Epilogue (Final- Chapter)

1K 81 10
                                    

Ranar suna, diyar Samha da Sabah taci suna Juwairiyya don tunda Khadie ta kwalafa rai akan sunan har Sabah ta yiwa magana shima yaji sunan ya kwanta masa yace babu matsala idan macece za'a saka mata.

Khadie na jin an sakawa yarinyar suna Juwairiyya tafi kowa murna, taji dadi sosai. Aka sha suna lafiya. A lokacin Nehal tayi wayo sosai har ta soma takawa, kyakyawa da ita itama don tana shan gyara daga wajen Anty Fanneh kamar yanda takewa Samha lokacin tana karama. Nehal bata yarda da mutane sai yan gidansu. Ko Samha ma bata yarda ta dauketa amman tana barin Sabah ya dauketa ko don yana bata sweet tana sha. Anytime ta ganshi sai taje ta kwanta a jikinsa wani sa'in har tayi bacci a kafansa. Sosai Sabah yake ji da kanwar nasa.

Sai da Samha tayi kusan wata biyu tukuna ta koma gidanta da ita da kyakyawar di'yarta suka cigaba da rayuwarsu cike da tsantsar so da kaunar juna. Juwairiyya rai da rai tana hannun Sabah, bacci ne kawai yake rabasu, yana dawowa daga aiki zai dauketa suyita wasa, har tayi bacci a hannunsa. Ji yake Samha ta gama masa komai data bashi wanan fine baby girl din. Juwairiyya a lokacin tana wata bakwai har ta fara zama abunta tana gane mutane. Duk inda suka shiga idanun mutane na kanta abun har yazo ya fara ba Samha tsoro, Anty fanneh tace ta di'nga mata toffin adduo'i. Yauma kamar every weekend sun fita shakatawa. Jara mall dake sabon ikeja terminal suk nufa suna da'an grocery shopping, Sabah yana rike da Juwairiyya a hanunsa na dama, da'yan kuma na tura trolley. Samha tana biye dashi picking abubuwan da suke bukata a gida.

Kiran sunanta da akeyi ne yasa Samha ta da'go hade da juyowa.wani irin shock tayi da idanunta suka sauka kan mai kiran nata. Madina ta gani tana kokarin karasowa inda suke cikin sauri. "Heartbeat kalla Madina ce fa ke kokarin karasowa inda muke".

Juyowa shima Sabah yayi idanunsa suka sauka kan Madina. Wani irin farin ciki ne ya lulube Madina tana karasowa ta rungume Samha tsam a jikinta tana fa'din "wayyo Antyna ashe inada rabon sake ganinki! Kwana dayawa!"

Itama Samha rungumeta tayi cike da farin ciki tana fa'din "Madina yaushe a gari. Yaushe kika shigo kasar namu" ta tambayeta tana kare mata kallo taga ta kara yin kyau tayi fresh sosai abunta".

"Wlh cikin satin nan. Sabah ina yini". Ta juyo tana gaishe da Sabah. Sabah cike da walwala ya ansa mata gaisuwar nata shima yayi farin cikin ganinta. Sai a lokacin idanunta suka sauka kan Kyakyawar yarinyar dake hannun Sabah. Wani irin shock ne taji ya ziyarce ta mika hannu ta karbi juwairiya tana fad'in masha Allah. Instantly taji yarinyar ta shiga ranta. "Samha babynku ce wanan? Na samu labari ai kunyi aure. Shinoh ke fa'damun last time da mukayi waya dashi" ta fada tana karewa Juwairiyya kallo cike da sha'wa, a ranta tana fa'din da itace yanzu da mallakin wanan kyakyawar babyn.sosai suka zurfafa da hiran yaushe gamo. Madina take sanar dasu harta gama masters di'nta gashi ta dawo gida. Yanzu aure ne kawai ya rage mata. Samha tace mata karta damu komai lokacine da sannu itama Allah zai fito mata da nata. Anan sukayi Sallama, Madina ta karba number wayar Samha tace insha Allah zata kawo musu ziyara har gida.

Juwariyya na cika shekara da'ya da yan' watani Sabah ya soma yiwa Samha magana akan ya kamata suje lebanon suje suga mahaifiyarsa don tunda taji yayi aure har matarsa ta haihu ta matsu kwarai akan tana son ganinsu. Ko jiya da sukayi waya da Sabah sai data dauko masa batun.

Sabah dayaje gida ya sanar da Abba batun son tafiyarsa Lebanon, Abbah ya goya bayan haka don tun ba yau ba yake ta son Sabah yaje ya ganta. Cikin da'an kankanin lokaci Sabah yasa akayi musu processing visa na zuwa kasar. Samha na cike da fargaba don bata san me zata je ta tarar ba acan.

A ranar da zasu bar kasar, su Anty Fanneh har airport suka raka su, Nehal harda kukanta wai sai ta bisu, da kyar Sabah ya samu ya lalabata tayi shiru hade da mata alkawarin sweets da biscuits iri iri, tukuna ta hakura. Jirginsu na landing a kasar Lebanon, Sabah ya kira mahaifiyarsu ya sanar da ita sun iso. Musamman ta tura driver yazo yayi picking dinsu daga airport. Samha ta shiga bin ko ina da kallo tana jin wani irin sensation na daban don kasar ba karamin burgeta yayi ba. Everything is so different there harta mutanen kasan duk larabawa ne, tun da sukayi landing a airport bata kuma ganin wani bakin fata ba.

Wani hadadden gida driver din ya kaisu yayi parking sa'anan suka fito cikin harabar gidan. Tun da'ga bakin kofar shiga parlourn gidan suka hango wata kyakyawar mace balarabiya fara sol da ita ta tunkarasu tana murmushi, idanunta kyam akan Sabah tazo ta rungumeshi tsam a jikinta tana jin wani irin farin ciki na ratsata duk illahirin jikinta. Yaushe rabon dataga dan'nata tun yana karami ta baro Nigeria sai yau. A hankali ta da'go tana kallon kyakyawar fuskarsa idanunta suka ciko da kwala tsabar farin cikin ganinsa ta soma mishi magana cikin harshen larabci. Shima Sabah wani irin yanayi ya tsinci kanshi ganin mahaifiyarshi after all these years.A hankali ya soma tuno da abubuwa da dama da suka faru a baya da kuma rashin kusancin shi da ita. Yayi kewanta har bai san yanda zai misalta ba.

A hankali matar ta dawo da dubanta ga Samha dake tsaye da Juwairiya a hanunta tana kallonsu cike da tausayi. Cikin harshen larabci ta juyo tana tambayar Sabah ko matarshi ce da yar'shi yace mata eh. Cikin sauri tazo ta rungume Samha da Juwariya tana musu barka da zuwa cikin hausanta daya saje da accent din Arabic. Da kyar Samha take fahintar abunda take fadi. Sabah yace ma mahaifiyarshi tayi mata turanci kawai tana ji. Dariya tayi sa'anan ta karbi juwairiyya daga hannun Samha tana kare mata kallo tana ji tamkar ita ta haifeta.

Hannunta rike dana Samha tayi musu bissimillah suka shiga ta daga ciki, ko ina fess sai yan aikin da suketa faman zarya cikin gidan. Suka zo suka soma jera musu abubuwa a gaba. Bafi 20 mins ba wani mutum shima balarabe ya sauko kasa yazo suka soma gaisawa. Tayi introducing inshi a matsayin mijinta, suna da da'guda da'ya amma baya nan yana boarding school sai anyi hutu zai dawo. Mutumin bashida matsala yayi musu tarba mai kyau. Dukda dai Samha bata jin abunda suke fa'di taji dadin yanda suka karbeta hannu bibiyu. Da yamma ne Jabbar ya samu ya shigo gida saboda tun safe yana school yana fama da lectures, tunda yaji labarin zuwansu yaketa Allah Allah ya dawo gida yazo ya gansu.

Murna a cikinsa kamar meye, suma sosai sukayi murnan ganinsa. Satin su Sabah uku a lebanon sa'anan suka dawo Nigeria saboda aikinsa. Mahaifiyarsa ji tayi kamar karsu tafi don cikin dan kankanin lokaci suna saba sosai har ta soma koyawa Juwairiya larabci itama tana da'an mayar mata da baby talks dinta. Sabah yayi mata alkawari cewa insha Allah idan an samu hutu zasu kuma zuwa.

A kwana a tashi juwairiya har ta kai shekara biyu, Nehal kuma na neman shekararta na uku, aka sasu a school suna zuwa. Juwairiyya ta kasance shiru shiru batada hayaniya da wuya ka ganta tana kuka ko wani abu sabanin Nehal uwar rigima abu kadan ke sata kuka. Juwairiyya na shekara kusan uku akayi mata kani, Samha ta sake haifo da' namiji yaci sunan Abba Mu'azzam amma sai ake kiranshi da Ayman shima kyakyawa dashi babu inda ya baro iyayensa a fanin kyau.

Bangaren Khadie da Amjad kuwa anata faman shirye shiryen biki amma a kano zasu zauna saboda can akayi posting Amjad wajen aikin custom daya samu. Amina ce kadai Allah bai fito mata ba har yanzu. Zack da Aliyah ma suma ana gab da shirye shiryen nasu. Lokaci nayi aka sha biki kuwa don babu wanda su Samha basuyi attending ba don ansha gwagwamayar rayuwa tare.

Musamman suka ha'da get together babu wanda bai halarta ba a cikinsu. Daga, Sabah, Samha, Zack, Abba, shinoh, Madina, Aliyah, khadie, Amjad, Amina. Duk sun halarta. A get together di'ine khadie ta soma tuna baya tana bada labarin how each and everyone of them met.. Tun daga crushing akan Amjad da Samha ta somayi, da fitinan Sabah ya rikitata har tazo tayi switching feelings zuwa gareshi da competition da suka dingayi da Aliyah akansa, aka dinga dariya. It was fun those days. Rayuwa kenan, you meet new people and before you know it they become such an important aspect in your life. A haka taron ya watse suka koma gida. Aka cigaba da tafiyar da rayuwa, Samha da mijinta suna zaune lafiya babu mai jin kansu, ga kyawawan ya'yan da Allah ya basu kullum kara gode masa sukeyi suna zaune lafiya cike da matsanancin son junansu.

The end.

ALHAMDULILAH, da wanan masu karatu na kawo muku karshen ZABIN SAMHA, my first completed hausa novel. kuma ina kara godewa Allah daya bani ikon kammalawa lafiya. To all ZABIN SAMHA FANS, su Anty Nabila, Maryam, sha'wa, zainab thanks for all the comments❤️ We've come such a long way Allah barmu tare. you guys are great.

Anticipate my other books that will be coming soon🔥

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now