🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*28*
Zaune Ammar yake shi ɗaya a tsakar gidan kan tabarma da wayar Noor hannunsa yana kallo.
Sallamar da Hidaya tayi ne yasasa ɗagowa da murmushi ya amsa mata da,"wa'alaiki salam"
Lanƙwafar da kai tai alama ta gajiya tazo ta zauna daga tabar da yake.
Ɗan kallonta yay kamin ya danna stop ajikin kallon dayake yace da ita.
"yunwa ko gajiya?"
"duka wlh"Ta faɗa tana yatsine fuska tare da kwanciya kan tabarmar.
"kefa wasawasa raguwa ce, bakinci abincin safe ba yanzu sha ɗaya shine zakina kiran yunwa"
"hmmm Hamma kenan wlh wannan teachng ɗin ba ƙaramar wahala bane ai dan bakai bane shiyasa"
Ƴar dariya yay duba da yanda take ta ɓata fuska dan tin rannan take masa mitar ita fa tagaji da wannan yawon teachng ɗin.
"to sannu""yauwa sannu kaima.. Naganka kai ɗaya inasu Inna"?
"sun tafi dubiya"
"shine kuma suka barka mani kai ɗaya a gidan"
"to yanzu ke bagaki kin dawo ba""hmmm ehhh mana.. To amma dai angama abinci ko?"
"ke zaki tashi yanzu ki ɗora tinda kin dawo"
"kayiiii wai daka dawowa ta kuma sai in kama wani ɗora girki banda gajiyar danayi"
"da agidanki nefa yaza kiyi? tashi kawai zakiyi yanzu ki ɗora kamin su dawo.... Kuma daga yau aikin ma ya dawo kanki tinda na lura kin koyi son jiki kalakansa kawai"
Kallonsa tai ta ɗan turo baki tare da miƙewa ta wuce ɗaki.
Sai data ɗan matse idonta na kusan 30mnts sannan ta miƙe ta fito da risho."to Hamma babu fa kayan miya"
Aljihunsa ya laluba ya zaro ɗari ya bata yace ta fita ta sayo amma tai sauri.
Mayafinta ta zira ta fita bata jima ba ta dawo kuma ta sami kayan miyan a arha dan haka ta rabasu biyu yanda zasuyi anfani dasu har washe gari.
Ruwa ta zuba a tukunyar tayi jajjage ta afa da ɗan mai yana tafasowa ta zuba taliya inda ta tada jallof ɗin taliya cikin mintina kaɗan ta sauke.
Tana saukewa ta ɗauko kwano ta zuba nasu Inna ciki sannan ta ɗauko plates ta zuba na Hamma da nata aciki sai wanda suke bama almajirin dake masu suyar awara a ɗan ƙaramin kwano.
Ajema Hamma nasa tayi danshi ce yay sai yayi sallah tukunna,kamin ya idda ko tini nata ya jima da narkewa ma aciki saboda wata muguwar yunwa data ke ji.
Shima yana idar da sallar ya jawo plate ɗin bayan ya wanko hannunsa yay bismilla ya fara ci.
Hidaya nata masa hira da labarin ƴan student ɗin data keso wayarta tai ƙara.
Lura da baƙuwar numba ne jiki ba suna yasa sai datayi ringinga har sau biyu tukunna ta ɗauka.
Karawarta a kunne tai sallama daga ciki aka amsa mata tare da faɗin,"kiyi haƙuri Hidaya na kiraki da sabon numba ko Rashida ce"
KAMU SEDANG MEMBACA
HIDAYAH NOOR completed.
Fiksi SejarahHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.