Chapter twenty-one

573 58 0
                                    

Jikin samha ne yayi sanyi dataga yanda sabah ya karbawa Aliyah baki a wajen yan matan. Gabadaya sai taji wani iri. Tunani kala kala ne suka soma mata yawo a ka. Suna cikin haka, Amjad yazo wucewa ta gabansu, khadie na ganinshi ta kwada mishi kira daga sama. waigowa yayi ya hangota a sama tare dasu samha. Amjad yana ganin samha ya kura mata ido yana kallonta, suna hada ido yaga ta kawar da kanta gefe. Amjad ya mayar da dubansa ga khadie wace take daga mishi hannu alamun ya hauro sama ya samesu. Sabah kam yana tsaye ta gefe yana binsu da kallo har amjad ya haura sama yaje ya tadda dasu. Khadie ce ta dan turo samha gaba tace taje ta sameshi suyi magana. Samha ta rikice ta rasa yanda zatayi don a lokacin wani irin kunyar amjad takeji. Shi kanshi amjad yana tsaye ya rasa abunda zai ce mata. Su khadie da sukaga shirun yayi yawa babu mai niyar magana a tsakaninsu, khadie ta matso kusa dasu fuskarta dauke da murmushi ta soma fadin " Dan Allah kuyiwa junanku magana ku daina wanan abunda kukeyi, haba meyasa kukeyin haka, karku manta fa haryanzu we are still friends, duk ana tare, kuma..."

Samha bata bari ta karasa maganarta ba ta katse ta da "ai daman ban sa komai a raina ba. Kawai dai ban san me zance bane". ta karasa maganar tana sunkuyar da kanta kasa.

Khadie tace " kar ki sa komai a ranki, ki sake jikinki samha, kuma ki daina yi kamar kin aikata wani babbar laifi."

Ta dawo da dubanta ga amjad ta cigaba da fadin "Kai kuma kana namiji, ai gaba ba nake bane. Abunda ya rigada ya faru, ya faru, so a manta da komai mu cigaba da kamar yanda muke a da." ta karasa maganar tana duban amjad wanda ya kasa kallon kowa, don gabadaya sun sashi a tsakiya.

"Kaga idan ka cire komai a ranka, ba karamin kyau zaka kara bama". Khadie ta fada tana kashe mishi ido daya.

Amjad dariya yayi ya dago yana dubanta sa'anan yace " ai babu wata matsala, komai ya wuce insha Allah."

Khadie ta aika masa da tsadaddar murmushinta sa'anan tace " toh bayan haka, samha tanada wata alfarma da take so ta nema a wajenka".

"Me kenan?"

"Tunda ka kasance kaine captain din basketball dinku, me zai hana ka mayar wa samha aikinta nada a matsayin manager".

Amjad shiru yayi yana nazari daga bisani yace "toh shikenan babu matsala bari yaje ya tambayai yan team nashi, yaji ta bakinsu, idan sun amince toh.

Haka suka yarda da wanan tsarin suka soma saukowa kasa tare.

Daman sabah tun lokacin da amjad yaje ya same su samha, gabadaya sai ya dinga jin wani iri. Wuri ya samu a gefen gym din ya zauna yana nazari don gabadaya hankalinshi da tunaninsa na can wurinsu samha.

Yayi zurfi cikin tunani sai ga Aliyah nan ta nufo inda yake zaune hanunta rike da bottle water tazo ta tsaya kusa dashi. Kurawa kyakyawar fuskarsa ido tayi tana murmushi. Wani irin dadi takeji a ranta a duk sanda taganta a tare dashi.

"Prince, ga ruwa nan na kawo maka idan kana bukatan sha" ta fada tana aika mishi da wani irin kallo mai cike da so da sha'awa.

Sabah dagowa yayi yana kallonta sa'anan ya bata ansa da "A'a ban bukatan sha, kuma bana miki kashedi akan wanan sunan da kike kirana dashi ba?"

Aliyah ta tabe baki bata ce mishi komai ba. Suna cikin haka, sai ga amjad nan ya dawo yana fadin " oya kowa ya matso akwai maganar da nakeso mu tattauna kuma ina bukatan kowa yasa baki ya fadi ra'ayinsa akai".

Gabadayansu suka matso suka tsaya kusa dashi suna jiran suji mai zai fada "gamu nan captain, kayi magana muna sauraronka".

Amjad ya dan nesa sa'anan ya soma fadin " yauwa, ina fatan kowa ya lura da yanda wanan club namu na basketball tayi suna kuma tayi fice cikin yan' kwanakin nan, don haka ina....."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now