PAGE 11

1.5K 111 0
                                    

🌀🌀🌀🌀
             *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀


           *Story~Written~Edited*
                  *_Mss Xerks_*🌺


          *Devoted to Ummi Aisha*




*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...


UMMU ABDALLAH
Bilkisu Rabi'u Ado
Nasiba Y Gidaɗo
Aisha Usama
UMMU HAIDAR
Maman Samha
Hajiya Bilkisu
Khadeejah
_Kuma ga naku godia nake da nuna kulawa._


*11*

cikin ƙanƙanen lokaci su Hidaya suka fara waec.

Bata da sukuni yanzu dan Schl  nasu ba'a bada expo sai dai mutum ya dage da karatu yayi kuma adua.

Lokaci ɗaya ta rame duk ta faɗa ƙasusuwanta sun ƙara fitowa.
Tana cin abinci tana karatu tana zaman shiru tana tinanin Hamma.

Duk da cewan da tension ɗin makaranta amma tension ɗin soyayyar Hamma yafi yawa.

Sam yanzu bata samun ganinsa dan azimi ya rage saura sati guda gaba ɗaya ya koma kwanan ɗinki.

Yanda zata tashi ta fita da safe bata ganshi ba haka zata dawo da dare ma taci zaman jiransa bai dawo ba saboda shigowarsa fisha ce itama sai da rana kuma time ɗin tana schl.

Watarana da yamma suna zaune su dasu Adda a tsakar gida saiga Ammar yay sallama.

Wata ajiyar zuciya Hidaya tay dan dama shine aranta ,tinani ta yanda zata gansa kawai take,tasan tacema Adda zata fita bazata barta ba.

A gajiye ya shigo ya nemi wuri kusa da Inna ya zauna yana nishi,
Allah sarki ɗiyan albarka Inna tace dashi tana shafa kansa.

"yau kuma kaine da yamman nan"?
"bari Inna,wlh yanzunma kamawa tayi dole ina son ganinku da bazaku ganni ba"

"lalle Allah to ya taimka ya ƙara rufa asiri kuna cin aiki ai ɗinki ba wasa ba"

Hidaya ce tace dashi,Hamma sannu da zuwa an dawo lapia ya aikin"
Kanta aƙasa take maganar.

Shiko dayake kwance kansa akan cinyar Inna yace da ita,"lapia lau ƙanwata ya exams ɗin ana karatu dai ko"

"Alhmdl kuma sosai nake karatu"
"tom sai akuma dagewa,in bahaka ba no u no kayan salla yarinya"

Ɗagowa tayi ta kallesa,ware ido tai tana ƙara kallonsa dan sai taga ya sauya mata kaman bashi ba.

Adda data fito daga bayi tana murmushi tana tailor tailor tinda yau anyi gudun ɗinki dole a waiwayo mu ai.

"kai Adda wlh ba wanda na gudowa kawai tahowa nayi, jibi azumi idan aka shige shi kwatakwata bazaku ganni ba dan na tara ɗinkin jama'a da yawa"

"sai da nace ai karka amsa da yawa saboda azimi amma yanzu haka zakai ta fama ga wahalar azumi gata ɗinki duk wa mutum shi ɗaya"
"karki damu Inna kamin yaje ƙarshe ma na kammala abina saboda haka yasa ai na fara ragewa da wuri"

Wani yaro ne yazo sayan soɓo Adda ta bashi,yana fita tace da Ammar.

"yauwa tinda ma Allah yasa ka dawo ga abincinka nan sai kaci,tin ɗazu nake neman almajiri babu ,ita kuma Hidaya tana karatu bana tasheta ba"

"tab,aƙoshe nake Adda sai dai ku aje kuci zuwa anjima"

Inna ce tace dashi,"kaman ya ka ƙoshi mai kaci"?

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now