.

"saboda me"?
"babu kai"

"inan mana, taya kikai kwanciyar"

"ummm hannaye na nakan wurin kwanciyarka sai naji kaman ina rungume da kai ne"

Murmushi yayi yace, "saima kin mirgina kinyi rufda ciki awurin sannan zakiji ki akaina"

Yanda yace tayi wanda sai taji da gaske kaman shike akwance wurin ita ke kwance samansa.

Cike da daddaɗn nishaɗi ta shiga watsa masa tsadaddun kalamai masu rikita tinani wanda ya dinga jinsa tamkar yay flying ya isa gareta.

Haka suka raya wannan daren suna masu jiyar da junansu daɗi da kalamansu har sai da lokacin yin sallarsu ta ƙiyamullail yay yace ta miƙe tayi sallah nan suka rabu tare dama junansu adu'a saduwan alkhairin Allah zuwa safiya.



_SHARE AND COMMENTS_.



*Xerks*✍🏼

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now