Chapter fifty-two

435 58 2
                                    

Shiru Madina tayi daga bisani ta cigaba da fadin " i was wrong, bai kamata na fadawa Sabah wanan maganar na cewa muyi pretending muna soyayya saboda kar iyayyen mu su gane ba."

Shiru Samha tayi tana sauraronta don itama jikinta ne yayi mugun sanyi data tuno cewa suma they are hiding their relationship from their parents .

"Big sis...Anty na.." Madina ta soma kiran Samha, amma ina Samha ta rigada tayi zurfi cikin tunani. Sai da Madina ta dan tabota tukuna tayi firgiti ta dawo hayacinta.

Madina ta dubeta tace "Big sis lafiya kuwa? Inata magana naji kinyi shiru"

Murmushin yake samha ta sake sa'anan tace "lafiya wlh. I'm okay. I just zoned out ne kawai".

Madina tace "okay, daman inaso na fada miki cewa inaso dani dake da Sabah mu zama good friends, da fatan dai babu matsala zaku karbe ni hannu bibiyu?"

Gaban Samha ne ya fadi dataji Madina tace tanason ta kulla abota da Sabah, kar dai kirkinta yanaso yajaza mata? Murmushin karfin hali ta sake kirkirowa ta sakar mata sa'anan tace "babu matsala Madina. You're always welcome".

Itama Madina murmushin ta sakar mata tace " nagode sosai Big sis"

Samha tace mata babu komai, sallama sukayi daga bisani Samha ta karasa department dinsu cike da sanyin jiki.

Tana shiga cikin class, bata tadda su khady ba, ciro wayarta tayi daga cikin jaka ta soma nemansu a layi.

Bugu daya khady ta daga, Nan suka sanar da ita cewa suna cafetaria.
Cikin yan mintuna kadan sai gata nan a cafetaria din.

Karasawa tayi inda suke zaune, itama ta samu wuri ta zauna sa'anan ta zabga wani uban tagumi.

Khady da Amina suka kalli junansu sa'anan suka dawo da dubansu gareta suka soma tuhumarta akan abunda yake faruwa.

Ajiyar zuciya ta sake sa'anan ta zayane musu duk abunda ya faru.

Cike da mamaki suke binta da kallo, Samha ta karasa maganar da " ni wallahi gabadaya ma na rasa yanda zanyi, I thought this arranged marriage crises is over sai gashi madina ta sawo kai, ga kuma yar'uwarsa shafa da duk tabi ta tadda hankalin kowa akansa. I think I've meddled too much. Ni maganar ma da Madina da fada mun dazu ne yake damuna, there's something wrong about what she said, na kasa fahimta".

Khady ce tayi saurin katseta tana fadin " ai kece Samha, atimes you do too much. Gashi kinje kinata yaba Sabah a gabanta ba dole taji ya burgeta tanaso ta hada abota dashi ba"

Samha ta mararaice fuska tace " toh ya zanyi? Kema kinsan banason ana misunderstanding dinsa, shiyasa nayi mata wanan bayanin, kuma naga duk tabi ta damu, harda da'an kukanta fa".

"Toh ai gashinan, keda ajayi work dinki. Gashi kina neman ki kwan ciki". Khady ta karasa maganar tana hararanta.

Amina ce dake zaune a gefe ta danyi dariya tace " na zata ni kadai ce a cikin mu nake irin wanan shirmen. Gashi har Samha ta zartani".

"Ai keda ita ban san me yake damunku ba, baku neman shawara kafun kuyi abu" Tsaki khady taja sa'anan ta cigaba da fadin

"Ai ni Sabah yayi mun daidai, gwanda daya fada mata kai tsaye, kinga the more she diskikes him, the better it is for you. Don gaba ta kaiki"

"Toh ai Madinan tace akwai wanda takeso". Samha ta fada tana dubansu daya bayan daya.

Turo baki khady tayi bata sake cewa komai ba don ita already ta rigada ta gama jin haushi.

Amina ce ta soma fadin "karki damu Samha, nasan da kyakyawar niyya kika aikata hakan ba tare da kinsa komai a ranki ba don haka ki cigaba da hakuri, don mai hakuri shine mawadaci, komai zai tafi normal da yardar Allah".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now