chapter two

1.1K 83 0
                                    

Washe gari da sassafe samha ta tashi ta fara shirin ta na zuwa makaranta kasancewar tanada morning lecture a ranan kuma ga abu mai muhimanci da ta saka a ranta yana jiranta. Anty fanneh da wuri itama take fita zuwa office. Don haka Suna gama breakfast, Suka fita tare ta sauke samha a school, Itama ta wuce office.

Samha na shiga school bafi 5 minutes ba sai gasu khadija suma sun shigo. Daman tun da ta shigo school kirjinta ke ta faman bugawa da karfi. Har tayi niyan ta fada wa su khady ta fasa, sai kuma tasan baza su ma saurareta ba don haka ta hakura.

Suna ajiye jakansu cikin locker, amina ta fito da letter din Wanda aka ninke cikin envelope, harda fesa masa turare.

Khady ce tace " kunga yanzu nan da yan mintuna zai shigo yaje departmental library. So zaki tsaya idan yazo wucewa sai ki mika mishi. Mu kuma zamu tsaya ta bayan office din admin, muna hango ki daga can, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi kamar yanda muka tsara, kinji besty. Amjad kamar ya gama zama naki ne insha Allah."

Haka suka yarda da wanan tsari, amina ta mikawa samha letter din suka sauka kasa. Daidai wurin gindin bishiyar fruits dake bayan department dinsu ta tsaya. Su kuma su Amina suka tsaya ta bayan office din admin.

Samha na tsaye zuciyarta sai bugawa takeyi kamar zata huda kirjinta ta fito. Sai faman gumi takeyi. Tana tsaye har kusan 5 minutes bai zo ba sai data kai kusan minti goma sa'anan ta hango shi yana zuwa. Juyawa tayi ta kalle su khady, Wanda suka daga mata hannu alamun ta cigaba da tsayuwa, ta jira ya karaso. Cike da fargaba ta jiyo takunsa alamun yana gab da isowa inda take. Fitowa tayi daga bayan bishiyan ta tsaya a gefe. Tana ganin ya karaso ta mika hannunta rike da letter din kanta a sunkuye ta rufe idanunta gam don bazata iya kallonsa cikin ido sa'anan tace "Amjad, ga sako nan dan Allah ka karba ka karanta..."

Kusan minti biyu tayi a tsaye taji shiru ba'ace mata komai ba kuma letter na nan a hanunta ba karba ba. shirun data jine yasa ta bude idanunta a hankali ta dago kanta cike da fargaba. Zuciyarta sai faman bugu takeyi kamar zata huda kirjinta ta fito.

Me zata gani?
Maimakon taga Amjad tsaye a gabanta sai kuma taga akasin haka. Idanuwanta ne suka sauka kan wata bakuwar fuska.
Wani saurayi tagani tsaye a gabanta, hanuwansa rungume bisa faffadan  kirjinsa ya kura mata ido, sai faman binta da kallo yakeyi. Fuskarsa dauke da alamar tambaya. Bata taba ganinshi a department din ba sai yau. Tama rasa ta inda ya bullo, kawai ganinshi tayi a gabanta kamar wani aljani. Toh ina amjad din? ta tambayi kanta.
Nan danan cikinta ya kulle, cikin in'ina ta soma tambayarsa" Aa..mjjad fa, inaa..yake?
Bai bata ansa ba still yana tsaye yana kallonta.

Haba nan da nan tunaninta ya dawo mata. Bata San sanda ta sake yar karamar kara ba ta kwasa a guje ta bar wurin, bata lura ba garin gudu letter din ya fadi daga hannunta.
Abunda bata sani ba shine Amjad ya saka earpiece a kunnenshi yana Sauri ya karasa library bai lura da ita a tsaye a wurin ba har ya wuceta. Su khadija ma tun da sukaga yanda abubuwa suka sauya suka bar wurin babu shiri.

Shi kuwa saurayin data gudu ta barshi tsaye a wurin, abun har yaso ya bashi dariya musaman ihun dayaga ta sake da kuma yanda ta kwasa a guje. Sunkuyawa yayi ya dauko letter din daga kasa, ya bude ya fara karantawa. Abun da yagani rubuce a ciki ne ya daure mai kai kuma ya mugun bashi mamaki. Nan da nan kuma ya fahimci abunda yake faruwa. Mata sunada matsala ya fada a ranshi, Saka letter din yayi cikin aljihunsa ya kara gaba.

Ita kuwa samha bata tsaya ko ina ba sai cikin aji, sai faman haki takeyi tsaban gudu da fargaba. Tana ganinsu khady a class din bata San sanda ta saka kuka ta daura hannu a kai tana fadin " nashiga uku, yau na tozarta, wani irin abun kunya na jefa kaina ciki yau? Daman na fada muku wanan abun shirme ne bazai yu ba, gashi amjad dinma ko kallo na baiyi ba ya wuce ya barni ina tsaye"

Rarashinta suka fara suna fadin " kiyi hakuri samha, ai bai ganki ba, akwai earpiece fa kunnenshi shiyasa bai jiki ba. Muna ganin komai. Ki kwantar da hankalinki."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now