Page 45

1.2K 83 4
                                        

🌀🌀🌀🌀🌀
         *HIDAYAH NOOR*
                         🌀🌀🌀🌀🌀




         *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks_*🌺




         *Devoted to Ummi Aisha*



*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



*45*

Koda Hidaya ta koma gida duk da damuwa ta shiga,da Inna ta tambayeta lafiya tace ba komai taci gaba da kukanta.

Shima Ammar koda Baba ya fita ya zauna da ɓacin rai yana tinanin, lalle bazai daina tsanar yarinyar nan baɓhar sai ya gudanar da aikinsa.

           ****

"Sadia dole abinn ya dameni har yau har gobe bana mantawa da irin walaƙanci da cin mutunci da suka mana, kina gani fa ƙarshe da abinda suka saka mana sharrin zina fa ,Ammar da ko kallon mace bai dameshi ba..."

Dafa Adda tayi, "Adda ki manta da komi tinda dai yanzu Allah ya kawo sauyi kuma duniya ta nuna masu kuskurensu"....

"ko zan manta komi bazan manta da sharrin datama Ammar ba dan taɓgama ɓata masa suna a idon duniya, kiga yanzu munaji muna gani muda garin mahaifanmu amma zaman cikinsa ya gagaremu ,kina son kiga ɗanki shima yana son yaga ɗansa amma saboda wannan baƙin sharrin kun kasa gudanar da haka ",

"bana manta komawar da mukayi ana ganinmu aka fara jifanmu da duwatsu manya wai ga mai ɓata ƴaƴan jama'a, zagi kuwa da yana fitowa jiki da ya fito a jikin Ammar ba shiri haka muka kuma tattaro yanamu muka kuma baro Adamawa batare da mun san inda zamu nufa ba ke banda Allah majiƙan bawa ne aida mawuyacin halin da zamu shiga ba kaɗan bane"

"to kin gani idan har Allah na tare da kai bazaka taɓa walaƙanta ba komin tsanain wuya kuwa"

Da kuka Adda tace, "Sadia koda za'a shekara miliyan nan gaba babu wanda zai daina kallon Ammar a matsayin mazinaci, na shiga uku ni Halima Allah ka wanke wannan tabon da yarinyar nan ta masa kasa gaskiya ta bayyana...bazan shiga tsakaninsu ba tinda itace farin cikinsa amma atleast kamin ya aureta ina so ta bayyanawa duniya cewar sharri tai masa bai aikata hakan gareta ba,kuma ina so Ammar ya nuna mata kurenta duk da cewan har yanzu yana sonta"

"bazai yi hakan ba, kin manta abinda hausawa suka ce So hana ganin laifi"

"to ai shikennan ,idan dawowarta rayuwarsa alkhairi ne muna murna....ke kuma Sadia dan Allah kiyi haƙuri kinji da sauyin dazaki samu daga gareshi yanzu"

"ba komi ai Adda"
"Allah yay maki albarka kinji"
"amin"

Hirarsu suka ci gaba dayi nan..

Sai bayan Isha'i Ammar ya shigo gida,
Ganin Sadia bata nan yasan bata dawo daga wurin Adda ba da haka ya kira numban Adda har sau 2 tana katsewa itako tana gani tai banza dashi dan fushi take dashi.

Sai ana uku daya ƙara kiran sannan ta miƙawa Sadia tace gashinn mijinki ne.

"hellow"

"im back" shine abinda yace mata ya kashe wayan.

Miƙewa tai taima Adda sai da safe ta wuce part nasu.

Zaune yake kan kujera ya jinginar da kansa jiki da alamu tinanin wani abu yake.

Kan cinyarsa ta haye tana masa sannu da dawowa.

"yauwa Hayatee nah, shine kikai zamanki acan ko"

HIDAYAH NOOR completed.Où les histoires vivent. Découvrez maintenant