Chapter twenty

660 71 0
                                    

Shiru tayi ta cigaba da kallonsa. Abubuwa da dama suna mata yawo a ka game dashi. Shima kallonta yake yi, kyawawar idanunsa da suka dan shige ciki ciki ya zube su kyam a kanta.

Shiru ne ya ziyarce su, kowanensu da abunda ke masa yawo a ka. Ba abunda kakeji zai zubar ruwar saman da aketa faman zabgawa da karfi.

Khadie ce ta bude baki zatayi magana, sai yayi daidai da lokacin da shima Amjad ya bude baki zaiyi magana. Tare suka katse juna sai kuma sukayi shiru kowa na jiran dan'uwansa ya farayin magana. Amjad ya dubeta yace "ban katseki ba kiyi maganarki ina jinki".

Khadie ta girgiza masa kai tace " ina jinka dai, ka fara magana".

Shiru yayi na dan lokaci yana nazari daga bisani ya bude baki ya soma fadin " Bazan boye miki ba khadija, a yanzu haka bansan irin maganar da zan furta miki ba wanda bazai bata miki rai ba. ina tsoron na fadi wata magana kuma kiji babu dadi".

"Karka damu Amjad. Ni kaina idan na zauna ina tunani abun yana daure mun kai. Garin ya nazo na fada tarkon son saurayin kawata? Meyasa zan aikata abu irin haka?. Nasan hakan bai dace ba amma Amjad I can't help it, kawai na wayi gari na tsinci kaina da matsanancin sonka, kuma na kasa dainawa. Sonka kullum dada karuwa yake cikin zuciyata."

Amjad shiru yayi yana sauraronta bai ce komai ba. Tana tsaka da maganganunta yaga ta yanke maganar ta soma jero attishawa, alamun sanyi ya soma shiganta.

Amjad ya rasa abunyi gashi sai faman jerosu takeyi, ai kam bai san sanda yasa hanu ya kamo lalausar hanunta cikin nashi ba ya soma shafawa a hankali yana fadin "naga alama sanyi na son ya shige ki, ki dinga goga hanunki kamar haka kina manawa a fuskarki zaki danji dumi,". Ya fada yana manna tafin hanunsa bisa fuskarsa. Kallo ta bishi dashi daga bisani itama ta soma kwaikwaiyon abunda yakeyi. Haka ta dinga goga tafin hanunta tana manawa a fuskarta har ta samu ta soma dan jin dumi.

Ba'ajima ba masu shagunan rumfar da suka fake suka zo suka ce zasu bude shagonsu su dauki abu. Amjad ya dubeta yace " gashi wanan ruwan sai dadda karuwa takeyi. Koh zamu karasa inda nayi parking motata, babu nisa daga nan."

Khadie kai kawai ta gyada masa. Amjad ya cire bakar jacket din dake sanye a jikinsa, ya rage daga shi sai blue tshirt. Jacket din ya daga yayi musu rumfa dashi yace da ita bisimillah. Haka suka shiga cikin ruwan, amjad na rike da jacket yana kokarin karesu daga ruwan, khadie ce ma yafi karewa da jacket din saboda kafun suyi nisa duk yabi ya jike da ruwa. Cikin sauri suka karasa inda yayi parking motarsa ya bude suka shiga ciki. Nan da nan ya tayar da motar ya kunna heat warmer na cikin motar, cikin yan mintuna motar ta fara daukan dumi, kayan jikinsa da suka jike suka soma bushewa. Ajiyar zuciya ya sake, ya lumshe idanunsa. Shuru ne ya dan ziyarce su Khadie ta kura mishi ido sai faman binshi da kallo takeyi. Bayan dan wani lokaci khadie ta bude baki ta kira sunanshi a hankali "Amjad....."

Bude idanunsa yayi a hankali ya juyo zube su cikin nata,"na'am....".

Shiru tayi daga bisani ta cigaba da fadin "Amjad nasan wanan abun danake shirin fada maka abu mai kamar wuya ce. Nasan har yanzu tunanin samha na nan fresh a cikin ranka, baka manta da ita ba. Amma baka tunanin nida kai zamu iya zama wani abu nan gaba?"

Amjad yayi shiru yana jinta bai ce da ita komai ba. Bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin " in har bazaka damu ba Amjad, inaso na nema wata alfarma wurin ka".

dagowa yayi yana dubanta don jin wanan alfarma da take kokarin nema wajensa.
" kaga dai ruwan sama akeyi babu mutane dayawa da suke wucewa. Inaso nida kai musa ido, duk wanda zai sake zuwa ya wuce rike da jar lema toh zakayi mun alkawari neman mazauni koda kadan ne cikin zuciyarka."

Amjad ya dan nesa jin kalamanta daga bisani ya bude baki ya soma fadin "Anya kuwa, kina tunanin hakan zai yu'?".

" please amjad. This is my only chance, dan Allah ka bani wanar damar, kaji".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now