Chapter three

968 78 1
                                    

Yau ta kasan ce Tuesday a cikin sati. Samha har ta soma mantawa da abubuwan da suka faru a wancen satin tsakaninta da sabah don taji shi shiru bai sake nemanta ba ko ya sake mata magana har ta soma sakawa a rai cewa daman barazana yake mata yanaso ya mata wasa da hankali ne. Shiyasa ta share shi ta cigaba da harkokin gabanta. Yau zaune take cikin aji, sai faman rubutu takeyi tana kokarin kammala notes dinta. Su khady da Amina suna zaune suna jiranta don su sauka kasa tare.

Kamar daga sama taji ana fadin " Wacece Samha Abdullahi?". Dagowa tayi tana duban wanda yayi tambayar. Haka zalika ma waenda suka rage a aji suka juyo suna kallon mai tambayar. Shima student ne amma da allamun ba department dinsu yake ba.
David lawson dake zaune a baya ne ya bashi amsa da " Gata can a zaune a gaba".

Harara khady ta watsawa david tana ce mishi " waya tambayeka, zan buge ma baki yanzu". Dayake akwai wasa a tsakaninsu.

David shima harara ya galla mata.

Samha ta tsura wa student din ido har ya karaso gabanta sa'anan yace"sabah yace ki sameshi a rest room na department dinsu.

Zaro ido su khady sukayi suna kallon student din sa'anan suka mayar da dubansu ga samha. "Sabah kuma? Toh meye hada samha da sabah, me zata mishi?"

Bai basu ansa ba yayi tafiyarshi ya barsu a wajen.
Mikewa samha tayi tana kokarin bin bayanshi. Khady ce ta riko hanunta tana fadin " keh ban gane ba ina kuma zakije, badai wurin sabah din ba? Meye hadinki dashi Kin san waye shi kuwa? Nayi bincike na musaman fa akan shi kuma an tabbatar mun da ba mutunci ne dashi ba. baya ragama kowa, kinsan inada friends a baze university kuma yawanci an sanshi a can. Please karki fada tarkon sabah dan Allah kiyi zamanki."

Ajiyar zuciya samha tayi ta zame hanunta daga rikon da khady ta mata sa'anan tace
" yanzu zan dawo khady, kudan bani minti biyar bari inje inji meke tafe dashi."

Tana gama fadin haka ta fita daga ajin. Su Amina suka bi bayanta da kallon mamaki.
Tana sauka kasa straight computer science ta nufa, taje rest room din. Nan ta sameshi zaune ya kishingida akan kujerar zama, kafafun shi daya kan daya, idanuwanshi a lumshe kamar mai bacci.

Tsayawa tayi tana kare mishi kallo, sanye yake cikin white Tshirt da bakin wando , kayan sunyi fitting dinsa sosai. Sai black jacket daya dora kasancewar daren ranan anyi ruwan sama ko ina ta dau sanyi.

Sumar kanshi ta kura wa ido yanda ya kwanta luu luu kamar na baby.
Sai gashin giranshi daya cika ya kwanta. Hancin shi straight, sai karamin bakinsa dayayi fitting fuskarsa ya kara fito to ainun kyaun halittar fuskarsa, komai nashi daidai kamar shi yayi kansa. Sai dai bakin hali ta fada a kasan ranta. Harara ta watsa mishi tana kara jin haushinsa.

A hankali ya bude Idanuwanshi farare tass dasu suka sauka a kanta, ganinta yayi tsaye a kanshi.

Dagowa yayi daga kwanciyan dayake yana shafo lallausar sumar kansa sa'anan yace " yan mata ya naga kinzo kin tsaya mun aka kinata bina da kallo, lafiya?"

Dan rainin wayo ta fada a ranta" ba kai bane ka turo a kirani ba" ta bashi ansa ranta a bace.

"Da kuma nace akira ki sai ki zo ki wani tsaya mun aka kaman wata bishiya?"
Ajiyar zuciya yayi sa'anan ya tura hanunshi cikin aljihu ya ciro yan dubu dubu ya mika mata " ban son wani dogon surutu ungo nan jeki cafetaria kiyi mun take away guda hudu na abinci, daga nan ki wuce snack bar ki siyo snacks da soft drinks ki kawo mun nan ina jiranki, kuma na baki minti biyar kiyi ki dawo".

Bude baki tayi tana kallon shi cikin mamaki da takaici sa'anan tace " ban gane ba, take away hudu fa kace? tayaya ma zan ruko kayakin nan ni kadai?"

" wanan kuma ba damuwata bace.Kisan yanda zakiyi ki riko su, in ma tafiya biyu zakiyi wanan ya rage naki .Kuma batun take away hudu danace kiyi wanan babu ruwanki. keh nifa bana son yawan tambayoyi. Oya yi ki tafi, kina bata mun lokaci yunwa nakeji" ya fada mata sa'anan ya koma kwanciyarsa ya barta a tsaye.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now