🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺
*Devoted to Ummi Aisha**_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*_Mutuniyar kirki uwar alkhairi mai ruwan comment Halima Ummu Leena wa Ayush here is your page ki yanda kike so dashi Allah ubangiji ya raya maki zuri'ah yasasu bisa tafarki na gaskiya._*
*55*
Sanye yake da apron yana ta saurin kammala girki dan baya son Sadia ta farka bai gama ba.
Doya ce ya soyata da ƙwai sai eggroll shima da yay shi da zafinsa ya haɗa juice da kunun tsamiya daya dama gefe guda kuma ferfesun kayan ciki ne dasuka sha alayahu samansa sai ƙamshi suke kaman ba girkin namiji ba.
Daya kammala tas ya kawo saman dining ya jeresu akai gurin yay kyau gwanin ban sha'awa.
Remote ya ɗauka ya kunna TV inda yakai saudi 2 da suke saka karatun qur'ani sannan ya wuce zuwa ɗaki.
yana shiga ya tadda Sadia zaune kan gadon wadda tashinta kenan.
Da sauri yayo wurinta ya zauna kusa da ita tare da tayata yeye blanket ɗin.
"my Soul kin tashi" ya faɗi dafe da hannunta.
Kallonsa tayi da murmushi ta ɗaga masa kai.
"Na tashi heart beat"
"to ya jikin naki" ya tambaya yana shafa wuyanta.
Jingina kanta tayi da kafaɗarsa tace, "da sauƙi sose"
"sure babu inda yake maki ciwo yanzu"
"100% sure"
"to Allah ya ƙara maki lafiya yasa ciwon ya tafi kenan karya kuma dawowa" ya faɗi a shagwaɓance fuskarsa da damuwa.
da amin ta amsa masa tana kallonsa,fuskarsa harta ɗan faɗa tsabar firgicin da ciwonta yasa shi na 2dayz.
Kallon datake masa yasasa hure mata ido haɗe da ɗaga mata gira.
Lumshe idon tayi ta buɗa ,
"heart beat gani nayi ka rame""hmmm ba dole ba Hayatee nah,nifa ko kaɗan bani ƙaunar abinda zai taɓa mani lafiyarki bare har takai ga ya kwantar mani dake,nida yay shawara dani ai ni zai kama bake ba"
"kai Mahbub to ainima ban son abinda zai taɓa mani kai, yanzu ma dai ba gashi naji sauƙi sai ka maida ƙibarka ko, dan ban son rama atare dakai"
"mudai mayar tare kema aikin rame dama ke aba ba aba kaman a hure ki faɗi"
Dariya tai da juyar masa da ido, "kai Mahbub duk wannan ƙibar tawa aima dai duk da haka na fika"
"kika fi wanda kika fi dai, yanzu dai tashi muje ki wanka kizo kici abinci kinga 2dayz wannan shamulakin cikin naki baiga wani abinci ba"
A shagwaɓance tace dashi, " ni sai da kazo muyi tare"
Da azamarsa ko ya miƙe yana ai dama haka nike so ni tashi muje mu cuɗe juna.
Tare suka shiga wanka inda suka ɗau awa sannan suka fito kowannensu cike da nishaɗi.
Da kanta ta shiryashi cikin ƙananun kaya jeans blue black da t-shirt nasa mai ƙaramin hannu white sannan itama ta shirya cikin english wears ɗinta masu kyau pink and blue.
Idanunsa ya buɗe ya ƙura mata ido yana kallon kyan da tayi.
Da dariya ta zaune kan cinyarsa ta saƙala hannunta ga wuyansa."zaka ƙara zuƙeni fa"
"Allah heart desire ji nike kaman na haɗiyeki tsabagen so da ƙaunar da nike maki,kina rikita ni fa da yawa"
Ƴar dariya tayi taja gemunsa tare da bashi kiss, " Allah ya barni dakai final choice"
Jinsa wani iri ya sauketa da kama hannunta.
"kinga muje kici abinci kizo ki shayar dani madarar 2dayz da baki bani ba dan a yunwace nake da ita""aikam dai ba yau ba"
Tsayawa yay da tafiyar tasa da dariya ta kama hannunsa,
"da wasa nike,mai abu da abinsa har sai an masa iko indai nice ai gaka gani sai yanda kaso"Koda suka fito parlo basu zauna a dining ɗin ba suka kwaso abincin zuwa ƙasa danshi Ammar yafi son yajishi zaune ƙasa indai zaici abinci.
Yana bata tana bashi haka har suka kammala cin abinci cikin so da ƙaunar juna.
parlon sama suka koma inda suka yada zangon soyayyar kwana biyu da basu sha ba sai ta jinya wanda basu suka ƙyale juna ba sai 4.Bayan yaje masallaci ya dawo ya tadda ta zaune tana danna waya.
"sannu da dawowa" tace dashi da tasowa tarbosa.
"yau sannu hubbi nah" ya faɗi da riƙe hannunta suka nufa kujera suka zauna.
Saman cinyarsa ta kwantar da kanta tana masa hira mai daɗi hakan ya tabbatar masa data samu lafiya sose ya kuma ji daɗi da hakan,wayarsa datai ƙara ne ya juya ya kalla sunan dake kan scrn ɗin ganin sunan Abban Hydar ya share bai ɗaga ba.
"miyasa bazaka ɗaga ba"
"Alhji ne nasan cewa zaiyi naje ni kuma ban san zuwa"
"to saboda"
"saboda ina tare dake"" Mahbub Alhji na kira kaƙi ɗagawa plss ka bar wannan wasan mana" ta miƙa hannu zata ɗau wayar ya riƙa hannun.
"Baby karki ɗaga dan Allah ,nifa bani son fita na ƙyaleki idan aikin ne ya bawa Hydar"
"to amma fa kana jin kiran yay yawa ka daure ka ɗaga kaji ko lafiya"
Ba dan yaso ba ya ɗaga Alhji yace yazo m yana son ganinsa yanzunnan.
Yana ta ɗan ƙaramin tsoki ya ɗau key ya fita bayan daya kira Gwaggo Amina yace ta kula masa da Rayuwarsa dan Allah ko ƙuda karta bari ya taɓata yanzun zai dawo ba jimawa.
Da adawo lapia suka rakashi ya amsa masu da Allah yasa.
****
Kwana biyar kenan da zuwan Jamil wurin Hidaya.Suna kitchen ita da Inna suna kwaɓin alkubus yaro ya shigo gidan da sallama bayan amsa masa da sukayi yace wai ana sallama da Hidaya a waje.
"inji wa" ta tambyi yaron tana harararsa.
"wanine a waje bai faɗa mani sunansa ba"
"kaje kace bata nan" ta faɗa yayin data juya zata koma kitchen.
Inna ce ta dakatar da yaron da cewan, "kai jekace tana zuwa kaji"
Da to yaron ya amsa ya fita inda Inna ta juyo kan Hidaya da faɗa tace tai maza ta shirya taje bata son shashanci in kuma ba hakan ba zata saɓa mata.
Tana zumɓura baki tai ɗaki ta yafo mayafinta tazo fita Mukhtar yasa mata kuka ta ɗauke shi suka fita.
Tana buɗa ƙofa ta hangi motar Jamil aiko taja dogon tsaki ta juya ciki shi kuma ya ƙaraso da sauri yana kiran sunansa tai banza dasshi.
Ɗaki ta shiga ta ɗauko ledar daya kawo mata randa yazo ta fito .
Ranta ɓace ta miƙa masa ledar hannunta inda ta kau da fuskarta gefe."ga kayanka bana so ,kuma dan Allah na roƙeka daga yau karka kuma zuwa gidann"
*MANAGE PLSSS ,UZURI*
_SHARE AND COMMENTS._
*Xerks*✍🏼
CZYTASZ
HIDAYAH NOOR completed.
HistoryczneHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.