Page 69.

1K 86 11
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
          *HIDAYAH NOOR*
                               🌀🌀🌀🌀🌀


          *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks_*🌺


       *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*



بسم الله الرحمن الرحيم...



*69*

Da sauri Rashida ta miƙe ta nufa Umma da ɗagota shima Dr Mujahid ya nufi Ammar da dafasa.

Tare suka haɗa baki wurin faɗin, "ku daina kuka tafa haihu"

Ido Ammar ya ɗago ƙirjinsa na bugawa yace da Dr Mujahid,

"ta haihu tana a wanna hali Dr plss ka faɗa mani ina matata"?

Ido Dr Mujahid ya rufe da futar da iska kamin yace,

"kuyi haƙuri mun faɗar maku da gaba"

"gaskiya kuyi mana afuwa wlh gajiya na aiki ne yasa da kuma tausayawa mai haihuwar" Rashida itama wadda ke gogema Umma hawayenta tai maganar.

Dr Mujahid ya ɗago da Ammar zuwa kan kujeran dake wurin ya zauna sannan yace dasu,

"Alhmdl mun sami nasaran aiki, anciro mata Babynta yanan lafiya itama kuma tana lafiya"

Inaaa ai suka duka suka yo kansa ido a buɗe suna kallonsa bakuna duk a washe saboda daɗi.

"da gaske Dr"? Su duka suka haɗa baki wurin tambayan nasa.

Ɗaga masu kai yay sannan yace, "ƙwarai kuwa yanzu haka ana gyara Babyn da muka samu ne"

"Alhmdl,Alhmdl,Alhmdl,Allah ka ƙarawa Annabi wasila da fadila,Allah na gode maka Allah ka ƙara masu lafiya"

Shine abinda Ammar ke faɗi alokacin daya ɗaga hannu sama yana mai nuna jin daɗinsa ga Allah S.W.A.

Fuskarsa ɗauke da annushuwar data gaza ɗaukewa yace, "Dr mai ta haifa"?

"ai ranka ya daɗe mune,an sami ɗa namiji baka gansa ba tilƙeƙe dashi dole ya bama Mamansa wahala ai"

"to masha'Allahu" su Umma suka haɗa baki wurin faɗa.

"yanzu zan iya shiga na ganta?"
Yaya maganar cike da zumuɗi.

"ehhh to bari mu fito da ita daga ICU ɗin akaita room ɗinta tukunna sai kuje ko"

Riƙe hannun Dr Mujahid yay yanata masa godiya kamin Dr ɗin ya tashi ya koma ICU.

Da ƴar dariya Rashida datazo wucewa tace dashi,

"Ooo Allah nah, su Hamma fa anyi ɗa baki yaƙi rufuwa"

Murmushin dake cike da jin daɗi yay yace da ita,

"nidai in kin shiga ki gaida mani ita kamin ku fito,ga waya ma ki ɗauko mani pix ɗinsu"

"O mai kake ci na baka na falling a down,kai da matarka da ɗiyanka kullum dazaka ta kallonsu"

Fuskarsa ya shafa yace da ita, "to dan Allah ku hanzarta wlh a ƙagauce nake dana ganta,ko kuma na biyoku ciki?"

Dariya Rashida tai tace, "kaman bakai ke kuka ba ɗazun,to bari jirani nan mintina kaɗan zan kawo maka yaronka amma sai ka bani tikwici na"

Murmusawa yay yce ,"kedai jeki dan Allah"

Duk su duka daɗi ya hanasu zama,a tsaitsaye suke suna jiran akawo masu Baby a fito kuma da Sadia su gansu.

HIDAYAH NOOR completed.Where stories live. Discover now