🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*_NA GAISHE DA DUK WANI MASOYIN LITTAFIN HIDAYAH NOOR,INA JIN DAƊIN YANDA KUKE KASANCEWA DANI SON SO DOMIN ALLAH._*😍
*51*
"nayiwa kotu alƙawarin zan faɗi gaskiya,wlh babu ƙarya a cikin maganata ,tabbas Ammar bai aikata laifin da mutane ke zarginsa dashi ba akaina wlh sharri nane bayin kansa bane"
Jin kalaminta Ammar yay saurin buɗa idanunsa dake a rufe cike da mamaki da kuma farinciki ya zubasu akanta.
Itama shi ɗin take kallo tin fara maganarta.
Da murmushin jin daɗi Barrister Muhammad ya kusantota wanda Barrister Al-Mustapha shima dake bayansa ya nufota yana girgiza kai alamu na A'a.
Ganinsu yasa duk ta dakatar dasu da hannu tare da faɗin,
"a'a dan Allah, bani kuma san wasu tambayoyinku gareni na riga na faɗi gaskiya...."
Dakatawa sukai da dubanta ita kuma ta maida kallonta ga Alƙali wanda ke rubutu a takardar dake gabansa.
"Na rantse dan Allah banma kotu ƙarya ba wlh tallahi Ammar bai taɓa nuna irin wannan nufin gareni ba, duk abinda ya faru haɗi nane bada niyyarsa ba, nayi hakan ne dan ya rabu dani da soyayyarsa har abada saboda ni na daina sonsa nayi2 ya rabu dani yaƙi shi yasa na ɓullo masa ta wannan hanyar"
Ta maida idonta ga dandazon mutanen dake kallonta riƙe da haɓa da mamaki tare da wadaran halinta banda Baffa dayay ƙasa da kansa dafe dashi.
"Ku yarda dani dan Allah ku daina masa kallon banzan mutum da kuke masa, ku wanke idanunku daga masa kallon mazinaci fasiƙi, ku daina kallonsa a matsayin wanda zai ɓata rayuwar ƴaƴayenku ko ƴan'uwanku ku kallesa matsayin wanda zai gyara rayuwarsu shine kyakykyawan halinsa ,abinda ya faru sharrin shaiɗanne wanda kuma daga baya nayi dana sani da nadama aikata hakan, Ammar ba mazinaci bane bai taɓa yunƙurin yima wata ƴa fyaɗe ba bare kuma ni wanda yake tsanain so da ƙauna, ruɗin duniya yasa na masa wannan mummunan sharrin amma bai nemi ya mani fyaɗe ba da kaina nasa masa ƙwaya cikin abin shansa"
Nan ta fashe da sabon kuka, " Dan Allah ina roƙon kotu data yanken hukuncin da ya dace dani akan ƙazafin dana masa tabbas na zalince shi na zalinci rayuwarsa,nasa mutane da yawa suna ƙyamarsa"
Alƙali ya katse maganarta da, "Malama Hidaya kin tabbata gaskiya kika faɗawa kotu ba Ammar ne ya tirasasaki ba dan mutane su saki jiki dashi daga baya ya shi kuma ya cigaba da aikata masha'arsa,baki gudun idan kinyi ƙarya ayanzu dan ki wankesa daga baya ya nemi ya haikewa taƙi ƴar matsayinki na mace ya kamata ki ceci rayukan ƴan'uwanki mata"
Dukan kantar datake tsaye ciki tayi da kuka,
"haba nafa rantse maku rantsuwar da in mutum yayita kan ƙarya taɓewa ce gareshi, wlh bai nemi ya mani fyaɗe ba kwatakwata baima san da abinda zai faru ba duk abin shiri nane da kaina na kirasa a waya, na faɗa maku ku yarda dani mana wallahi tallahi billahillazi la'ila ha'illahu babu ƙwarzanan ƙarya a magana ta kotu ta yarda da hakan ko mutane sa daina masa kallon mazinaci su daina ƙyamarsa su dawo da soyayyarsu gareshi in baku yarda ba ku kira Khadija ƙawata da Umma Zakiya su shaidane".
Barisster Al-Mustapha ya katseta da, " ko kinsan kotu zata yanke maki hukunci mai tsanani kuwa dan ƙazafin zina ba ƙaramin abu bane har kike hargowar gaskiya kike faɗa"
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.