Page 22

1.6K 91 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀
            *HIDAYAH NOOR*
                        🌀🌀🌀🌀🌀



         *Story~Written~Edited*
             *_By Mss Xerks🌺_*


         *Devoted to Ummi Aisha*


*_2018/2019_*


بسم الله الرحمن الرحيم...



*22*

Da safiyar litinin tinda wuri Ammar da Yahya suka wuce bank ciro kuɗi kaman yanda ya alƙarwanta yau zai kai kuɗin aure.

Gaba ɗaya kuɗin accnt ɗin nasa 30k ne,dubu ashirin ya ware ya cira ya bar goma aciki.

Da suka dawo gidansu Yahya suka wuce wurin Babansa.Kawu na zaune a ɗakinsa suka shiga da sallama suka zauna gefe dashi.

Bayan da suka gaidashi cikin ladabi Ammar ya fiddo da kuɗin daga aljihunsa ya miƙama Kawu.

Hannu Kawu yasa ya amsa inda ya shiga ƙirga kuɗin naira dubu ashirin ne cas.

Zama Kawu ya gyara yay gyaran murya tare da kallon Ammar yace dashi.
"masha'allahu ɗana kayi ƙoƙari gaskiya.yanzu iyaka kuɗin aure ne koko harda nasa rana?"

Cike da ladabi Ammar ya amsa masa da,"ehhh kawu da duka biyun na haɗa ai yayi ko"

"ahh yayi sose ma,dabara ce wannan babba sai dai kuma idan kana ganin zakai irin ta abokin naka kai kuɗin aure daban daga baya kakai akwatun sa rana ko...amma ni inaga hakan dakai zaifi maka sauƙi koya kace"

Da rissinawa Ammar yace" yanda kace Kawu"
"to shikenan ka barshi hakan Allah sa masu albarka ya tabbatar mana kuma da alkhairinsa a wannan abu da za'ai "

Da amin suka amsa dukansu,da ƴar shawara Kawu ya bisu da kuma nasihohi kaman yanda ya saba masu akoda yaushe in yana tare dasu.

Kamin azahar Kawu ya shirya ya tafi gidan malm Shuai'bu,bayan gaisawarsu ya ciro kuɗin auren Hidaya ya damƙa masa inda suka tsaida rana wata uku kaman yanda Inna tace a saka.

Bayan sallamarsu shima Malm Shuai'bu bai zauna ba ya miƙe ya tafi gidan Inna.
Da gaisawarsu da ita ya miƙa kuɗin auren ɗiyayarta da aka nema ,nan yake shaida mata duk yanda sunkayi har saka ranar anyi .

Godia tai masa sosai harda ƴar ƙwallarta,kuka sosai Inna tai data dawo cikin gida wanda ta misaltashi da abu biyu farinciki da kuma baƙin ciki.

Adda ma kanta sai datai kuka yau sosai.mahaifansu kawai suka faɗo mata da ace suna raye Allah kawai yasan irin murnar daza suyi yanda suke matuƙar son Ammar.

Juna suka rungume Inna na lallashin Adda,"Halima nice da kuka,mijina ya gudu ya barni yau tsawon shekaru 9kenan bai taɓa tinanin ya waiwaye mu ko badanni ba dan ɗiyarsa daya bari...yanzu waya sani ma ko ya mutu amma idan har yana raye har yanzu yay mana haka bako zan taɓa yafe masa ba.."

Da Rana Adda taje gidan Maman Hauwa suka taho tare dan ganin kaya.koda suka zo da gadon ƙarfen da kwabar gabaɗaya a dubu sha huɗu ta sayesu suma dan su Inna ne tana ganin yanayin da suke yasa tai masu sayan mutunci.

Ala amfana Inna tace tai mata godia sosai.da Maman Hauwa zata tafi Adda kecewa da Inna mai zai hana kawai abar mata kuɗin a hannunta ta ijjesu tinda wurinta zasu saya kayan ɗaki,yafi ace sun amsa kuma suzo sa iya taɓawa.

Ehh Maman Hauwa tace gaskiya kinyi tinani ko,kinga koda ansamu kaya a iya ajewa tinda nasan an ragen wasu kuɗin.

Inna ma to tace dan tana  amfani da shawaran Adda sose, hakan sukai suka barma Maman Hauwa duka kuɗin ahankali kuma zasu na kawo mata ɗan abinda aka samu .

HIDAYAH NOOR completed.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora