🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
Its ur page Jamila M ladan adu'anki gareni na sani nishaɗi ubangiji ya amsa mana baki ɗaya.
*63*
Sabuwar shaƙuwa ta sake kasancewa a tsakaninsu a saboda irin kulawar da suke bama juna wanda aduk sanda Hidaya bataji muryarsa ba takan jita ne kamar mara lafiya.
Lokacin daya sanar da Hidaya cewan zasu tafi adamawa dan sada zumunci harda ƙwallarta, saboda rashin ganinsa dazatayi wai har tsawon watanni uku sai dai kawai taji muryarsa.
Sai daya lallasheta yace ai kaman yau ne kumama shima idan yaji bazai jure rashin ganinta ba sai ya dawo,
Da wannan ta ɗanji sanyi aranta duk data san ba lalle me yiwuwa bane dawowar tasa tinda tafiyar harda matarsa.
Cike da kewansa dazatai sukai sallama ya wuce gida.
Ranar Wednesday suka miƙe su duka zuwa Adamawa babu wanda aka bari a gidan sai masu aiki Gwaggo Amina ma ta wuce garinsu.
Dake jirgi suka bi ƙarfe 10:30 suka isa adamawa anan suka rabu dasu Adda sukai gidansu suma sukayi nasu gidan da suke sauka idan sunzo garin.
Ranar Sadia agida ta yini wurin Umma da Abba, zoka gata dama itace ƴar fari bare kuma yanzu datake da ciki abinda suke ta muradin samu wato jikansu.
Motsinta kaɗan Abba yace mene ko mi take so,cinyar Umma ko akai ta yini dan har Ammar yazo tana maƙale jikinta.
Dayace zasu tafi Abba yace toko zasu kwana anan tinda in sun tafi basu da mai aiki.
Tab Ammar yce aransa _in kwana anan ahanani jin daɗi umumum gwara mun tafiyr mu gidanmu._
"a'a Abban Sadia barsu su tafi in yaso da gobe a nema masu mai aiki kaminsu koma"
"to shikenan ,saiku tashi dan naga lokaci yaja ga gari ma ba kyau lokacin siyasar nan yayi"
Da to suka amsa suka miƙe suna masu jin daɗi da godiyar irin adu'ar da iyayen ke masu.
Da suka koma gida nan Ammar yasata gaba yana ta tsokanarta ita kuma na cikwikwiye shi.
"hhhh wayaga tulu,nifa harna ƙaguma cikinn ya daɗa fitowa naga yanda zaki koma"
"dama tinda ba jikinka yake ba, ai da ana sama wani idanba jikinka zan maida shi ba"
"wa" ya faɗi da zaro ido,
Kansa saman cinyarta yana shafa ɗan ƙaramin cikin daya fara fitowa yace,
"kinsan Allah Hayatee da ace akan iya sama miji ciki wlh my soul ba iyaka shi zan ɗaukar maki har haihuwan ma zan amsar maki duk wannan wuyan bazan taɓa bari kisha ta ba"
Idonsa daya lumshe ya buɗa ya watsa su akanta wanda itama shi ɗin take kallo tana mai fitar da ƙawataccen murmushi.
Sai daya hura mata iska tukunna ta ɗan lumshe nan haƙoranta suka bayyana.
Ƴar dariya yay ya miƙe da faɗin, "Hayatee kinga"
Kallonsa tai yanda ya wani sa hannu baya yana neman miƙewa da ƙƴar kaman mai tsohon ciki.

DU LIEST GERADE
HIDAYAH NOOR completed.
Historische RomaneHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.