Page 42

1.1K 83 5
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



     
          *Story~Written~Edited*
              *_By Mss Xerks_*🌺




         *Devoted to Ummi Aisha*





*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الحيم...





*42*

5:00 na asuba Ammar ya farka ya faɗa bathroom yay wanka tare da ɗoro alwala.

Fitowarsa duban yanda Babyn nasa ke takurewa ya daɗa jan blanket ya ƙara rufe kayarsa sose yanda sanyi bazai raɓar masa ita ba.

Farar jallabiyarsa daya ɗauko ya saka tare da ɗauko praying mat ya shimfiɗa nan ya tada raka'atanil fajr bayan ya idda kuma ya zauna yana lazimi.

Duba da lokaci ya miƙe zuwa kan gadon ya kwantar da kanta bisa ga cinyarsa,
Zaren dake jikin blanket ya cizge ya shiga yi mata yawo dashi a kunne.

Hannu tasa ta kaɓe, kuma yi matan da yayi ta doke wurin da ƙarfi,"umum" ta faɗi idonta rufe.

Miƙa tai tare da silalewa daga saman cinyar tasa ta koma ga pillow.

Ƴar dariya yayi ya kuma mata yawo dashi da idon bacci ta buɗa kaman zatai kuka tana sosa kunnen.

Blanket ta ƙara ja ta rufa har kanta shiko sai dariya yake,
Sanin bazata tashi ba ya yaye blanket ɗin ya ɗagata yana mata miƙa tare da faɗin la'ila ha'illallahu Muhammadu rasulillah kaman yanda ake ma yaro.

"oya open ur eyes is time for subhi prayer"

"uhm uhm uhm nifa ban gama baccin ba"

"sorry idan kika sallah sai ki koma kinga time na tafiya gashi har za'a shiga masallaci"

"tom zanyi amma sai da anjima" ta faɗi tana neman ƙara kwancewa.

"Ohhh Baby ,ki tashi mana plsss bani so sallah n asuba tana wuceki pa"

Badan taso ba ta buɗa idanuwanta tana turo baki ya kamota ta sakko daga kan gadon.

"yauwa ko kefa, dan Allah karki koma sai kinyi sallah bari nai sauri kinga nayi late saina dawo"

"adawo lafiya"

"Allah yasa"

Sai daya ga shigarta bathroom ɗin tukunna ya zari keys ya fita.

Dawowarsa ya tadda harta ta koma barci,
Girgiza kai yayi a zuci yake faɗin _Ooo Baby nah sarkin bacci_.

Praying mat ya kuma shimfiɗawa ya zauna tare da ɗauko qur'ani izu sittin ya buɗa karatunsa da suratul ɓaqra, sai daya karanceta har gari ya waye sannan ya kuma miƙewa ya kawo raka'a biyu ta nafila wadda ma'aiki yace ga duk wanda ya sallaceta ladansa tamkar yay aikin umra ne awata ruwayar kuma ladansa tamkar ya aikaci aikin hajji ne.

Sai 7:30 ya samu ya koma ya kwanta shima dan ƙara matse idonsa.

Bacci mai daɗi ne ya ɗaukesa bayan kwanciyarsa sai 9:30 ya kuma farkawa still Sadia nata sheman baccinta dan ita Allah ya hore mata idon bacci musamman ma tasan Ammar bazai fita office ba.

Saukowa yay ya fita zuwa kitchen ya kunna gas cooker ya ɗora tea ya soya plantain da egg souce cikin ƙanƙanin time ya kammala.

Kan dining ya jere komi kaman yanda yaga Sadia nsa nayi.

Dawowarsa ɗaki ya shiga bathroom yayo wanka da fitowarsa ya shirya cikin jeans blueblack sai Tshirt mai dogon hannu daya sa skyblue.

Har ya gama shiryawa bai tashi Sadia ba duba da yanda yaga barcin na mata daɗi infact ma night duty gareta yau a asibiti dan haka ya ƙyaleta.

HIDAYAH NOOR completed.Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora