PAGE 3

2.3K 138 0
                                    

*HIDAYAH NOOR*
'''Reposting'''

*©️Halima.hz*
*halimahz@Arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*3*
Yahya ya miƙe ya isa shagonsa ya sallami mutanen da suka zo siyayya. Har ya dawo ya zauna kusa da Ammar bai sani ba saboda nisan da yay a cikin tunani. Sai da Yahya ya kai hannu ya dafo kafaɗarsa tunna yay firgigit yana sauke dogon numfashi da cewa,"Ka sallame su?".

Yahya ya kaɗa kansa yana cewa,"Hmm yawan tunani dai ba kyau, haba Ammar kai kenan kullum a haka sai an taɓa zaka dawo daga nisan tunanin da ka tafi, baka gudun hakan ya cutar da kai? Yanzu ina jinka mai ke faruwa? Akwai wata matsala ne?".

Shafa goshi Ammar yayi. "Ka ga mu fara zuwa masallaci naji ana kira idan muka idda zan maka bayanin komai".

"Ok as you said, muje".

Tafe suka jera suna taɓa magana kaɗan kaɗan har suka isa masallaci, dukka suka samu jam'i a wannan gaɓar kam baka taɓa rasa su da rasa jam'i a masallaci. Duk irin customers ɗin da Yahya zai tara ana kiran sallah zai basu uzuri, masu jira su jira wanda basa iyawa su tafi. Bayan sun dawo suka yada zango bisa teburin da suka saba zama idan babu wuta cikin shagon Yahyan.

Ammar ya numfasa idanuwansa a ƙasa, a hankali cikin muryarsa mai kaushi ya kira sunan abokin nasa. "Yahya".

"Na'am Umar Faruq uban ƴan ɗorawa kai damuwa ya akai ne?".

Murmushi Ammar yayi wanda ya bayyanar da malotsin kumatunsa. Ɗan duka ya kaima Yahya wanda shima ke murmushin.

"Ban hanaka faɗin sunan gatsal ba, ko Mama bata faɗarsa don haka kaima ka haƙura da faɗa ka tsaya a iya Ammar ɗin".

Yahya duk da ya ƙosa yaji damuwar abokin nasa ya dafa hannunsa yana cewa,"To yayi mai babban suna, ina jinka dai tukunna kasan bana son ganinka cikin damuwa wallahi".

Ammar ya busar da iska mai ɗumi daga bakinsa. "Wato kasan menene Yahya? Wallahi a matsala na ke sosai, ina ga idan ba zaka manta ba kasan Alhaji Ibrahim Marina ko, wannan mai shagon kayan kwalliyar da ke bakin titi".

"Ƙwarai kuwa ni nasa Alhaji Marina, haka zaka ce shegen Alhaji mara mutunci".

"Kai kuma ai kaji matsalarka, babban mutum ne fa kake ce masa mara mutunci, shiyasa wani lokacin bana son faɗa maka abu baka iya jifan mutane da kalaman daɗi ba".

"A'a to Ammar ƙarya nayi, ai billahillazi mutumin nan ba zan taɓa mantawa da irin rashin mutuncin da ya yanka mana ba".

kallonsa Ammar yayi,"To naji sarkin ƴan ruƙo, bar tuna baya a kalli gaba kawai".

Kai Yahya ya juya gefe yana girgiza kai irin na yanda gayu ke yi wato eyy ka gane yawane Baabaa.

"To ni kana ta jan zance ka faɗa min, ko ƙara cewa yayi kayi masa satar ne wallahi naje har gida na saɓa masa kamanni".

Gyara zama Ammar yayi.

"Jiya bayan na tashi da daddare zan tafi gida sai ya aiko ƙaninsa akan yayi kirana. to da naje sai yake ce mani zai yi tafiya kuma yaga zai shafe watanni kusan biyar zuwa shida, don Allah yana so na zo na zauna masa har ya dawo. To tun a lokacin ma nace masa A'a kai tsaye domin sai naga kamar da wulaƙanci a lamarin, sai kuma nayi zurfin tunani kawai na amince masa. To mun gama.magana da shi don yanzu haka ma ga maƙullin shagon hannuna sai dai babbar matsalar naje yanzu na yiwa Inna bayani tace sam bata yarda ba, ita ba zan ƙara zaman aiki a wurinsa ba".

Yahya juyo da kallonsa gaba ɗaya ga Ammar, yana yi masa kallo na mamaki.

"Lallai Abokina sai yau na tabbatar da cewa baka da zuciya, a nawa tunanin ko wani yace kaje gurin mutumin nan ka yanka masa rashin mutuncin da kare ba zai lasa ba bare kuma shi da kansa ya kira ka. Haba Ammar babu ai ba hauka ba ne da zai sa mutum yay ta wulaƙanta kansa, amsawar nan fa da kayi shine babban cin mutuncin da ka yiwa kanka a wurin Alhaji".

HIDAYAH NOOR completed.Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora